← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 38

Sashe 18

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda yashiga cikin hospital din direct office din Dr yanufa,bayan sun gaisane yanemi da Dr yabasu sallama"Kallon sa Dr yayi yace anma dakabari takara kwana daya dan jikinta yasake karfin dan gaskiya tana bukatar kukawa,"Kai ya girgiza yace No Dr kasancewar naga jikin dasauki kuma inada dalili mai karfi dayasa nakeso abamu sallaman, maganar kulawa kuma insha Allah babu wata matsala.Ok Allah yakara afuwa yakuma raba lafiya Dr yafada yana wasu yan rubucece rubuce yanagamawa yamika masa,yace pls kakula da ita yanda yakamata"karba yayi yaimasa godiya,sannan yaimasa bill din kudin sa yafice..
Fuskarsa babu walwala yashiga dakin datake"Still kamar yanda yasamesu da farko haka ma yanzu yasake tarardasu,Hira suke abinsu cike da farin ciki kamar ba a hospital sukeba bazakace Sukainat bace Mara lafiyar ba dan ta sake se walwala take abinta.Hjy ansal lamemu zamuwuce gida yafada asassauce dan wani irin kwarjini Hjy Amina tayi masa"Toh masha Allah haka akeso Allah yakara afuwa yakuma raba lafiya,kallon Sofi'a tayi tace Sofi'a tashi muje ko?"marerece fuska Sofia tayi tace anma momy yakamata muje mutayata zama idan yaso se dare mukoma gida"Hararanta Hjy Amina tayi tace ke bansan shashanci!! zakiwuce muje ko Yaya,?Kafin Sofia tace wani Abu Sukainat tayi rau rau da ido,cikin sanyin muryanta tace dan Allah momy kiyi hakuri mutafi tare,tafada tana langwa'bar dakai"ganin yanda Sukainat ta marairaice ne yasa Hjy Amina jin tausayin ta, toh kuwuce muje tace dasu tana Murmushi ganin yanda suka Rungume juna suna dariya.Wani irin takaici ne yakama Ahmad jiyake kamar ya makawa Sukainat mari" anma bece komai ba yafice afusace....Bayansa Sukainat sukabi itada Sofia hannunsu rike da juna,direct jikin motar Sofia tanufa tana zuwa tabude gidan gaba tace kawata bismillah,shiga Sukainat tayi tana sakar mata Murmushi.Dasauri Nadiya dake sit din baya tafito tana bin Sukainat dake gaban mota dawani shegen kallo, dauke kai Suky tayi tajingine bayanta da sit din tare da lumshe idanunta"Daga Hjy Amina har Sofia bawanda yabi takanta bare yace da ita wani abin,motar suka bude suka shiga baya...Wani irin takaici ne yaturnuke wa Nadiya zuciya ganin yanda suka maida ta mahaukaciya Kallon ta tamayar kan Ahmad dake kokarin zama mazaunin driver"Cikin kunan zuciya tace Honey a ina zan zauna kuma naga kana shirin tafiya kabarni?? ta'fada tana tsaye jikin motar,bece da ita komai ba yafito hannunta yarike suka koma gefe,komai yafada mata oho tadawo tashiga baya kusa da Sofi'a shi kuma yazauna amauzaunin drive yaja motar batare da ya kalli gefen da Sukainat take ba...Suna isa gida yayi parking,yafito Nadiya tabi bayansa sukashige sashen ta...Koda Sofi'a da Hjy Amina suka shiga sashen Sukainat shawarwari na nagari sukadinga bata Wanda zata karu dashi sukuma zauna lafiya da kowa dakuma yanda zata kula da lafiyar ta..Sosai taji dadin shawaran dasu kabata seyamma ci kafin suka tafi."Ahmad na ganin fitarsu yanufo dakin Sukainat fuskarsa amurtu'ke tamkar beta'ba dariya ba"Lokacin daya shiga dakin yayi dede da shigar ta toilet, daga ita se towel Wanda bewuce cinyar taba.Ido yakura mata yana Kallon baiwar Kiran jiki da Allah yamata,Ganin irin kallon kurullan dayake binta dashine yasata saurin kama handle din kofar toilet za tashiga"taku biyu yayi yafisgota zuwa jikinsa kankameta yayi yana binta dawani irin kallo mecike da shauki"Jinta afaffa'dan kirjinsa yasata lafewa tana shakan daddan kamshin sa"Jin yanda tanutsu tana sauke ajiyar zuciya akai akai ne yasa shi dago kanta yana Kallon ta,da Idanunsa dasuka rine izuwa begenta...Cikin wani narkakkiyar murya yace waya baki wayar dakika kira wa'accan mutanen??"Yi tayi kamar bata fahimci abinda yake nufiba,Dan haka tace wasu mutane kake nufi??,tafada tana kokarin zame jikinta daga nasa jin yanda yake matseta."Sake matseta yayi ajikinsa Yana maka mata harara yace Sofi'a,waya baki damar gayyatosu??"Saboda ina bukatar temakonsu, katafi kabarni batare dakasanar dani inda zakajeba,bayan kuma kasan ina bukatar Wanda zedebemin kewa acikin yanayin danake,wannan dalikene yasa nakirasu, tace dashi tana janye idanunta daga cikin nasa...Ba Wannan nakeson jiba"da wayar ubanwa kika kirasu??shine abinda nakeson ji"Banza tamasa dan talura rigama yake nema da ita!!Afusace yace ba tambayar kinakeba kin yimin banza.!Wayar Dr ta'fada tana kokarin mayar da hawayen dake kokarin zubo mata.Me ha'dinki dashi dazaki karbi wayarsa??,Bejira amsar taba yaciga da cewa,Wannan yazama karo nafarko dana karshe da zaka sake yin irin wannan shashanci,Wannan airashin kamun kaine dasanin darajar aure...ta inda yakeshiga batanan yake fitaba.Cikin kunan zuciya tajanye jikinta daga nasa tajuya,Yayinda wani takaici da bakin ciki ya mamaye mata zuciya tarasa me Ahmad yamayar da ita...Hannunta yariko yana narkar da 'kwayar idanunsa acikin nata,fisge hannun ta tayi tana janye idanunta daga cikin nasa datake hango tsantsar ajaraba acikinsa,dasauri tajuya masa baya"Cikin shammata yafisgota dasauri tarike towel din dake kokarin sincewa.Fincike towel din yayi dakarfi,durkushewa tayi awajen tafashe da kuka,Tsugunna wa yayi agabanta cikin rawan murya yace haba my Kainat meye abin kuka dan nafada miki gaskiya??Hannunsa tature ajikinta tace Nide banaso kabarni karkaseka ta'bani.Rarrashinta yashiga yi,ganin duk rarrashin dayake babarinsa zatayiba yasa shi mikewa,daukar ta yayi yawurgata kan gadon,Dasauri tamike tanaja baya tare da kankame jikinta"biyota yayi yadanne bakinsu yaha'de waje daya yashiga kissing dinta,kuka take tana dukansa daya kushinsa,ganin zata bata masa lokaci ne yasa shi nunamata karfin su badayaba,turmusheta yayi yashiga aikamata da sakonninsa masu wuyar mancewa,kankame jikinta tayi taki yarda tabiye masa"Seda bukatar sa yabiya kafin ya'dagata zuciyar sa wasai"Cikin 'kunsa takaici yace Jarababbiya kawai kinaso kina wani pretending kamar bakiso anyway natemaka nayi miki abinda kikeso.Banza tayi dashi tacigaba da kukan bakin ciki.toilet yashiga yayi wankan,kana yafito still yana inda abarta, harzuwa lokacin batabar kuka ba, ko Kallon ta beyiba yafice abinsa zuciyar sa Wasai"Seda taci kuka takoshi kafin tamike Ahankali tashiga toilet, wanka tayi tadaura alwala,tafito"Sif tabude tadauko sleeping dress Mara nauyi tasanya kana tayi Addu'a,takwanta zuciyar ta ba dadi dahaka bacci yadauke ta Batare data shiryaba.......

Kuyi hakuri da typing error bansamu damar ederting ba🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

*_ESHAA CE~_*🤙🏻

[3/23, 15:13] ESHA: *FREEDOM WRITER'S ASSOCIATION.* 📕🖊️

*KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_

*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD* _Realeshaa_

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*

*PAGE 31&32*🖌️

________________________📖Washe gari;bata farka da wuri ba se wuraren bakwai nasafe kasancewar gajiyar da Ahmad yatara mata adare jiya"toilet tashiga tayi wanka,da ruwan zafi sannan taji dama dama.Simple gownt tasanya Wanda yabayyanar da kiran ta fitowa tayi tanufi,sashen Nadiya koda tashiga bakowa a parlour,batayi yunkirin neman kowa acikinsuba tanufi dining area tazauna,ta'be baki tayi tayi bayan tabude warmers din taga peper soup din kan rago,sake bude dayan tayi taga funka sau da wainar kwai sekuma sinkin bread"Wainar kwai da Tea kawai tasha dan bata tunanin zata iya cin komai awajen bayan wannan."Bayan ta kammala breakfast din,tayi hamdala ga ubangiji kana tamike tanufi corridor daze fitar da ita zuwa garden dan mike 'kafafunta datake jin sunyi mata tsami.Ahankali take tafiya tamkar wacce 'kwai yafashewa aciki,har ta isa garden din lumshe dara daran idanunta tayi tana shakar dadda'dan Iskan dake fita daga shukokin"Tana 'daga kai tahango Ahmad yakishin gida,akan dadduma yayi zaman 'kasaita tamkar wani jinin sarauta.Ido takura masa tana Kallon tsantsar kyawu da Allah yamasa,hakika kyau ba afarin mutum yakeba baki ma yanada nasa na musamman"duk dakuwa kasancewar Ahmad baki ne,hakan behana ainihin kyawun sa bayya na ba,Sanye yake cikin wando 3quater me ruwan kakin sojoji da farin singlet Wanda ya bayyanar da faffa'dan kirjinsa nakiran jarumtaka,karamin bakinsa dake motsawa wajen cin inabi tasake tsurawa Ido tanajin kaunarsa naratsa bargo da tsokar dake jikinta.

Jikinsa ne yabasa ana kallon sa hakan yasa shi daga kansa"Sukainat yahango ta'kura masa idanu ko kyaftawa batayi tamkar yau tafara ganinsa"mikewa zaune yayi yanabinta da kallon sha'awa ganin yanda rigar ya bayyanar da suran jikinta"Hannayensa yabude mata alamar tataho garesa yana sakar mata da kayataccen Murmushin sa"Cikin takun kasaita tanufosa tana karairaya tamkar tarwada kana tana sakar masa da Murmushi me ratsa zuciyar duk Wanda akayiwa" tana karasowa ta'fada kirjinsa ta lumshe idanunta.Zazzafar ajiyar zuciya yasauke jin ta ajikinsa,kankameta yayi tamkar za akwace masa ita Iskar bakinsa yashiga hura mata acikin kunnnta cikin wata mayaudariyar murya yakira sunanta "Yarrrr tsikan jikinta yatashi sakamakon yanda yakira sunanta cikin wani salo,hannu yasanya yadago fuskarta yanabin Ilahirin fuskarta da kallon kauna,karamin bakinta yakura wa ido dayafi dauke masa hankali,kauda kaitayi tasake makalesa l"hannu yasanya yadago kanta ba bata lokaci ya hade bakinsu yashiga aikamata dawasu zafafan kisses masu wuyar mancewa,tamkar zecinye mata le'be yayinda hannunsa me yawo akowanne sassa najikinta.Da kyar tajanye bakinta daga nasa tanamaida numfashi,Jajayen idanunsa yadago yana kallonta tacikin kwayar idanunsa ke sake aika mata dawasu sakonni,Sunkuyar dakai tayi tare dasake kankame jikinta afaffadan kirjinsa.Hannu yasanya daniyan dagota yaji tafiya" dasaurj yadaga kai danganin wake zuwa Nadiya yaga tatunkaro wajen fuskarnan amurtuke tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa.
Cikin sauri ya Janye hannunsa dake jikin sukainat"Wayarsa dake gefe yadauka yashiga latsawa kamar meyin wani muhimmin abu"Jin yajanye hannunsa daga jikinta ne yasata dago fuskart gani tayi baki daya hankalinsa nakan wayar hannunsa,dan haka tamaida kanta takwanta domin atunaninta wani Abu me muhimmanci yake"Sannu karuwar Gida!! Muryan Nadiya ya karade mata dodon kunne"Har tabude baki daniyyan mayar mata da martani sekuma tafasa tasake maida kanta izuwa kafadar Ahmad tana lunshe idanu.Jarababbiya kawai wannan kokafaci da nacin kine yasa iyayenki suka aurar dake batare dakinkai lokacin ba, karamarki dake harkin San kimakal kale namiji, in badama kinsaba biye biyen mazan banzaba taya zaki Iya zuwa kina manne masa??.Hakika ranta bakaramin baci yayi da mugayen kalaman da Nadiya kejifanta dashi.Cikin kunsa takaici tace"Alhamdulillah iyayena sun kawoni gidan mijina amatsayin cikakkiyar mace,ba ragowar wani ba sannan Ina alfahari da kaina dan ban barwa iyayena abin kunya ba sannan maganan jaraba dakikeyi inace sadaki yabiya sannan al'ummah sukataru sukashaida daurin auren mu??, alhamdulillah gariban aure da jaraba anan ta'fada tana nuna cikinta," kinga kuwa inhaka jaraba tayi rana,nariga naga fahimtar bakiso kiga mun kadaita da ya Ahmad ne shiyasa kike wasu abubuwan anma kisani munraga da mungama zama daya nidashi tunda ga albarkar aure kwance akasan marata sede kiyi hakuri kije kirungumi sorry...
Chapter 18 · 0% Book details