← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 38

Sashe 30

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Haushi,takaici,bakin ciki, ne suka lullubewa Sukainat zuciya,Ganin irin bakaken maganar daya yaba mata" Gakuma wulakanci da Nadiya tayi NASA"Ganin bazata Iya jure takaicin bane yasa tajuya tanufi sashenta ranta bakikkirin tarasa meke damun Ahmad.tana shiga tarufe kofar ta,fadawa kan gado tayi tafashe da wani irin kuka me ban tausayi shin wannan wace irin rayuwa ce daga wannan matsalar ta kau se wannan shin se yaushe Ahmad zegyara rayuwar sa suyi rayuwar me inganci tamkar kowasu ma aurata,Shin yaushe ne za tasamu farin ciki? rayuwar ta agidan Ahmad yazame mata jaraba"Ganin kukan baze fish-shiteba yasa tamike tashiga toilet ta daura alwala tazo ta tada sallah tana kuka tana rokon Allah daya kawo mata dauki acikin rayuwar ta...
Washe gari;
Se wuraren karfe bakwai Nadiya tabude kofar ta"tana budewa taji mutum ya fado dakin"Dasauri ta kalli kofan Ahmad tagani,cike da mamaki take kallon sa, da alama bacci ne ya daukesa awajen.Wani irin farin ciki ne ya lullube mata zuciya,jitake kamar ta taka rawa tsaban farin ciki,shikenan aikinta yariga ya kammala burinta yacika Ahmad yazamo mallakinta se yanda tayi dashi"ganin yanda yakafeta da birkitattun idanunsa ne yasanyata dedeta nutsuwar ta.tana mai daure fuska tamkar wacce taga,makiyinta."Malam me kakeyi min akofa!?tafada babu walwala afuskarta.Cikin kwantar da murya yace"kiyi hakuri My Queen Wlh so nike in ganni kusa dake,bani da burin daya wuce inganki agefena,tare da kallon wannan kyakykyawar fuskar taki me sanya min nutsuwa.Dan sassauta fuska tayi jin abinda yace.Tace"ni banason karya da dadin baki inace tarewa kayi adakin amaryan ka kana wulakan tani,kanuna nida banza daya mutake kanuna bani da muhimmanci awajen ka,kanuna waccan kucakar yarinyar tafini muhimmanci da daraja A idanunka"Har dukana kayi akanta,Dan haka ka tattara ka koma wajen ta dan ni bana zama da makaryaci kuma mayaudari.

Marerece fuska yayi kamar zeyi kuka duk yadawo kalar tausayi yace"Dan Allah kiyarda dani My Queen ina matukar kaunar ki ke ka'dai ce sanyin idaniyata kuma Uwar yaya na.Jin kalaman sa yasanya taji, zuciyar ta yai sanyi dan haka sedata gama jamai aji kafin ta hakura.

Bayan ta idar da sallan walha ne tamike ahankali tanufi kichen,baki daya batajin karfin jikinta ga yunwa dake nanukar cikin ta"Hakan yasa ta kunna gas tadaura indomie guda daya hungry man, tasanya mai kwai da gesher tare da hada masa kayan lambu,sosai girkin yayi dadi se tashin kamshi yake.
Nadiya dake parlour ta hakimce akan tangamemen kujeranta tana danne danne awaya yayinda Ahmad ke yimata massing a kafafunta suna hira jefi jefi.Baki daya kamshin indomie ya karade parlour ta Kallon Ahmad tayi cike da kissa tace"Honey kamshin girki nakeji ko amaryar ka keyi?,Bata fuska yayi yace"aini banida wata amarya data wuceki my Queen.Tabe baki tayi aranta tace yanzu daka shiga hannu kenan,!Azahiri kuwa seta langwabar dakai tace"Pls honey ina so inci abincin dake kamshin nan,bari naje tasammin tafada tana kokarin mikewa"sake mata kafafunta yayi,yakoma yajingina bayan sa da kushin tare da lumshe idanun sa yana jin wani yanayi atare dashi....

Madede cin plate tadauka tajuye indomie dataga yamata kyau a idanu,Bare kwoyin tayi,kana tayi silaizin dinsa akai,se hadiyar yawu take abinka da mai ciki kasa hakuri tayi yayi sanyi,Hakan yasa tanemi kujera tazauna a kichen din tafara ci da zafi.
Cokali hudu tayi taji ajanye plate din daga gabanta.Dasauri tadaga kai tana kallon Nadiya dake rike da plate din ahannunta tana hararanta da kananun idanunta."Wani irin Neman magana ne haka mumy rufy!?kibani abincina bana son abin tashin hankali, takarashe cikin sanyin muryan ta!.Dariyar rainin hankali Nadiya takece dashi kafin tace"nakarfine,inza ki Iya kikar ba,matsiyaciya yar matsiyata ba asaba ci agida ba shine akazo nan ake rawan jiki wajen ci,tana gama fadin tajuya ranta fes tayi hanyar fita.Rai abace Sukainat tamike tarike plate din,tare dacew aikuwa bazaki ci ba domin baki isa kina zaune inyi miki girki ba,maganar tsiya dakike kiwa Allah ne yaga damar barin mu ahaka"Sannan nagodewa Allah daya bawa mahaifina wadatar zuci,baya zuwa maula.
Takaicine yakama Nadiya hakika yarinyar taga gadon baccinta anma bakomai daf take daseta mata hanya"Kisake min abinci"Kin sakewa Nadiya tayi,Fincike plate din Sukainat tayi da karfi,cikin rashin sa'a ya kwabewa Nadiya akafa!..
Ihu tasanya ta durkur kushe awajen tamkar wacce ake yankar naman jikinta"Rau rau Sukainat tayi da idanu ganin yanda abincin ta yatarwatse akasa,jitake kamar tafashe da kuka.Arazane Ahmad yashigo kitchen din jin ihun Nadiya,Ganinta adurkushe yasanya shi saurin karasowa gabanta,tsugunnawa yayi yana kokarin rike kafar,cike da damuwa?yace"meyasa meki haka my Queen!?,Kukan kissa Nadiya tafashe dashi tajanye kafar ta,duk dakuwa bawani zafi kafar keyi mata ba anma tadauki alwashin musgunawa rayuwar Sukainat"cikin muryan kuka tace"Kawai danna ce tabani indomie inci shine tahau zagina!hadda cemin wai bazata bayar ba tunda ba ubana ne yasaya ba,ta inda take shiga batanan take fita ba,karshe ma dubi abinda tayimin tafada tana nuna kafarta da indomie ke azube...

Cike da matsananin cin bacin rai Ahmad yamike yadun fari Sukainat,yana me binta da wani shegen kallo,.Baya tafara ja,dan ta tsorata daga nin yanayinsa bakaramin razanata yayi ba"ganin yanda lokaci daya idanunsa suka canza kala izuwa tsantsar bala'i,da jaraba datake iya hangowa aciki.Cikin sauri tajuya tafice daga kitchen din,cikin mugun sauri domin tasan idan tatsaya komai zai Iya faruwa a irin yanda take kallon kwayar idanunsa.

Taku biyu yayi yariko hannunta,cikin wani irin murya mecike da karaji dakuma hargagi yace"kije kinemi yafiyarta abisa lefin da kikayi mata!,dasauri takallesa cikin rawan murya tace"kamar ya in nemi yafiyarta?kamata yayi katamba yeni meya hadamu anma bawai kace...Be bari ta karasa fadar abinfa tayi niyya ba, yakife ta da Marin daya sanya taga gilmawar taurari a idanunta.cikin karaji yace"wannan yazama karo nakarshe da zanbaki umarni kiyin musu,in bahaka ba zanyi miki abinda bakyayi zato ba da kikiya kawai.Zafafan hawayen dasuka zubo mata yayi saurin sanya hannunta tashare,Jin diban albarkan daya kemata agaban kishiyarta" kokarin hana kanta kukan dake cinta take kodan Nadiya dake kallon ta tana sakar mata da murmushin mugunta...

Wai bazakiyi abinda nasaki bane sena tattakaki!?"muryansa yakatse mata tunani cikin tsawa.Ahankali ta karasa shiga kitchen din, cikin rawan murya tace"kiyi hakuri.Wani kaskantaccen kallo Nadiya tawatsa mata,kafin tamaida kallonta ga Ahmad dake tsaye yana kallonsu"cikin bada umarni tace"Honey kasa tadafa indomie yanzu inada bukata,tana gama fadin haka tafice daga kitchen din tana murmushin mugunta"Wani shegen kallo ta watsawa Sukainat kafin tafice,ranta fari sol.

Ina fatan kinji abinda tace tana bukata,base nasake maimaita mikiba?shiru tayi kanta akasa takasa furta komai banda sake sake da zuciyarta keyi.Ahasale yace"Ke bamaga na,neke dake ba kinyi min banza, koda yake balefin kibane,Lefin iyayen ki ne da basu baki cikakkiyar tarbiyan dazaki yiwa mijin ki biyayya ba.
Kukan datake kokarin dannewa ne yakufce mata shin wannan wani irin cin mutunci ne Ahmad keyimata.Durkushe wa tayi awajen tashiga rera kuka mecike da ban tausayi da kuma tausayin kanta.Tsaki yaja kana yamaka mata harara kokadan babu digon tausayinta azuciyar sa hasalima yatsani koda ganin fuskar tane"Afusacr yace"Wallahi minti goma nabaki kigama abinda tasanya ki inba haka ba kofa yayi batare daya karasa fadar abinda yayi niyya ba yafice....

Sosai tayi kuka,Wanda yasanya mata matsananncin ciwon kai" dakyar ta Iya mikewa tsaye,tana jin jiri nadibar ta,ahaka tadafa mata indomie,sannan tajuye a plate tanufi dakin,ahankali take tafiya sakamakon jiri dake dibarta.Da sallama tashiga parlour...kasa karasa sallamar tayi,sakamakon ganin Nadiya da Ahmad na kissing junansu tare da wasu abubuwa Wanda idanunta bazasu Iya gani ba.Dasauri ta ajiye plate din tafice hartana tuntube da kofa.
Tanashiga daki tafada akan kujeran tare dafashewa da kuka meratsa zuciyar duk wani mai imani kuka ne irin na Wanda yake cikin tsananin damuwa da tashin hankali"Yunwa takeji anma saboda damuwar datake ciki takasa cin abincin..Da karfin gaske aka banko kofar dakin tamkar za'aballa.Arazane tadaga kai tana kallon kofar tare da furta kalmar innalillahi wa'inna ilahi raji'un....

_VOTE COMMENTS &SHARE_

*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_

*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_

*WATTPAD*
_Realeshaa_

_Like my page on Facebook_👇🏻

https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/

*_Ya Allah kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

*PAGE 49&50*🖌️

_______________________________📖Cikin tsawa Nadiya tace"ke dakata shedanu kikagani kome!?dazaki tsaya kina yimana sallami,au na manta ashefa yar malamaice,tafada cike da kaskanci.Shiru Sukainat tayi batace komai ba,cikin ranta tace" aibabu maraba da shedanun,azahuri kuwa setayi kasa da kanta.Kafin tayi wani yunkuri daga inda take zaune,Nadiya tadaga plate din indomie dake tiririn zafi ta watsa mata.Jin saukar Abu mai zafi ajikinta yasanya ta daga kanta,Akidime tana kallon Nadiya dake tsaye da plate din indomie adaya hannunta,yayinda daya hannun ke kugunta tana jijjiga cike da bala'i!.

"Kallonta ta mayar kan Ahmad dake tsaye abayan Nadiya kamar bodyguard ko alamar gezau beyi ba ganin abinda Nadiya taimata hasalima dauke kansa yayi kamar bega abinda kefaruwa ba.Cikin rawan murya tabude bakinta da niyyan magana...Anma kafin tafurta komai Nadiya tarigata da fadin" ke yar talakawa dangin jaraba,saboda rainin hankali irin naki shine zakije kidafamin abinci me uban attaruhu saboda kina bakin ciki dani kinason ganin bayana to bari in sanar dake abinda baki sani ba wallahi ko ubanki ne sarkin malaman duniya baku Isa kuga bayana ba bare ma shi bakowa bane face dan maula,dan haka ina me gargadinki dakifita daga cikin rayuwar mu inba haka bane nuna miki bakin rijiya bawajen wasan makaho bane.
Chapter 30 · 0% Book details