← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 38

Sashe 11

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari:bayan tatashi tayi sallah da azkar,bacci takoma kasancewar baccin be ishetaba, cikin baccin takejin anabugun kafar ta tare dacewa kizo inji dadyn na"Ahankali tabude idanunta bataga kowaba,ganin bakowane yasata koma wa tacigaba da baccin ta dan haryanzu batajin karfin jikinta...Rufaida nafita daga sashen Sukainat tanufi wajen mahaifinta tana share hawaye,Hankalin sa tamayar kacokam kanta Cike da kulawa yace 'Yar dadynta meyesa meki??,Fashewa da kuka tayi tace Wai Aunty Sukainat ne dan nace tazo injika shine tamareni wainafita nabata waje batasan damuwa,hawayen yashare mata yace kiyi hakuri kizauna zan ramamiki kinji,Dady zaka mareta kamar yanda tayimin??,Kai ya gyada mata alamar "eh" Nadiya datashaka batace komai ba dan takaici, taso ace da rufy tace Sukainat tamareta mikewa Ahmad yayi yaje yaramamata anma seya shashantar da maganan... Se misalin 11:00am tatashi toilet ta'fada wanka tayi sannan tasaka simple gownt ko mai batashafa ba dan wani azabebben yunwa kedamunta"Da sallama dauke abakinta tashiga parlour amsawa sukayi batare dasun kalletaba direct dinging area tanufa zama tayi tacika cikinta sannan,tamike tadawo parlour kujeran dake kusa da Ahmad tazauna,Cike da ladabi tace barka da safiya ya Ahmad"bayabo ba fallasa ya'amsa tare da tambayar tayajiki?dasauki tacedashi tare dagaishe da Nadiya, fuska acunkushe ta'amsa ganin yasa tamike daniyyan barin wajen..Sukainat taji muryan Ahmad, Ahankali tajuyo tace na'am"zo inason magana dake ba musu tadawo tazauna a'inda tatashi,Batare da yakalleta ba yace yau zaki amshi girki danhaka kishirya,kanta a'kasa tace toh Allah yakaimu anjiman lafiya,shiru sukayi babu Wanda ya'amsa kanta a'kasa tace zan iya tafiya?,"eh yace da ita yana nazartan yanayin ta yalura baki daya jikinta asanyaye,sekuma yaji tabashi tausayi.Har takai bakin kofa yace dawo kizauna anan inkinje dakin mezakiyi?,kanta a'kasa tace sonake inkwanta danbanjin dadin jikina.Kidawo nan inkina Cikin mutane aizakifijin dadin jikin,bamusu takoma tazauna.Baki Nadiya ta ta'be cike da jin haushi tayi zaton Ahmad zemata kaca kaca kan tamari rufy anma kuma bece komai ba sema wani shish'shige mata yake"Cikin murtuke fuska tace Sukainat me rufy tayi miki daga zuwa tatasoki kika mareta tafada tana tsareta da 'kananun idanunta"Cikin yanayin rashin karfin jiki Sukainat tace wace rufy kuma??Harara Nadiya tamaka mata tace ke bansan rainin wayo dama rufy nawa kikasani agidan daza ki yimin tambayar banza??,Kau da kai Sukainat tayi tace banga abin tambayar banza ananba dan ni banfahimci inda zancenki yadosoba.Har Nadiya ta bude baki zatayi magana Ahmad yadaga mata hannu alamar tayi shiru"kallon sa yamayar kan Sukainat,yace dazun natura Rufaida takiraki kizo kuyi breakfast...tiryan turyan yafada mata abinda rufy tace.Baki tarike cike da mamaki tace ni yaushe ma naga rufy wlh ya Ahmad inba yanzu ba nibanga rufy,dazun de Cikin baccina naji kamar anamin magana koda na farka banga kowa ba danhaka nacigaba da baccina takarashe tana kallon rufy cike da mamaki...Bakomai zaki iya tafiya yace da ita,Ahankali tamike tabar wajen cike da mamakin karyar da rufy tayi.Mikewa Ahmad yayi yashiga bedroom batare dayace da Nadiya komai ba hakan dayayi bakaramin kona ma Nadiya rai yayiba anma datatuna abinda tashirya musu setaji zuciyarta tayi wasai kinshingida tayi tana sakin murmushi masu ma'anoni da dama...
Ko da Nadiya tagama dinner zama tayi ita da 'ya'yan ta sukaci batare data nemi Ahmad ko Sukainat ba...Ganin time yawuce yasa suky nufar sashen Nadiya, da sallama dauke abakinta tashiga idan kushin din dake dakin ya'amsa to Nadiya ma ta'amsa"Sukainat bata damu da kin amsa sallamar ba tace momyn rufy ina abinci na?,Banyi dakeba tace da ita!!cike da mamaki tace kamar ya?kamar yanda ki kaji nafada miki tafada tanashigewa bedroom"tadade atsaye awajen kafin tajuya takoma sashen ta.Nadiya nashiga daki tasamu Ahmad Cike da 'kissa tace Honey kagafa nakira kanwata tazo tayi lunch taki wai takoshi,kuma naga bakomai taciba shine nace bari nafada maka kaje kabata hakuri ko fushi tayi kan maganan da akayi 'dazu ne yasata fushi.Kafa'da yadaga yace ki kyaleta inace cikinta ne tahusher da kanta"haba honey yaushe zakace haka aibaza kabiye mata ba dan Allah kaje kararrasheta,dan Allah ki kyaleni dawaya hanataci?,'bata fuska tayi tace gaskiya kaje kabata hakuri danbe kamata kabiyetaba.mikewa yayi yace shikenan tunda kinnace bari naje,murmushin jin dadi tayi tace kokaifa bece komai ba yafice direct sashen ta yanufa"Zaune yahangota tazabga tagumi tunanin duniya ya isheta,zama yayi agefenta yace kidena Wannan tagumin bashida amfani,Kallon ta tamayar kansa tanajin wani son sa naratsa kowani lungu da sakon dake jikinta" 'daure fuska yayi yace meyesa kikaki cin abinci??,Kallon sa tayi tace bakin ci nayi ba naje wajen momyn rufy tace wai batayi girki daniba"wani irin kallo yamata yace yaushe kika koyi karya ne Sukainat da bansanki da karya ba anma yanzu baki daya kincanza halayyarki da Wanda nasan ki dashi ada,Nadiya ce taturoni nan tace takiraki kici abinci kinki shine tace inzo inji meya hanaki?.Shiru tayi tamarasa mezatace kawai se kallo datake binsa dashi,"magana nake dake kinyi shiru"kanta tasanya akafadarsa ta kwantar Cikin yanayin damuwa tace kayi hakuri insha Allah hakan bazesake faruwa yanzu muje inci.Bece komai ba yamike tare da rike hannun ta,Nadiya na ganin sunshigo hanunsu sarkafe dajuna wani irin takaici yaturnuke mata zuciya.Kallon ta Ahmad yayi yace Wannan kanwartaki yar rigimace tafiso komai ayita lallashin ta,yake tayi tace aikuwa de Daga haka bata sake cewa komai tazubawa TV ido.Zama sukayi a dining sunaci suna hira harsuka gama,Nadiya dan takaici kasa zama tayi awajen takoma daki"Bayan sun gama lunch din ne Sukainat tace ya Ahmad wani irin girki za'ayi??,Shiru yayi nawasu mintuna kana daga bisani yace kitambayi My Queen "Murmushi tayi " tace toh,mikewa tayi tanufi bedroom din Nadiya"stayawa tayi tanemi izini,seda tabata izini kafin tashiga"kwance tahango ta dawaya ahannun ta da alama charting take,cikin rashin walwala tace lafiya??Murmushin dake kona mata zuciya Sukainat tayi tace ya Ahmad ne yace intam bayaki me za'ayi na dinner? Ta'be baki tayi kafin tace tuwon shin ka fa zakiyi miyar aghusi"Sukainat nagama ji tajuya tafita batare datace komai ba dan Wannan gadaran yafara isarta....

Da yammaci Sukainat tashiga kitchen dan shirya musu dinner, lafiyayyan tuwon shinka miyar aghushi da farfesun kayan ciki ta musu kana ta ha'da musu juice din gwoba dana mango"a sashen Nadiya tajere komai a dining sannan taje toilet wanna ta tsantsara cikin wasu English wear's green riga da Wanda masu kyangaske tasanya,Wanda yaimatukar fitar mata dasuran jikinta.Cikin takun kasaita tanufi dining din inda su Ahmad ke jiranta,tunkafin takarasa shiga sashen kamshin dadda'dan humranta ya mamaye musu hanci,shagala Ahmad yayi da Kallon ta dan bakaramin kyau tayimasaba musamman yanda kayan ya amshi jikinta"zama tayi akujeran dake kusa da Ahmad tace barkanku da Wannan lokacin "Ahmad ne kawai ya iya amsamata dan Nadiya bakin kishi yahanata magana.Mikewa tayi tafara serving din su rufy ce tafara kai abinci bakinta Wani irin furzar da tuwon tayi tana kokarin amai......

KUYI HAKURI BAKO DA YAUSHE ZAKUDIN GA JINA BA SAKAMAKON KOMAWA SCHOOL DA'AKAYI ASATI BEFI KUJINI SAU HU'DUBA INA FATAN ZAKUYIMIN UZIRI

_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_

*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_

*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD* _Realeshaa_

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*

*PAGE 19&20*🖌️
Chapter 11 · 0% Book details