← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 38

Sashe 6

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

________________________📖Ba abinda ketashi acikin motar banda shesh'she'kan kukanta"Ahankali yarage gudun motar tare da sanya hannunsa 'daya yari'ke nata,yana murzuwa alamar tayi shiru,Cikin lallashi yace kukan ya isa haka mana Amarya ta koso kike nima inyine?, yafa'da yana langwa'bar da kai"Banza tayi dashi tare da cigaba da kukanta batare data kallesaba" ganin bazatayi shiru bane yasanya shi maida hankalinsa kan tukin insunje gida yayi lallashin dazatayi shiru.Suna zuwa kofar katafaren Gidan sa ya danna hong dasauri gate man ya wangale masa gate din,ya cilla hancin motarsa ciki"yana parking yamaida hankalin sa kanta ganin harzuwa wannan lokacin batabar kukan ba,bece da ita komai ba yabude motar yafito sannan yazagayo gefen datake yabude,kifito yace da ita yana me gyara tsayuwarsa bamusu tasanya kafa tafito fuskarta alullu'be"Hannunta yakama suka nufi sashen Nadiya "Tun sanda sukashigo gidan take hangosu ta window dakinta wani malolon bakin cikine yatokare mata zuciya ganin yanda Ahmad dinta keta rawan kafa akan wata ba itaba" Jin alamar shigowarsu parlour yasa takoma bakin tangamemen bed dinta dasauri ta kwanta tare da lumshe idanunta kamar me bacci.Da sallama dauke abakinsa ya shiga parlour ganin bega Nadiya a parlour ba yasa shi zaunar da Sukainat adaya daga cikin manyan kujerun dake cikin parlour,kallon ta yayi da Har izuwa yanzu batabar kukanba yace kiyi shiru barina kira Nadiya yanagama fadin haka yashige Ciki yana gyara malun-malun dinsa"Da sallama dauke abakinsa yashiga yana washe fararen hakoransa,bakin gadon yakara sa tare dazama agefenta hannu yasa yashafa fuskarta Cike da zumudi yace my Queen harkinyi bacci ne bakijirani ba?,Banza tayi dashi tanajin zuciyarta na ingizata anma haka tadanne dan intabiyashe zata fallasa kanta"sake shafa fuskarta yayi akaro nabiyu yace dan Allah My Queen kitashi baccin yayi wuri haka.
'Bude idanunta tayi tana mutsikawa tamkar me baccin gaske sewani ta'be baki tayi,murmushi yayi yamikar da hannunta tare dacewa zomije 'kanwarki najiranki, bamusu tamike hannunta yarike suka fito parlour,kan daya daga cikin kujerun sukazauna kamar zata shiga Cikin sa" gyaran murya Ahmad yayi Cike da nutsuwa yabude taron da Addu'a, kana yamaida kallon sa kan Nadiya data wani makalesa tamkar zata koma cikin sa"Cikin Nutsuwa yace Nadiya takanki zanfara ga amanar Sukainat nabaki ina kuma fatan zakikar ba kikulamin da ita domin nayaba da nutsuwarki dakuma kalamarki"Murmushi tasaki mecike da ma'anoni masu yawa tace bakada matsala Honey wannan me saukine anma fa bazan karbi amana ba sede zankula maka da ita"Alhamdulillah daman nasan baza'asamu matsala daga 'bangarenki ba domin nafi kowa sanin wacece ke Allah yabada ikon kula wa da ita Uwar gida sarautar mata"Banza tayi dashi batace komai ba domin duk abinda takeyi daurewa kawai takeyi anma jitake tamkar tashakesa yamutu dan jin zuciyarta take kamar zefashe.
Kallon sa yamayar kan Sukainat dakanta ke kasa yace Sukainat kece karama inaso kibi Nadiya sauda kafa, nasan halin Nadiya macece megudun zuciya dasanin yakamata bazata taba yin wani abinda zebata miki raiba danhaka kema sekiki yaye duk wani Abu da ze bata mata rai ko kuma yakawo muku sabani,domin na fada miki tunfarko bawai tashin hankalin bane yasanyani kara aure sedan raya sunnar ma'aiki (S.A.W)
da hanka banason fitina sannan banason kawayen banza masu zugaki ko kuma sucanza miki hallaya ina fatan kin fahimta.
Gyada masa kai tayi batare datace komai ba"kallon Nadiya yayi yace My Queen kokinada magana??murmushi tayi tace bakomai aikagama magana,sede ka manta baka sanarmata dacewa kar tatakura maka yaya ba domin kasan wasu amaren basason yayan miji!!kai Ahmad yajinjina Cike da gamsuwa yace wannan hakane Amarya inafatan kinji abinda Nadiya tace ko? Duk danasan bakida wannan halin anma kikiyaye,Kai tasake gyadawa akaro nabiyu batare datace komai.ba dan haka Ahmad yarufe taron da Addu'a kana yamike tare da nufar inda Sukainat take yarike hannunta,yana me maida kallon sa kan Nadiya yace My Queen seda safe...Dasauri tamike tarike hannunsa tare da langwa'bar da kai tace kaje zankawo maka ita aibe kamatace ace bawanda yarakataba"Wani farin cikine yamamaye zuciyar Ahmad Cike da farin cikin yanda Nadiya kemartaba duk wani abinda yakeso danhaka yasake hannun Sukainat yace toh my Queen gdy nike da wannan karramawar.Murmushi tayi tarike
Hannun Sukainat sukafita shi kuma yazauna yanamejin farin ciki na mamaye kowani kungu da sako najikinsa.Bude kofar ma daidaicin parlour tayi Wanda yayi masifar kyau komai na parlour golden and blue ne direct bedroom din ta tanufa da ita agefen madede cin gadonta tazaunar da ita kana tasanya hannu tabude mayafin dake kan Sukainat ta tsareta da 'kananun idanunta, Ahankali Sukainat tadauke kanta daga fuskar Nadiya domin bazata juri kallon tsanan datake Binta dashi ba....Barka da shigowa gidana Sukainat hakika nayabawa jajurcewarki dakuma nacinki duk da kasancewar nayi miki kashedin karki yi gangancin shigowa Gida na domin mallakina ne nida 'ya'ya anma haka kikasanya kafa kika shure toh kisani bauta kikashigo yi cikin gidan domin nafada miki sekin gwammaci zaman prison da wannan gidan, domin babu abinda zaki tsinta banda bakin ciki da takaici dakuma kuncin rayuwa"tanagama fadin haka tajuya tafice,hartaje bakin kofa tajuyo tace
karki dauki maganata kamar barazana ko kuma cika baki domin muddin nace zanyi abu ba makawa senayi dan haka ina miki fatan alkhairi"tanagama fadin haka tafice daga sashen...
Da kallo Sukainat tabi kofar hartafi ce Wani irin kuka tafashe dashi me tsuma zuciya.Jin alamar shigowar mutum yasanyata saurin share hawayen ta tare da dago kai Ahmad tagani da Nadiya hannunsu sarkafe dajuna"Kafin Ahmad yace wani abin Nadiya tayi saurin katsesa tahanyar cewa Honey da alama wannan amaryar taka akwai Kewa atare da ita yakamata inbaku waje kasamu daman rarrashinta,Amarya inamiki fatan"Ficewa tayi tana sakin wani killer smile Wanda ita ka'dai tasan ma'anarsa.
Zama Ahmad yayi agefenta tare darike hannunta cikin sweet voice dinsa yace pls Sukainat kibar kukan haka,hannu yasanya yashare mata hawaye tare dacewa tashikije kiyi alwala kizo muyi sallah mungode wa ubangiji" ba musu taziro kafafunta masu 'dauke da zara zaran yatsu Wanda sukasha kunshi ja da baki,bayin tashiga tadaura alwala sannan shima yashiga yayi yafito.Sallah raka'a biyu yajasu sannan yadafe kanta yayi Addu'a" tambayoyi yamata game da addini Cikin ikon Allah tabashi amsar komai.gashash shiyar Kaza da freshmilk yadinga bata ka'dan taci tace ya isheta,ba yanda beyiba takara anma taki dan haka yakyaleta" yaci yakoshi sannan yariketa sukaje toilet sukayi brush,bayan sunfito yakashe wutar dakin yabar deam night.
Kusa da ita yamatso yace kirage wannan kayan yayi nauyi dayawa yafa'da yana janye mayafin kanta"ganin bata hana shiba yasan yashi fara shafata tareda wasanni da sassan jikinta yana romance dinta cike da zakuwa"tuni jikinta yafara amsar sakonnin sa masuwuyar fassarawa Cike da ficewar hayyaci takamo bakinsa tashga kissing dinsa cikin salon dabatasan ta iyaba sosai suka birkicewa junansu,ganin hankalin tabetare da ita yasa Ahmad rabata da kayan jikinta tare dacire nasa kana yafara kokarin Neman hanyarsa,jin haka yasa Sukainat tafara turesa tana rokon yakyaleta ina Ahmad bemasan tanayiba burinsa yajefa 'kwallo cikin raga"wani irin Ihu Sukainat tayi..Wanda yasani razana najefar da alkalamina🤭

Nayi waje dagudu🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️

_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_

*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_

*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD* _Realeshaa_

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*

*PAGE 11&12*🖌️
Chapter 6 · 0% Book details