← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 38

Sashe 37

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kai ta girgiza hawaye nataruwa a idanunta aranta tace wannan wace irin tambaya yake mata"Cikin sanyin murya tace"A'a wankesu nayi shine yanzu nake ninkewa takarashe cikin raunin murya!!, tsaki yaja tare da maka mata harara,kafin yazagayo gabanta yatsaya suna fuskantar juna,Ahankali tajanye idanunta daga nasa dan babu abinda take hangowa acikin kwayar idanunsa banda tsantsar-tsananta.

So nake kitambaye ni abinda ko wace mace ke tambaya awajen mijinta idan tanaso takoma gidan su,yafada babu alamar wasa atare dashi.Cike da mamakin furucinsa take Kallon sa cikin dakewa tace"ni babu abinda nake bukata,In kincika yar halak dan Allah kitam bayeni Sukainat,banza tayi masa tacigaba da ninke kayanta.
Har tagama yana tsaye yana jifanta da kallon datakasa fassara na menene,tsaki mai karfi yaja yace"jarababbiya kawai da kitam baya mana idan ba tsoro ba yafada asanda yake fita daga bedroom din...

Inmalillahi wa'innah ilahi raji'un tafada asanda kuka yaci karfin ta shin Wannan wani irin jaraba ne shin wai wani kalar kiyayya Ahmad kenuna mata!?azatonta kowani irin laifi tayi masa beci ace yana nuna mata irin Wannan kiyayyar ba koda kuwa ace auren dole akayi musu bare ace auren soyayya sukayi anma bashida makiyiyar data wuceta,kan gado tafada tana Jan zuciya,hakika da ace hawaye Na karewa to da tuni nata sunkare,dahaka baccin wahala yadauke ta batare data shirya ba...

Bata fuska tayi asanda yagama labarta yanda sukayi da Sukainat cikin daure fuska tace" kana nufin ka fada mata haka!?Cikin rawan jiki yagyada mata kai alamar eh"tsaki Nadiya tayi tace"tunda nake bantaba ganin mace mai naci irin Wannan matar takaba,koda yake banga lafinta ba domin daka koreta Aida tuni tatafi anma dake kaima nason zama da ita shine kakasa tabuka komai. Cikin sauri yace"Wallahi my Queen bayanda zanyi ne anma nima nagaji dazama da ita!.hmm nifa banga amfanin zama da macen dabata da ibada ba,dan ko a musulunci idan mace bata sallah be hallata kazauna da ita!!..

Rai abace yakalleta yana hura hanci yace"kina nufin bata ibada shine baki fada min ba!?Dan marairace wa tayi tace ai tsoron fada maka nake,tafada tana kunshe dariyar ta.Daga yau karki sake bata abinci har natsawon kwana biyu seta fara sallah kafin tafaraci.

Haba Honey anya hukuncin be yimata tsauri ba kuwa??,hade fuska yayi cikin bada umarni yace"nagama magana yafada asande yake ficewa daga dakin...

Se misalin karfe biyu ta tashi toilet tashiga tawatsa ruwa kana tadaura alwala tazo ta tayar da sallah bayan ta idarne tanufi kitchen tahada musu jollof din taliya dayaji kayan hadi se kamshi ketashi kana tajere komai a dining kafin tanufi bedroom din ta.Ga mamakinta data fito bataga abincin taba,bedroom din Nadiya tanufa tayi knocking daga ciki taji anbata izinin shiga.Da sallama dauke abakinta tashiga,daga kofar dakin tatsaya tace"Aunty ina abinci na!?Murmushi Nadiya tayi tace "Au Dadyn rufy bece miki komai ba ne?kai tagyada alamar eh.Ayyah ainayi zaton yasanar dake domin yace kar asake baki abinci senan da kwana biyu!,Rai abace Sukainat tajuya tafice batare datace komai ba...

Yau kimanin kwana biyu Sukainat bataci abinci ba kamar yanda yafada Iya galabaita ta galabaita,gashi babu abinda suka ragemata na bautar datake musu...Kwance take atsakiyar dakin tana fitar da numfashi da kyar, da sallama abakinsa yashiga dakin tsayawa yayi akanta yace" kin shirya yin sallah yau abaki abinci??.Cikin karfin hali tamike hijab din ta dake kan kofa tadauka tasanya tare da daukar wayarta trolley tajanyo tashiga sanya kayanta duk yana tsaye yana Kallon ta seda tagama shiryawa tadago rinannun idanunta dasuka dafe dakuka tace"ya Ahmad zan barmaka gidanka ayau din nan insha Allah idan har ina cutar dakai azaman takewar auren mu zakagani idan ma bana cutar dakai zakagani bayan bana nan, badan komai zanbar gidan kaba sedan kazafin dakayimin kancewa bana sallah kaje Na barka da mai kowa mai komai shize yimana sakayya tana gama fadin haka tafice daga gidan tana hawaye....Da kallo yabita har tafice,cikin daga murya yace"kifi ruwa gudu...

Tafiya sosai tayi kafin ta Isa bakin titi lokacin tagalabaita cikin ikon Allah tana karasawa tasamu adaidaita hawa tayi tare dasanar dashi inda ze kaita bamusu yace"tashiga,da bismillah dauke abakinta tashiga jin gina Bayan ta tayi tana jin jiri nadi barta addu'ar ta daya Allah yakaita gida lafiya koda mutuwa ne ta mutu agaban iyayenta,kunna adedetar yayi suka tafi.

Suna Isa tasauka tabiyasa hakkin sa kafin tashiga gida da kyar take Iya daga kafanta,azaure sukaci karo da Malam Ahmadu dake shirin fita sallan la'asar amatukar galabaice tatsugunna tagaishesa yayin da muryan ta ke sarkewa saboda tsananin yunwar dake damunta gatarin gajiya da tashin hankali datake ciki.Dasauri Malam Ahmadu yatareta izuwa jikinsa ganin zata fadi.Dagota yayi yariketa ajikinsa suka shiga gidan, direct dakin Ummi yanufa da ita ya ajiyeta yana mata sannu cike da damuwa,Da kyar take Iya Jan numfashi yayin da idanunta ke Neman kafewa asama,cikin sauri Ummi tashafa addu'ar tajuyo garesu cikin tashin hankali,da dimuwa,fita waje tayi ta debo ruwa akofi tashiga Shafa mata afuska tare da tofa mata addu'o'i,Ahankali idanunta suka fara dawowa dai-dai sejan ajiyar zuciyar datake akai-akai.Malam Ahmadu kuwa yakasa tabuka komai banda kafe yar tasa dayayi da idanu cike da matsanancin tausayin ta, ganin duk yanda tawani jeme tamkar wacce ta warke daga cutar amai da gudawa...

Cikin shakakkiyar Muryan ta da befita sosai tace"Ummi yunwa nakeji tafada jikinta na rawa tamkar mazari tsaban yunwar dake addabar ta.Dasauri Ummi tamike ta dauko flaks din dake cike da ruwan zafi tazuba mata tea kana tadauko peak sachet da Milo na sachet,tazuba mata,sesetawa tayi sedataga zafin yayi dai-dai kafin,takarasa inda take takafa mata kofin abakinta cikin sauri tafara sha,seda tashanye tass kafin tajanye bakinta ajikin kofin tana maida numfashin wahala yayinda taji zuciyar ta natashi tamkar zatayi amai...

Ahankali Ummi tamaida Kallon ta ga Malam Ahmadu daya zubawa Sukainat ido ko kyaftawa bayayi cikin sanyin murya tace"Malam kayi sallan kuwa?, Cikin yanayin damuwa yace"Yanzu zanje inyi yafada yana asanda yake mikewa,ficewa yayi yanufi masallaci lokacin dayaje Har an idar hakan yasa yayi shi ka'dai bayan ya idarne yashiga addu'o'i kan Allah ya dedeta tsakanin Sukainat da mijinta.

Sukainat kuwa idanunta talumshe ajikin mahaifiyar ta yayinda taji nutsuwa naratsa kowani lungu da sakon dake jikinta hakika iyaye rahama ne duk Wanda yarasa su toh yayi kuka musamman Uwa domin wata garkuwa ce acikin rayuwar yayanta Wanda in babu ita rayuwar su bakomai bane.daga ta Ummi tayi daga jikinta tanufi kitchen tuwon masara miyan danyen kubewa tazuba mata,Hannu baka hannu kwarya Suky tafara ci.Sosai Ummi tayi mamakin yanda takecin abincin tamkar mayunwa ciya tass tacinye,tace akara mata,Karo mata Ummi tayi sannan tabata ruwa tasha,baki daya tacinye abincin da ruwan kana tashiga sauke ajiyan zuciya...

Kai kawai Malam Ahmadu da Ummi ke jinjinawa a lokacin da Sukainat tagama sanar musu da halin datake ciki dakuma irin kuncin datake fuskanta bata boye musu komai ba domin batada kamansu kaf duniya yazama dole tasanar musu da sirrinta...Cike da dattako Malam Ahmadu yace"Allah yarufa asiri yakuma kiyaye gaba,sannan kidage da addu'a kan Allah yazabar miki abinda yafi zama alkhairi,Iya abinda yafada kenan yafice daga dakin duk Iya abinka bazaka gane yanayin da fuskarsa keciki ba"Ameen Ummi ta'amsa tana maijin tausayin yar tata....

Cikin dare Sukainat tafarka dawani matsanancin ciwon ciki Wanda dole yasanya su nufar asibiti, suna zuwa aka karbeta tare da bata temakon gaggawa kana akayi mata alluran bacci.se asannan Malam Ahmadu da Ummi suka samu sukaje sukayi sallan asbah kasancewar lokaci yayi...lokacin dagari yawaye Dr yakira Malam Ahmadu yaita masa fada kan yunwar da akabarta dashi natsawon kwanaki.hakuri Malam Ahmadu yabasa,rubuta masa magunguna yayi yace"yaje yasayo karba Malam Ahmadu yayi tare da ficewa...

Yau kimanin satin Sukainat daya a asibiti alhamdulillah jikinta yayi sauki kuma Har yau Ahmad bene mesuba haka zalika iyayenta ma basu nemesaba,da yammaci aka sallame,tsaye suke abakin asibitin suna Neman adedeta,wata motace tazo gabansu ta tsaya,da kallo sukabi motar ganin ya tsaya asetinsu Ahankali mamallakin motar ya bude glass din,da sauri Sukainat takawar da kai ganin Hema dawani da alama itace tasaci tsayawa.Cike da Iya barikanci tace"sannu Sukainat kushigo inrage muku hanya mana?,akuma lokacin ne adedeta yakaraso wajen Malam Ahmadu ya tsayar dashi,cike da kulawa Ummi tace"mungode yata anma gashi munsamu abin hawa,Sukainat kuwa dauke kai tayi kamar bata gan taba suka shiga napep din yaja sukatafi"Ahankali Wanda ke tukin yace"ina kika santa yafada fuskarsa babu walwala"Murmushin yaki hema tayi tace sweetheart kishiyar Nadiya ce baka ganeta bane?tabe baki yayi batare dayace komai ba yaja motar,...

Nadiya dake kwance kan kushin tafashe da dariya tace"kai kawata talauci beyi ba Wallahi!!,ita hema dariyar tayi tace"kede bar matsiyata suna tsaye se rana sukesha anma dayake ta Iya girman ka shine taki shiga inrage mata hanya,Anma suna fama da talauci kingansu kuwa tafada asanda take sake fashewa da dariyar keta,ahaka suka gama wayar Wanda duk hiran aibanta Sukainat da iyayenta suke kafin daga bisani suyi sallama.
Ahmad nadawo wa Nadiya tasanar dashi cewa hema taga Sukainat a asibiti,kana cikin duniyanci da kissa tace"Honey yakamata muje mudubasu"hannu yadaga mata da alamun bacin rai afuskarsa yace"babu inda zanje tunda bani nadaura mata rashin lafiyan ba sannan basu kira sun sanar dani ba mekikeso inje in musu?...zata sake magana yadaga mata hannu alamun besan jin komai hakan yasa taja bakinta tayi shiru....
Chapter 37 · 0% Book details