Sashe 12
Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
________________________📖Dasauri Nadiya tamike tana cewa rufy lafiya meke damunki me yasameki haka?me akasanya miki acikin abincin??, cikin kidima take maganar"Cikin muryan kuka tace momy Wannan abincin ba dadi kamar ba'asa komai acikin ba nide bazan iya Ciba,Inde naci cikina ze 'baci tana fadan haka tafara sheka amai tamkar zata amayar da hanjin cikinta,tadauki lokaci tana aman kafin daga baya yatsaya.Rungumeta Nadiya tayi cikin karaji tajuya tace mekika saka acikin abin cin nan?, Sukainat niyar kashe mu kikeda shi komeye?,dubi halin da kikasanya min 'ya aciki!!.Kai Sukainat tashiga girgizawa cikin damuwa tace wlh bansaka komai aciki ba lafiya kalau nayi girkina dan Allah kuyarda dani mezesa insanya wani Abu acikin abinci na cutarwa"wani 'kas'kantaccen kallo Nadiya kemata mecike da tsantsar tsana tace wlh inhar wani Abu yasamu 'yata bazan 'kyakekiba azzaluma kawai me bakar aniya.Hawaye Sukainat tashiga sharewa jin kalaman Nadiya jiki asanyaye ta matsa kusa da Ahmad hannunsa tarike cikin raunanniyar murya tace ya Ahmad kayar da dani Allah babu abinda nasa acikin abincin bansan ya'akayi hakan yafaruba takarashe hawaye nabin fuskarta.Sosai Ahmad kansa ya kulle da lamarin yamarasa abin cewa,dan haka yasanya hannu acikin abincin yakai bakinsa dan jin ta ina matsalar yake"furzar wa yayi sakamakon wani 'karni da hamamin da girkin keyi da tuwon yayi gashi yayi danye"Dasauri ta dafa kafadarsa cike da ru'du tace ya Ahmad kaima kaji akwai wani Abu aciki ne??.Hannunta yature daga jikinsa yana binta dawani shegen kallo Wanda takasa gane na mene ne!!Cikin daga murya Nadiya tace ke banasan rainin wayo kina nufin babu abinda kika saka acikin abincin haka kawai yarinya zata hau amai sannan kizo kinayiwa mutane pretending??,Allah dagaske bansa komai... Hannu Ahmad yadaga mata yace naji bakisa komai ba,hakan nanufin baki iyaba girki ba kenan?,Dasauri takallesa jin furucin dayayi"Ya Ahmad nice ban iya girkiba ta tambayeshi cike da mamakin furicinsa"hannu yasanya yashafi sajensa fuskarsa yace gaki ga abinci zaki iya ci,sekibawa kanki amsa dan bakinki baze miki karyaba.komawa jikin dining dintayi tasanya hannu tayi testing din abinci,runtse ido tayi sakamakon wani irin test da abincin keyi,kai tadafe tamarasa yanda yanda zata misalta rashin 'dan'dan abincin.Yanzu kin tabbata ba kazafi akayi miki ba ko tunda kinji dandanon abakinki??muryan Ahmad yakatse mata tunani"Kai ta gyada cike da rashin abin cewa harga Allah tasan lafiya lau tayi girkinta anma gashi yanzu abincin yabaci.Pls ki dauke abincin anan kije kisamo mana simple din abinci Wanda zamuci yanzu"jiki asanyaye takwashe warmes din tanufi kitchen.Wani shegen harara Nadiya kebinta dashi kamar idanunta zasu zazzago jitake kamar taje tashake mata wuya tamutu kowa ya huta.Tana zuwa kitchen din tarufe fuska tafashe da kuka me ban tausayi"seda taci kukanta takoshi sannan tashare hawayen ta ganin babu me rarrashinta"Ganin time yawuce ne yasa tayi musu lafiyyen jolof din taliya Wanda yaji kayan hadi da kifi,wasu warmers masu kyau tadauko tajuye acike spoon tasanya tayi testing din abinci lumshe ido tayi dan test din abinci bakaramin dadi yamata ba"Har tadauka zatafita ta tatuna bata zubar da abinci dazun ba, hakan yasa ta ta'ajiye warmers din hannunta ta dauki warmers din tuwon backyard tazagaya tazubar acikin dosbing sannan tadawo tadauki warmers din tanufi parlour.Da sallama dauke abakinta tashiga Parlour hannunta rike da warmers,zama tayi a dining din tasake serving dinsu cikin sanyin jiki tace bismillan ku"wani irin Kallon reni rufy taimata cike da rashin kunya tace Nide bazan sake cin Wannan abincin cikina ya kumbura ba,baki nadiya dake gefe ta ta'be tace yo daman wazesake ci kalan a illatamu.Ahmad de bece komai ba yamike yazauna dan abinci bakaramin kyau yaimasa a ido ba spoon yasa yakai bakinsa" ido yaruntse yakasa cewa komai sakamakon wani azabebben zafin barkono da gishiri daya gauraye masa baki gashi taliyar yayi kamar jikasa aruwa akayi akicire,cikin matsanancin bacin rai yature plate din yafadi a'kasa abinci yatar watse,Wannan wani irin rashin mutunci ne kikwashe abinci nan anan kafin na watsamiki afuska"Wani irin farin cikine yamamaye zuciyar Nadiya jitake kamar tamike tataka rawa"jiki asanyaye takwashe warmers din tamaidasu kitchen zuciyar ta cike da al'ajabin abinda yake faruwa.Cikin kissa nadiya tace rufy tashi kije ki dauki snacks da mineral kisha kinji"tana tura baki tamike tare dacewa toh momy.Sukainat nafita Direct dakin ta tawuce, zama tayi a bedroom din ta tarasa meke mata dadi aduniya taya zatayi abinci me lafiya sannan ace idan anzo ci seyabaci yazama babu test."Kallon Ahmad Nadiya tayi tace agaskiya Honey Sukainat bata iya girkiba,dubi abincin datayi nide gaskiya bazan jure Wannan abinba yakamata ace kayi wani Abu"karkidamu zata gyara insha Allah nasan abinda zanyi."Honey inada shawara tace dashi tana tsare da ido"wace irin shawara yace da ita yana tsareta da dara daran idanunsa"cike da kulawa tace why not indinga koya mata girki tunda de naga bata iyaba inde harzata yadda"kai Ahmad ya jinjina cike da jin dadi yace nagode my Queen hakika ina alfahari dake abisa nuna kulawarki ga duk abinda nakeso.Karkadamu Honey kafi haka awajena"hira sukayi sosai bashi yabar dakin ba se misalin shabiyu lokacin daya shiga Har Sukainat tayi bacci atakure da alamar bata shiryamasa yadauketa.Batare daya gyara mata kwanciyar ba kokuma yatasheta tagyara ba ya kwanta agefenta,ko Addu'a beyi ba da haka bacci yadaukesa....
_Kuyi manage da Wannan bayawa_
_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
```I hide my tears when I say your name. But the pain in my heart is still the same although I smile and seem care free. There is no one misses you more than me.My lovely Father may Allah forgive all ur sin Short coming and make jannatul fiddausi be your final destination. Happy juma'at Kareem😭😭😭😭😭😭😭😭👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻```
*PAGE 21&22*🖌️
_Kuyi manage da Wannan bayawa_
_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_
*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*
*WATTPAD* _Realeshaa_
*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*
```I hide my tears when I say your name. But the pain in my heart is still the same although I smile and seem care free. There is no one misses you more than me.My lovely Father may Allah forgive all ur sin Short coming and make jannatul fiddausi be your final destination. Happy juma'at Kareem😭😭😭😭😭😭😭😭👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻```
*PAGE 21&22*🖌️