← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 38

Sashe 33

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai yadafe cike da tunani,besan mezece da baffan nasa inyagane karya yamasa.Jin karan knocking yasashi mikewa jiki asabule yanufi kofar yabude.Barka da zuwa baffa yafada a lokacin dayake kokarin rufe kofar dan tuni Alh Ali yashige ciki.seda yazauna kafin yace"ina matan gidan??Cikin inda inda yace"bari inkira maka su yanagama fadin haka ya nufi bedroom din Nadiya kwance yasameta tana latse latsen waya,My Queen tashi muyi magana banza tayi masa kamar batasan Allah yayi halittarsa awajen ba, cikin sanyin murya yafara lallashin ta tare dayimata alkawarin zekareta awajen dakyar tahakura tabi bayan sa.Akan 2siter tazauna adakile tagaishe da Alh Ali kamar wacce akaima dole,se wani huhhura hanci take, amsawa yayi batare daya kalleta ba...

Ahmad kuwa Ahankali yake knocking din kofar Sukainat gudun karya yi da karfi Alh Ali yaji ya fahimci wani Abu anma yafi sama da minti goma beji alamunta taba hakan yasa yakoma jiki amace dan beson yagane da akwai matsala.Kallon sa Alh Ali yayi yace"ina ita suky din cikin rawan murya yace" Wallahi taki bude kofar Baffa.

Shikuwa Alh Ali bece komai ba yasanya hannu acikin aljihun babbar rigansa yaciro wayarsa,number Sukainat yakira...

Sukainat kuwa duk buga kofar da Ahmad keyi tanajinsa banza tayi masa dan tasan muddin ta bude wulakanci da tozarci ne zebiyo baya hakan yasa taki budewa,tana kwance taji ringing din wayarta hakan yasa tamike tadauka,Ganin mai kiran ne yasata saurin dagawa kamar yana gabanta haka tagaishesa cike da ladabi amsawa yayi cike da kulawa kafin yace"tasameshi a parlour Nadiya, Cike da mamaki ta amsa da gatanan zuwa aranta tana mamakin abinda yakawo sa.Dogon hijab tasanya akan dan figigin rigan baccin dake jikinta kana tafito Cikin nutsuwa tanufi sashen Nadiya yayinda zuciyar ta ke bugun tara-tara dan batasan me zata tarar ba....

Da sallama dauke abakin ta tashiga Alh Ali da Ahmad ne kawai suka amsa mata yayin da hakimar tacure baki waje daya tare da kankance kananun idanunta alamar rashin mutunci.Cike da girmamawa Sukainat tagaishe da Alh Ali kanta akasa,amsawa yayi yana mejin tausayin ta har kasan ransa.
Gyaran murya yayi tare da kallon Ahmad yace" mai maita abinda kafa da min awaya,yafada babu alamar wasa atare dashi....

_VOTE COMMENTS AND SHARE_

*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(True life story)_

*Na Marubuciya*
_REAL ESHAA ~_

*WATTPAD*
_Realeshaa_

_Like my page on Facebook_ 👇🏻

https://www.facebook.com/REAL-ESHAA-FANS-114689303720405/

*_Ya Allah mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

```Dan Allah masu cewa ga yanda zanyi suyi hakuri subarni in karasa labarina a yanda nafara be kamata ace Ku zakuna fada min abinda zanyi ba wacce taga zata karanta ayanda natsara fakat wacce bazata Iya ba kuma seta hakura anma dan Allah kidena yimin kutse cikin lamarina 🙏🏻🙏🏻🙏🏻```

*PAGE 51&52*🖌️

_______________________📖Murmushin samun nasara tayi kafin tace"Shin awatan nin baya irin haka nafaru da kai!?Batajira jin amsar saba taci gaba dacewa Katsaya kayi tunanin meyesa se ayanzu hakan ke faruwa dakai,Na tabbata zaka gane inda maganata tadosa.
Shiru yayi nawasu mintuna yana nazarin maganin ta,ganin bai tuna komai bane yasanya cewa"A gaskiya niban fahimci komai ba, kawai de nasan kaddara ce tafado min kuma ina fatan Allah yamayar min da alkhairi dama shi kasuwanci yagaji haka bazeyu ace kullum mutum na samu ba dole wataran seya rasa.Kai Hjy kultum tajinjina cike da gamsuwa da maganan Ahmad tace"Kwarai kuwa dama shi kasuwanci yagaji haka wata ran samu wata ran rashi,inde ba ma hassada ke yimaka jifa ba to bana tunanin wani abu daban,dan haka seka dage da addu'o'i inma wani sharrin suke binka dashi zeko ma musu kansu kaciga ba dayin addu'o'i dan shine mafita.

Haushi ne ya tokarewa Nadiya makoshi,jitake kamar ta makesu dan takaici ganin basu fahimci abinda take nufi ba.Danne bacin ranta tayi tace"Hjy wai kina nufin kema baki fahimci abinda nake nufi ba?,ko dayake shikenan tunda baku fahimta ba abar maganan!.Cikin sauri Hjy kultum tace"Kamar ya abari ai seki yimana bayani yanda zamu fahimta inkinsan wani Abu akai,ko baha kabane Ahmad takarashe tana juya akalar tambayar kansa.Kai ya jinjina alamun hakane.Zama tagyara kafin tace"Ni azatona aduk maganan da akeyi agari yana kunnen ku,kancewa Sukainat farar kaface!,Domin gado tayi wajen mahaifiyar ta, dan lokacin da babanta ya auri mahaifiyar ta yanada dukiya anma tunda tashiga gidan yafara rasa komai seda yatsiyace kaf yadawo bashida komai shi yasa Dadyn rufy nazuwa Neman Aurenta suka bashi saboda sunsan insukaja lokaci za'a fasa dan za a Iya fada masa abinda ke damunsu...Hannu Hjy kultum tadaga mata dasauri tace"base kin karasa ba nariga na fahimci abinda kike nufi,anma meyesa baki sanar damu tun kafin ayi auren ba?Cikin yanayin damuwa tace"Hjy ai a wannan lokacin kona fada bazu yardaba cewa kazuyi kishine.Haba Hjy kultum tarike cike da jimami tace"Wannan yarinya akwai tsinanniya,Mara imani saboda zalinci irin na iyayenta sunsan annoban dake damunsu shine zasu kakabawa Dana!?toh Wallahi bazata sake koda minti daya ne acikin wannan gidan ba seta fice"Cikin bada goyon baya Ahmad yace kin kyauta Hjy tunda aka munafurceni toh bazata zauna min agida sutalau tani ba dole takoma gidansu.Dolen ta mata fice ai cewar Hjy kultum gama fadin haka tamike afusace tanufi sashen Sukainat...

Sukainat nashiga daki tawuce bedroom dinta direct, kwanciya tayi da hijabin batare data cire ba hawaye na kwaranya daga idanunta dasuka kankance saboda kuka tarasa me ta tsarewa Hjy kultum aduniya databi tadaura mata karan tsana,komai tayi bata burgeta sede hantara da kyara yabiyo bayan abin alkhairi da mata...

Tana Cikin wannan tunanin taji an fincikota da karfin gaske seda tafadi kasan tiles din.Cikin hargagi Hjy kultum tace"tashi kifita tunda ba gidan uban kiba ne yar matsiyata! mai farar kafa!,baki isa ki talauta min da ba kamar yanda uwar ki ta talauta ubanki dan haka dole kibar min gidan dana takarashe tana me fincikar ta da karfi...Kuka Sukainat tafashe dashi tare furta _(Alhumma ajirni fi musibati wa'ahlif khairan minha)._ Mari Hjy kultum ta kwada ma tace"dan ubanki nice masifar!?Toh kome zakiyi se kinbar min gidan dana Wallahi!, maza wuce Irin jaraba tafada tana hankada keyarta zuwa waje.Hannu Sukainat tasanya tadauki wayarta dake kan beside drawer, tafice Hjy kultum na bayanta tana tura kayar ta.Seda takaita Har kofan gate din kafin tadawo.

Kai Baba mai gadi ke girgizawa cike da tausayin yarinyar hakika da'ace shi wanine toh daya bawa iyayenta shawaran su dauketa takoma gabansu,dan muddin taci gaba da zama agidanan wataran sede abude kofa atsinci gawarta ciwon zuciya yakasheta,sede kash!!shi ba kowa bane daze Iya bada wannan shawaran, Anma hakika yana tausayawa rayuwar ta shida yake mai gadi ma yafita samun kwanciyar hankali da nutsuwa...

Direct sashen Nadiya Hjy kultum takoma tana kumfar baki.Kallon ta Ahmad yayi yace"Hjy ina fatan kinfitar min da ita daga gida?,Kai ta jinjina tana haki tace"Wallahi Ahmad narasa a inda ka kwaso wannan annobar da hannunka dakuma kudinka.Cikin sauri Nadiya tace"Hjy nifa ina tunanin ba ahaka banza ya aureta ba da asiri suka hada in ba haka ba mezeyi da ita irin masifa!.Kai Hjy kultum ta jinjina tace"shakka babu maganan ki gaskiya ce da akwai mana kisar dasuka kulla karfin auren.shide Ahmad shiru yayi besake cewa komai ba baki daya hankalinsa yatafi wani tunanin daban.Zama Hjy kultum tagyara amaimakon tatafi kamar yanda tayi niyya seta fasa acewarta se bayan sallan isha...

Sukainat nafita tanemi waje tazauna tana tunanin inda zataje a yamman nan,tasan muddin takoma Gida acikin wannan halin datake hankalin iyayenta zetashi,takuma sanya su cikin damuwa.Hakan data tuna yasanya ta yanke shawaran da zuciyar ta kebata kan tasanar wa da Alh Ali. Shawaran zuciyar ta tabi tashiga contact dinta tafito da number sa ta danna kira.Ringing daya Alh Ali yadauka fuska asake ya amsa sallamar ta.Cikin rawan murya tagaishe sa,Am sawa yayi yana yana tambayar ta lafiya jin yanda muryan ta kerawa!?.Kukan datake kokarin danne wane ya samu nasaran subce mata tashiga rerewa cike da tausayin kanta...Cike da damuwa yace"yata me yasa meki?,Kiyi shiru kisanar dani damuwar ki insha Allah zan miki maganin matsalarki.Kasa tsayar da kukan tayi sakamakon wani Abu me nauyi daya tsaya mata akirji.cikin muryan lallashi yace"kiyi shiru kisanar dani abinda ke damunki,ko Ahmad ne ya miki wani abu kisanar min nayi miki alkawarin hukunta sa dade da lefin sa!".Da kyar ta iya tsagaita kukan tana Jan zuciya tashiga labar tamasa abinda yafaru tun farko harzuwa yanzu da Hjy kultum takoreta...

Kai Alh Ali yake jijjigawa Rai amatukar bace yarasa yaushe Ahmad yazama Mara imani da tausayi,Danne bacin ransa yayi yashiga bata hakuri,tare dacewa tajira sa awajen gashi nan zuwa.
"Bayan takashe wayar ne takife kanta akan cinya tashiga rera kuka meban tausayi a zuciyar duk wani me tausayi...
Ba adau lokaci ba Alh Ali yakaraso,awaje yayi parking motarsa daga can gefe ya hangota tahada kai da gwiwa da alama kuka take.Fita yayi amotar yanufi inda take,Sunanta Yakira cike da tausayin ta hakika yana tausayawa rayuwar yarinyar domin ya fahimci batada kwanciyar hankali agida.Dago kai tayi tana share hawayen dake fuskarta,Cikin sanyin murya yace" taso mushiga.jiki amace tamike tabi bayan sa tana tsoron abinda zata tarar aciki.

Tun kafin suka rasa shiga parlour sukajiyo sautin dariyar Hjy kultum da Nadiya tamkar zasu tsaga gidan.takaicine ya tur nukewa Alh Ali makoshi Sam yarasa kultum wace irin macece Mara tunani da hangen nesa.
Cikin kakkausan murya yayi sallama tare da jiran izinin shiga,Ahmad ne yamike yanufi kofar dan ganin ko waye kasancewar basu gane muryan sa ba.
Chapter 33 · 0% Book details