← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 38

Sashe 34

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahmad Na ganin Alh Ali tsaye da Sukainat abayansa seda hanjin cikinsa takada tsaban furgici da ru'du,domin yasan halin baffan nasa muddin ransa yabaci ze Iya yin komai musamman ma ace bakada gaskiya.Cikin dauriya yace"barka da zuwa Baffa...Kafin ya karasa Alh Ali ya kwashesa da wani razanen nen mari amatukar fusace.Ba Ahmad ba hatta Sukainat dake bayan sa se da tarazana da Marin, bata taba zaton zafin mutumin yakai haka ba,batasake tsinkewa ba seda taga yasake kifa masa wani Marin daya fi na farko.Cike da bacin rai Alh Ali yace"Ashe Ahmad baka da mutunci?nizaka ciwa mutunci ka wulakanta Ahmad!? inje har gaban iyayen yarinyar nan subani ita nadawo maka da Ita shine zaka wulakan tata saboda ba ni dakima da daraja a idanunka??yakarashe cikin hargagi tamkar zetsaga gidan.Shiru Ahmad yayi tamkar ruwa ya cinyesa yakasa koda daga kansane tsaban bakin ciki tunda yake da baffan sa betaba sanya hannu ajikin sa da sunan duka ba se yau ta dalilin Sukainat, ji yayi zuciyar sa tayi bakikkirin yayinda tsanarta kesake mamaye zuciyar sa.

Jin kamar haya niya na tashi a compound din yasanya Hjy kultum da Nadiya fitowa cikin sauri dan ganin meke faruwa.Ganin Alh Ali tsaye fuskarsa amurtuke, yasanya su dedeta nutsuwarsu domin duk abinsu suna shakkarsa.Karasawa wajen Hjy kultum tayi cikin girmamawa tagaishe sa,adakile ya amsa batare daya kalle taba"Dan Allah kakaraso mushiga ciki Alh tace"dashi,banza ya mata seda tasake maimaiwa kafin yawuce batare dayace da ita komai ba"bayan sa sukabi suka dun guma parlour.

Bayan sun zauna ne Alh Ali ya kalli Hjy kultum da alamun bacin rai afuskarsa yace"a gaskiya kultum kinbani mamaki da girman ki da tunanin ki kike aikata Abu irin na yara kanana!? koda wasa akace min zaki iya aikata abin da kikayi bazan yadda ba segashi kin aikata,Ina hankalin ki da tunanin ki yaje alokacin da kike wannan katobaran"Bejira jin abinda zatace ba yaci gaba da cewa kultum kada ki manta yaya da dukiya ba a muguntar su sannan nasan bazakiso a aikatawa diyarki haka toh shin ke meyesa kike aikata haka ga 'diyar wasu kokina tunanin ita iyayenta basa kaunar tane kamar yanda kowasu iyaye ke kaunar 'ya'yan su...Cike da takaicin yanda yake mata sababi agaban suky tace"Alh Wallahi bakasan halayyar wannan makirar yarinyar bane,gabaki daya ta wargazawa Ahmad gidan sa tunda ya aureta yafara haduwa da masufu iri iri gaba ki daya nema take ta susutar min da yaro ga asara daya sakosa agaba aharkan kasuwanci bayan kuma da baya fuskankar hakan aharkokin sa wannan ba irin alkhairi bace kana ganin ta...Subhanallah!!Alh Ali yafada rai abace ,haba kultum meyesa bakida lissafine??kina Abu kamar wata yarinya karama taya zakice haka, Allah shike azurtawa asanda yaso yakuma kwace asanda yaso meyesa bazaki yadda da kaddara ba wannan yarinyar bata Isa tasa Allah yakwace arzikin daya baiwa Ahmad ba dan haka ki watsar da wannan camfin.
Baki Hjy kultum tatsuke alamar duk maganga nunsa basu shige taba.

Juyawa Alh Ali yayi yafuskanci Ahmad "Cikin kakkausan murya yakira sunansa"amsawa yayi kansa akasa.Ahmad katuna cewa wannan yarinyar amanace awajenka muddin kazalin ceta Allah baze taba yafe maka ba,domin matan mu da 'ya'yan mu kiwo Allah yabamu kuma seya tambayemu abisa kiwon daya bamu dan haka kakula kada Allah yatasheka gefe daya ashanye abisa rashin adalci daka keyi atsakanin su,sosai yashiga yi musu nasiyya me ratsa jiki anma baki daya tabayan kunnen su maganan yakebi.Cike da ladabi Ahmad yace"Dan Allah Baffa kayi hakuri in Allah ya yarda irin haka baze sake faruwa ba zankula yanda yakamata.Allah yasa cewar Alh Ali yana kallon Hjy kultum da Nadiya.murmushin dabe wuce saman labba ba Hjy kultum tayi yace"Mungode da wannan nasiyya taka kuma insha Allah zamu kiyaye Allah yabar zumunci."Kallon Sukainat yayi Wanda tunda suka shigo kanta nakasa yace" kiciga ba da hakuri 'ya ta Insha Allah kece da nasara domin mahakurci wataran zema mawadaci.Mikewa Alh Ali yayi yana tattare babban rigansa yace Nabarku lafiya bawanda yayi magana acikin su se Sukainat datace nagode Baffa Allah yakara girma da daukaka"Ameen ya amsa yana me ficewa...

Ahankali tamike da niyyan tafiya sashenta bayan fitar sa"Dawo ki zauna bakar munafuka annamimiya mekama da aljanu muryan Hjy kultum yadaki dodon kunnen ta..Jitayi kafafunta sun gaza daukar ta dafe kujera tayi tazauna tana karanto duk addu'ar datazo bakin ta.Mikewa Hjy kultum tayi ta Isa inda take Hannu tasanya tarike kunnen ta dake Cikin hijab cike da tsanar ta tace"ke annamimiya wato harkin kai matsayin daza kidinga kai kararmu ko!?,Nadiya da tunda akafara magana batace komai ba seyan zu tadago kai adakile tace"ai muddin ba atakawa wannan bakar munafukar burki ba nanga ba setayi abinda yafi haka!.

Shiru Sukainat tayi kanta akasa burinta kawai su sallameta tatafi.Kallon Ahmad Hjy kultum tayi tace"Ahmad anata magana bakace komai ba, rai abace yace"Hjy Wallahi bansan wani irin hukunci zan yankewa yarinyar nan hankali na yakwanta ba shiyasa kikaga nakasa cewa komai yakarashe cikin kunan zuciya...Shiru yayi nawasu mintuna kafin daga bisani yace"Na rantse da Wanda raina yake hannunsa koda wasu kikasake daukan sirrin gidan kika kai waje sena dauki tsatstsauran mataki akanki Wanda ko karene baze daukaba domin sena wulakanti jahila kawai annamimiya ki bace min dagani kafin in kyafta idanu.Cikin sauri tamike tafita tana mai yiwa Allah godiya dayasa basu taba lafiyan ta ba..

Bayan fitarta Hjy kultum da Nadiya suka dinga ingiza Ahmad kan yadauki tsatstsauran mataki akanta aduk sanda tasake zuwa takai karansa"kwafa yayi yace"Wlh Hjy nasan muddin nasa Hannu na ajikinta da sunan duka sena kasheta shi yasa na kyaleta.kayi tunani mekyau anma nan gaba tasake kwatanta irin haka kada ka kyaleta...

_VOTE COMMENTS AND SHARE_

*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???.*
_(True life story)_

_Na Marubuciya_
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD*
_Realeshaa_

_Like my page on Facebook_👇🏻

https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai kaske kabarinsa ya Allah kajikan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

*PAGE 53&54*🖊️

_________________________📖 *Bayan wata daya:*
Rayuwar gidan Ahmad yayi wa Sukainat zafi kullum Cikin bakin ciki da kuncin rayuwa take, tashin hankali da masifu babu kalar da bataga ni daga wajen Ahmad da Nadiya daga wannan se wannan duk tadawo kalar tausayi komai rashin imanin ka/ki idan ka kalli halin datake ciki seka tausaya mata.Bata da kata'bus da zatayi Wanda ze nuna cewa Ita matar gidan ce sede baiwa baiwar ma makaskanciya wacce basu da tushe...Domin shigarta da kuma aikinta kadai ze tabbatar maka da bakaramin bautu wa take ba."
Tayi baki tarame idanunta sun koma ciki ciki kana sundanyi ja saboda tsananin kuka datake har kasan idanunta sun dafe tayi wani irin canzawa kamar wacce tayi shekara da shekaru acikin jinya.

Nadiya takafa kujeran mulkinta agidan seyan da taga damar juya kambunta itake tsara musu komai acikin rayuwar su daga Sukainat har Ahmad se abinda da tace zasuyu."Ganin wannan dama da Nadiya ke da shine yasanya ta shiryawa Sukainat tuggu kala kala awajen Ahmad da farko se tace"dashi akullum dayasa kaga yafice Sukainat zatabi bayan sa bazata dawo ba har seta Dede ci lokacin daya kusa dawowa kafin tadawo idan kuma ta tambayeta daga inatake seta hau kanta da zagi da fada shuyasa tafita hanyar ta anma tafada masa ne dan yadauki mataki akai.Lokacin data gama sanar wa da Ahmad wannan maganan ransa bakaramin baci yayi ba,dan kalaman Nadiya bakaramin tunzura masa zuciya sukayi ba akan abinda suky ke aikatawa hakan yasa yasamu Sukainat yamaita dukan tsiya Wanda koda daga yatsartane takasa bare kuma ace tatemaki kanta,seda yaga ko motsi batayi yabarta.

Bayan wannan yawuce ba dadewa Nadiya tasake dana mata tarko Na biyu kancewa akullum kafin magriba sewata mace tashigo cikin gidan sushige dakin Sukainat suyita shirya makirci kalala kana daga bisani suyita bunka maka sihiri suna kiran sunanka ,taci gaba dacewa alokacin dataga haka hankalinta bakaramin tashi yayiba shiyasa tayi gaggawan sanar masa dan yadauki mataki aikuwa nan ma haka yaje yasamu Sukainat yayita dukan ta kamar Allah ne ya aikosa tare da hanata abinci Na tsawon yini daya yakuma ce inwata tasake shigowa cikin gidansa adalilin ta seya karairayata ko laluran cikin dake jikinta basu ganiba suke azabab tar da ita.Wannan magana dayayi yasa Sukainat hana kowa nata zuwa gidan tasanar dasu kancewa tayi tafiya...

Rayuwar Sukainat yadawo abin ban tausayi ga duk wani mai imani dakuma tausayi duk Wanda yasanta ada yakuma ganta seya zubar da hawayen tausayin ta kana zeyi wuya yaganeta sede in farin sani kai mata shine zaka ganeta, hakika ko makiyin tane inde yana da digon imani a zuciyar sa to ze tausaya mata halin datake ciki bare kuma ace masoyan ta.Wannan dalili yasanya takasa sanarwa da iyayenta halin datake ciki kasancewar tasan hankalin su bakaramin tashi zeyiba idan sukaji halin datake ciki kuma babu wani mataki dazasu dauka face hakuri dazasu bata wannan dalilin yasanya ta shanye takaicin datake ciki takuma fawwala Ubangiji lamuran ta domin shi ka'dai ne ze iya yaye mata kuncin rayuwar datake fuskan ta agidan Ahmad.

Abangaren Nadiya kuwa burinta yacika domin se abinda tafada acikin gidan akeyi wannan dalili yasanya Nadiya yin abinda taga dama kasancewar baki daya ragaman gidan Na hannun ta. Ayanzu matsalan ta dayane ganin haryanzu Ahmad be saki Sukainat ba duk dakuwa irin wulakanci datake sanya shi yamata kan koza tanemi saki da kanta anma baki daya abin yaci tura wannan abin ne in tatuna yakesa ke sata jin tsanar Sukainat dakuma gallaza wa rayuwar ta fiye da tunanin mai tunani.Ganin duk irin cusguna war datake wa Sukainat taki tafiya yasanya ta fitowa da sabbin hanyar wulakan ta rayuwar ta tahanyar bautar da ita da ayyukan cikin gidan.kama daga wankin kayansu duk dakuwa cewa a akwai washing machine anma Nadiya tace"baza ayi amfani dashi ba tunda suna da baiwa,haka zalika sharan compound din gidan itakeyi duk dakuwa girman sa itakeyi,batun girki kuwa ba a magana domin rabon da Nadiya tayi girki har tamanta komai Sukainat keyi koda abinci tagama bata Isa taciba setajira Nadiya ta dibar mata wataran ko isarta bayayi haka za atsakura mata duk ranan datayi ganganci ci batare da sunsani ba kuwa insuka gane tofa seta karbi tsatstsauran hukunci...
Chapter 34 · 0% Book details