← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 38

Sashe 17

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

****
Yana fita direct motarsa yashiga,driving yake anma baki 'daya zuciyar tsa cike da was-wasi yake yakasa nutsuwa zuciyar sa se sa'ke-'sake take masa gameda kalaman Sukainat yarasa wanne zeyi amfani dashi,!zuciyar sa yakasa hakuri da sunayen data kirasa dashi abaya.Yana isa gida yayi parking direct sashen Nadiya yanufa,harzuwa lokacin basu tashi daga bacci ba, tashinta yayi kafin yashiga toilet yawatsa ruwa cikin 'kan'kanin lokaci yafito yashirya cikin kananun kaya bakin jeans da White t-shirts bakaramin amsar jikinsa kayan sukayiba, dadda'dan tularensa yadauka yashefe ilahirin jikinsa dasu...Ido Nadiya ta'kura masa ko 'kyaftawa batayi, ganin irin kyan dayayi tamkar dan shekara ashirin da takwas" 'karasawa gabanta yayi da 'kayataccen Murmushi a fuskarsa yalakace mata hanci cike daso yace wannan kallon fa my Queen??, Fari tayi masa da 'kananun idanunta tace ina Kallon mijin dayafi ko wani 'da namiji kyau da aji je aduniya..Dariya yayi Wanda ya bayyanar da fararen hakoransa yakuma lotsar da dimple dinsa yace banda San Kai",ido tasake kuramasa ganin yanda ainihin kyawun sa yasake fitowa tace bawani San kai gaskiya nafada..Kallon ta yayi anutse yace shirya mutafi asibiti,dasauri ta kallesa tace waye ba lafiya Allah yasa de ba Hjy bace!!Baki ya ta'be yace Sukainat ce ba Hjy ba,yasalam meke damunta haka honey??Kede shirya mutafi,zatakara magana yadaga mata Hannu yace kije kishirya kizo mu je kigani.Jiki asanyaye tamike tashiga toilet. Batadau dogon lokacin ba tafito anma kafin tagama shiryawa se goma,Kallon sa tayi tace muje ko?,mikewa yayi batare dayace komai ba yanufi hanyar fita,hannunsa tarike tace honey haka zamuje ba komai ahannun mu??,Kallon ta yayi yace Kamar ya??breakfast tace dashi"Kai ya dafe yace na manta anma muje se musiya a restaurant kinga lokaci yawuce,kai ta girgiza tace no ba za'ayi ahaka ba, kabani minti ka'dan Yanzu zangama,bata jira jin abinda zeceba tawuce kitchen tabar sa awajen...Zama yayi yana latse-latse a wayarsa se misalin karfe,shabiyu tafito hannunta dauke da babban basket da warmers aciki.da Murmushi a fuskarta tace nadade ko Honey??, Kayataccen Murmushi yasakar mata yace no ai girki is not easy namaga saurin ki, muje ko yafa'da yana karban basket din hannunta, bashi tayi,tanayafa mayafinta, fita sukayi zuwa parking space key yasanya yabude motar, mazaunin driver yashiga itakuma tazagaya dayan side din tazauna key yayiwa motar suka nufi hospital...
Se misalin shabiyu da arba'in suka isa hospital din,bakinsu dauke da sallama suka shiga,tunkafin sukarasa shiga sukajiyo dariyan Sukainat natashi sama-sama"dasauri Ahmad yakarasa shiga dan ganin da wa take wannan dariyan".Sofi'a da mahaifiyar ta yahango sun sanyata atsakiya sehira suke cike da farin ciki,tsaki yaja aransa yana binsu da mugun kallo"Hjy Amina ce ta daga kai bayabo ba fallasa ta amsa musu sallaman tare da maida hankalin ta kan warmers din dake hannunta tana zubawa Sukainat peper soup din kayan ciki.murtuke fuska Ahmad yayi yayinda ya karasa cikin dakin,kujera yaja yazauna kafin Nadiya tashigo kusa dashi tazauna tana binsu da wani kaakantaccen kallo ta kasan ido,kamar Wacce aka tilastawa haka tagaishe da Hjy Amina "Amsawa tayi batare data kalletaba domin Hjy Amina irin matan nan ne dabasa daukar reni komai kankantarsa."Sarai Sofi'a taga irin kallon renin dateke binsu dashi anma se tadanne zuciyar ta tace ina kwananku"Daga Ahmad Har Nadiya babu Wanda yaimata amsawar mutunci,Musamman ma Ahmad dan wani irin haushinta yakeji, yafuskanci yarinyar batada kunya ko ka'dan" Juyawa bangaren dasuke sukainat tayi ba walwala a fuskarta tagaishesu.banza suka mata hakan yasa takauda kai suka cigaba hira tsakanin su batare dasun sake bi takansuba.Wannan shariyar dasuka musu bakaramin 'konawa Nadiya zuciya yayiba dan haka ta kalli Ahmad tace Honey nizan koma gida,tunyan yace da ita yana nazartan yanayin ta, rau rau tayi da Ido tace"eh gwanda intafi tunda Wanda nazo dansu basu sani ba tana gama fa'din haka tafice,dasauri yabi bayan ta,tsaki me karfi Sofi'a taja wanda yasa Ahmad tsayawa harzeyi magana kuma yafasa,yafice cikin kunan zuciya.Jikin mota yahangota tajin gina bayanta hawaye 'daya nabin 'daya.....

_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_

*_ESHAA CE ~_*🤙🏻
*KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_

*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD* _Realeshaa_

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*

```Kishiya ko Baiwa Fans hakika inajin dadin comments dinku 100℅ Kuyi hakuri da rashin amsa muku comments da bansamu nayiba ina busy ne anma hakika comments dinku nasanya ni nisha'di Nagode😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘```

*PAGE 29&30*🖌️

________________________📖Hannu yasanya ya'bude motar kana yasanyata abaya shima ya zagaya yashiga kusa da ita yazauna.Tallafo ta jikinsa yayi Cikin muryan lallashi yace am so sorry my Queen pls kidena zubarmin da Wannan tsadaddun hawayen naki jinake kamar wuta ake watsamin aduk lokacin dazanga kina hawaye zanyi fansar da komai domin hawayen ki su tsaya"Cikin sheshekan kuka da kissa tace honey bansan menatsarewa Sukainat da yan uwanta ba,baki daya duk l sun tsaneni ko Kallon fuskata basu kaunar yi,sunbi sun 'dauramin karan tsana, irin wannan halin ko inkula dasuka nuna min yanaci min tuwo a'kwarya,me natsare musu arayuwa dasuke son ganin bayana burin su bewuce suga sun kuntatawa rayuwata ba nalura sosuke infita inbar musu gidan!!??.Rungumeta yayi yana bubbuga bayanta alamar rarrashi sundauki kusan minti goma ahaka, sedayaji tadena kukan kafin ya cireta daga jikinsa yana kallon fuskarta cikin sweet voice dinsa yace,kijirani anan yace da ita yana fita daga motar.Da kallo tabi bayansa harya shige cikin hospital din"wayar ta dake cikin hangbag tayi saurin cirowa,number Hjy kultum takira ringing biyu tadauka,da fara'a Hjy kultum tace lafiya lau Nadiya ya mai gidan da 'yan jikokina"Duk muna lafiya yanzu ma kiranayi inyi miki albishir Hjy.Baki Hjy kultum tawashe tace toh inaji,Kin kusa samun jika tace da ita tana son jin abinda zatace"Cike da farin ciki Hjy kultum tace kai masha Allah anma naji dadi sosai anjina zanzo indubaki Atika da jumi dake gefe sukayi saurin cewa Hjy kuma zamu biki,kai tagya'da musu alamar toh"Ai Hjy banice keda cikin ba! auntyn su Rufaida ne,wani dogon tsaki Hjy kultum taja Wanda yasa Nadiya saurin janye wayar daga kunnenta tana kunshe dariyar dake cinta.Cike da Bacin rai tace Innalillahi, anma nayi bakin cikin jin Wannan maganan me za'ayi da Wannan irin rashin tarbiya yarinyar dabata ganin mutunci kowa yaushe zakaso ha'da zuri'a dasu Nide Ahmad be kyauta minba daya dibomana irin wannan jaraban da tsiya..Hmmm Hjy bazakisan wanna yarinyar bada zuciya daya suke son dadyn rufy ba se kinji abinda suke fada itada yan uwanta"Basusan ina kusa ba hadda cewa wai Wannan cikin shine zasu samu damar tatsarsa yanda suke bukata,wlh Hjy baki daya hankali na atashe yake kar suje su yita yashesa.'Kwafa Hjy kultum tayi tace ki kyalesu ni nasan yanda zanyi dasu,Toh Hjy Allah de yasa adace dan wlh ina cikin matsala damuwa"Karki damu nasan abinda zanyi Allah yamiki albarka duk abinda kikagani bakiyarda daahiba atare dasu kisanar mana"Ameen ta amsa kana tace insha Allah duk abinda nagani zakisani tana piñata sallama tayi mata sannan takashe wayar.Kallon atika da jumi Hjy kultum tayi Cike da 'bacin rai tace Wannan yarinyar ba karamar she'daniya bace,Muddin bata bini Ahankali ba wlh za aga surukar banza dan wlh se nayi mata dukan tsiya sannan tattara yanata yanata, tabar gidan tunda bana Uban ta bane 'Yar matsiyata kawai,me za'ayi da wannan zuri'ar tsiyar"Atika dake duk tafi jumi zafi tace Hjy bar yar kutumar Uba wlh senaje Har gidan nacimata mutunci,irin tsiya da jaraba bansan me Yaya yagani ajikin Wannan yarinyar mekama da Yunwar kenya ba Har ya aureta nifa ina shakku ma Anya dasaninsa ma ya aureta ba asiri suka masaba??!,Dariya jumi tafashe dashi tace kai aunty Atika irin wannan ba'a haka??"tsaki Atika taja tace kede bar matsiyaci ya bansan ina ya Ahmad yahadu da wannan abinba kodayake ba abanzaba.Yanzu Hjy mekike ganin za'ayimata??Shiru Hjy kultum tayi nawasu lokacin kafin daga bisani tace kubari nasan matakin da zandauka...
Chapter 17 · 0% Book details