← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 38

Sashe 10

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

________________________📖Tana shiga daki ta'fada kan gado tare da fashewa da wani irin kuka me cike da takaici da bakin ciki meyesa ko yaushe se Nadiya tacimata zarafin mahaifa shin meye laifin iyayenta acikin wannan abin?,shin Nadiya wai wace irin macece Mara tsoron Allah me mugun bakin hali dakuma zamba cikin aminci talura idan agaban Ahmad ne zata nuna barunta shiyasa Ahmad ke goyon bayanta akoyaushe...tana cikin wannan tunanin taji tsayuwar mutum akanta Ahankali ta'dago kanta tanajin zuciyarta natsinkewa"Ahmad tagani tsaye akanta fuskar nan amurtuke tamkar Wanda aka aikowa da sakon mutuwa"Sosai ta tsorata daganin fuskarsa,dan haka tayi 'kasa dakanta taname jin zuciyarta na tsinkewa.
Sukainat yakira sunan ta akausashe"cike da tsoro ta'amsa batare data 'dago kanta ba dan tsoron ha'da fuskarta data sa take..Wato Sukainat rashin mutunci naki haryakai ki iya bude baki kizagi Nadiya agabana,kinsan irin matsayin datake dashi acikin zuciyata?,tunkafin na aureki na fada miki zaman lafiya nake bukata acikin gida na,bana son tashin hankali komai 'kan'kantar sa?Sannan tun kafin in aureki nafada miki ba wai dan Nadiya bata faranta min bane yasa zan aureki dan raya sunnar ma'aiki(S.A.W) yasani kara aure"saboda haka kiki yaye duk wani Abu dakikasan ze 'bata mata rai wannan yazamo shine karo na karshe da zansake yimiki kashedi akan Nadiya"Maza kitashi kije kibata hakuri akan bata mata rai da kikayi muddin kinason mishurya dake.Hawayen datake boyewane sukayi nasaran zubowa Cikin muryan kuka tace anma ai ita tafata zagina meyesa alokacin bakace tabar zagina ba,se yanzu zakace inbata hakuri bayan ita tafara,karfa ka manta Uba befi Uba ba dan haka ni babu wani hakurin da zann.....be bari ta karasa ba ya kwasheta dawani azabebben mari wanda seda shatin yatsunsa guda biyar suka fito a innocent face dinta.cike da bacin rai yace yaushe reni yafara shiga tsakanin mudake?, Har ina miki magana kina mayarmin saboda nazama tsaranki,wlh inbaki tashi kinje kin bata hakuri ba Sena yi miki abinda bakya tsammani shasha kawai.Mikewa tayi tanajin jiri na 'din bata ga goshinta dake radadi tamkar anbarba'da barkono"Cikin wani raunanniyar murya tace wlh bazan iya zuwaba jinake kamar kaina zefashe. "Wlh ko mutuwa zakiyi sekinje kinbata hakuri ni zaki rainawa hankali yafada atsawace"Da 'kyar take iya 'daga 'kafanta sakamakon duhu daya lullu'be mata idanu,tana zuwa kofar bedroom tayanke jiki tafa'di"Ihun azaba tasanya tare da dafe kanta hawaye na malala daga idanunta.Wani dogon tsaki Ahmad dake bayanta yaja ke banason munafurci da rainin wayo nizakiyiwa pretending wlh kokitashi kije kibata hakuri kokuma inyi miki abinda bakiyi zatoba!!Jin taki tanka masa ne yasanyashi sanya kafa yatake hannunta cike da mugunta, ga mamakinsa ko matsawa batayiba dan haka ya tsugunna ya dagota,gani yayi takoma baya, kanta yasake ido yazare cike da ru'du yasanya kunnensa ahancinta jiyayi bata numfashi,Cikin sauri ya dauke ta yadaurata akan bed sannan yadebo ruwan sanyi ya yayyafa mata.Numfashi taja da karfin gaske kana tafashe da kuka mai ban tausayi"hannun ta yarike Cike da lallashi yace dama baki da lafiya ne baki fada Minba??,Duk da tana cikin zafin ciwo hakan behanata dago kai takallesa ba, cike da mamakin rainin hankali irinsa wai batada lfy natasanar masa ba tasake maimaiwata aranta,banza tayi dashi sema lafesa datayi da ido
"Ganin irin kallon data ke binsa dashine yasa yasha jinin jikinsa cikin wayencewa yace ki kwanta bari na hado miki tea yana gama fadin haka yafice dasauri" Ido Sukainat tarintse tanajin bakin cikin abinda Ahmad yaimata aranta koda wasa bata ta'ba zaton ze iya aikata rashin adalci agidan sa ba anma gashi tun ba'aje ko inaba tafara fuskantar kalubale...Ba dadewa Ahmad yashigo hannunsa dauke da cup da kuma table's mika mata yayi yace gashi kisha sekisha magani, bamusu takarba dan wani azabebben yunwa takeji gakuma zazzabi dake Neman rufeta"bayan tashan yene tasha magani takwanta zuciyarta cike da tunani kalakal,batada de kwanciya ba baccin wahala ya dauke ta....
Yana ganin tayi bacci yamike yanufi sashen Nadiya" 'Dakin 'ya'yansa yafara shiga time dayaje duk sunyi bacci"Rufo musu kofar yayi yawuce dakin Nadiya zaune yahangota kan tangamemen bed dinta, se danne danne take awaya ko kallon inda yake batayiba bare yasa ran zata amsa sallamarsa,ganin haka,yasa yashige toilet batare dayace da ita komai ba,wanka yayi yafeshe jikinsa da turaruka masu dadin kamshi bayan yagama kintsawa ne yamatso kusa da ita ya zauna" hannu sa yasanya yajuya da fuskarta zuwa tasa cike da lallashi yace haba gimbiyar mata Uwar yaya na Abin alfaharina,karfaki manta kece sarauniyar dake mulkin zuciyata duk wata mace dazata shigo cikin fadarki to baiwar kice domin ke dayace sarauniya acikin masarautar ina fatan zanga murmushi daga fuskar matar da tafi duk matan duniya kyau da ado"Wani irin runguma tayi masa tana kyalkyale dariya tace harnaji sanyi acikin raina,murmushin samun nasara yayi yace kokefa inkina dariya bakiga yanda kike kara kyauba.Batace dashi komai ba se zama data gyara tana fuskantar sa,shima zama yagya yana me maida hankalin sa kanta"Gyaran murya tayi tace Honey Maganan raba kwana da akiye kwana bibbiyu ne kamar yanda kasani mafiya yawan mata haka suke yi, toni gaskiya babu tsarin kwana bibbiyu anawa ra'ayin dan haka nayanke cewa kwana 'da'd'daya zamurikayi ma'ana tayi girki yau inyi gobe,kaga nayi yau toh gone zata karbi girkinta dan haka sekasanar da ita tun wuri takarashe tana wani daure fuska dan karya ki amincewa.Murmushi yayi yace tunda hakan ya mike shikenan zansanar mata"fadawa tayi jikinsa tace ngd da wannan kauna Honey Allah yabarmu tare "Ameen y amsa yana me gyara kwanciyar sa matsawo tayi tarungume sa da haka bacci yadaukesu...
Chapter 10 · 0% Book details