← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 38

Sashe 16

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

****
Tun daga Wannan lokaci Sukainat tashiga rayuwar 'kunci da ba'kin ciki,duk wani aikin wahala da bauta acikin gidan itace,Nadiya tadena komai,saboda tsaban mugunta irin nata ga injin wanki anma bazata yi dashi ba sede ta tattarowa Sukainat nata dana 'ya'yan ta tayi musu haka zalika wanke wanke, moffing sharan compound din gidan,duk wani aiki me wahala itace zatayi Ahmad kuwa yagoyi bayan matarsa acewar sa aikin yakamaceta"shiyasa suke mata duk lulakancin dasuka ga dama ita da 'ya'yan ta batada ikon tankamusu tun da mai gidan yagoya musu baya.Tsakanin ta da Ahmad kuwa wani irinin zama suke mecike da ban tausayi,Sai ranan girkinta ne ze shiga dakin ta,tsakiyar dare asbah nayi zefita bakuma za tasake ganinsaba se wani ranan girkinta, wani lokacin ma batasanin shigowar sa sede taga alamar mutum ya kwana adakin...Yauma kamar ko yaushe se misalin 'karfe biyu nadare yashigo dakin nata gani yayi tanata murkususu,A'kasan 'dakin tana shesshe'kan kuka,cike da rashin damuwa ya kwanta batare daya kalletaba yayi kwanciyar sa,yakai kimanin minti talatin bacci yaki daukarsa sakamakon sheshshe'kan kukanta"mikewa yayi yana Jan tsaki cike da takaici yace Dan Allah malama ki yimin shiru kinbi kin dameni da kananun kuka idan kuma bazakiyiba nabar miki dakin,ai wannan wulakanci ne kinsani gaba da kukan munafurci jarababbiya kawai yafa'da yana binta da mugun kallo....Kasa cewa komai tayi se kukan dake kara kufce mata ga wani azabebben zazzabi dake damunta shin wai yaushe Ahmad yakoyi rashin tausayi ne?tatambayi kanta"Jin taki yin shiru yasa shi yamike afusace yayo kanta hannu yasa daniyyan janta waje,Dasauri yajanye hannunsa daga jikinta sakamakon wani zafi daya gauraye ilahirin jikinta.. Zama yayi agefenta yana binta dawani mugun kallo,saboda tsaban bakin hali da munafurci baki da lafiya shine bazaki sanarmin ba,Inkin kashe kanki iyayenki kikayiwa asara baniba danni bakya gabana jarababbiya kawai yace da ita"ko Kallon sa batayiba domin ita tasan abinda kedamunta,seda yagama jifanta da mugayen kalamai kafin yajanyo hijabi yasanya mata, sukanufi asibiti lokacin uku da Rabi yayi ko acikin motar se hantaran yake tare da ya'ba mata ba'ka'ken magana...Suna isa asibitin aka shiga bata temakon gaggawa, gwajin farko aka gano tana dauke da ciki na tsawon sati shida,Bayani Dr yashiga yimasa na yanda yakamata abata kulawa sannan kartayi aikin wahala kokuma ta'daga Abu me nauyi,saboda zejanyo matsala,sannan sakamakon binciken dasukayi sungano akwai yunwa da damuwa atare da ita dole adena yimata abinda zesata cikin damuwa domin tana bukatar kulawa na musamman.Magunguna Dr yarubuta masula Wanda zatayi amfani dasu"Godiya Ahmad yamasa sannan yawuce masallacin dake cikin asibitin kasancewar ana kiraye kirayen sallah.Bayan ya idar da sallah ne yashigo,dakin datake Zaune yasameta tajinga bayanta da bango idanunta alumshe kamar me bacci,jin kamshin tularensa yasata bude idanunta tana Kallon sa cike da So, kawar dakai gefe yayi yana Jan tsaki"jiki asanyaye tayi kasa dakanta talura ko Kallon besonyi"wata noise ce tashigo hannunta dauke da Leda me tambarin asibitin da alama maganine aciki tabaiwa Ahmad,Kallon Sukainat tayi tace madam congratulations natayi murna Allah yaraba lafiya"Ameen ta amsa tana nazarin maganan, fuskarta da yakwateccen farin ciki tace ya Ahmad, ciki ne dani??Wani mugun kallo ya watsa mata yace, adakile"yece eh",bata damu dayanayinsa na halin ko inkula daya nuna mataba sema wani farin ciki daya mamaye mata zuciya,hannunta tadaura akan cikin tashiga shafawa tanajin wani yanayi me wuyar fassarawa atare da ita Ita ce ke dauke da cikin Ahmad ajikinta?,gudan jinin Ahmad ne ke kwance acikin mahaifarta,?zata haifawa ya Ahmad dinta yara kyawawa kamarsa?,wasu hawayen farin cikine suka shiga zubo mata afuska,Dawani irin sauri tadira akan gadon tarungume sa tana hawayen farin ciki....Rai abace yasa Hannu yafinciketa daga jikinsa yanabinta dawani irin kallo Wanda shika 'dai yasan ma'anarsa...

_VOTE_ ✅
_COMMENTS_
_AND_
_SHARE_

*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_

*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD* _Realeshaa_

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*

*PAGE 27&28*🖌️

__________________________📖Cikin kakkausar murya yace mehaka kikeyi?,bakida hankaline in wani yashigo yaganmu ahaka fa?!Wani irin kallo kike zaton za ayi mana ya fa'da yana tsareta da dara daran idanunsa"Cike da mamakin kalamansa take Kallon sa!,cikin sanyin muryanta tace nifa matarkace ya Ahmad meye aciki dan anganmu ahaka??batajira amsarsaba taci gaba dacewa Ya Ahmad farin cikine yasani rungumarka,nasan duk duniya bayanni babu Wanda yakaika farin cikin samun Wannan cikin, shiyasa nake ganin yadace innu nama farin cikine abayyane ya Ahmad duk abinda zanyi bazan iya fadan farin cikin danake ba sede in misalta..Hannu ya'daga mata yana ta'be baki, cikin halin ko inkula yace"Sannu Uwar iya tsara magana niba Wannan tsarin nace ki yimin ba.Saboda munafurci 'dazun kin langwabe kan cewa ke bakida lafiya anma dubeki yanda kike wani rawan kai dakikaji cewa kinada Ciki natsani karya da munafurci arayuwata, dubi yanda kika tashi kika kankameni wai farin ciki ya fa'da yana maka mata harara.
Asanyaye tace kayi hakuri in ranka yabaci wlh banyi hakan daniyyan 'bata maka raiba maganan cewa lafiya ta kalau kuma kaima kasan bahaka bane, kawai de ina farin cikin zanhaifi yara kyawawa kamar kane,sannan kuma zanhaifi yaran dasuka fito daga tsatsonka, inaji ajikina duk yaran da zanhaifa maka,zansosu fiye da komai arayuwa ta saboda soyayyar dana ke yimakane zedawo kansu, ina matukar kaunar ka arayuwa ta fiye da yanda uwa ke kaunar danta ina kaunar ka fiye da yanda nake kaunar kaina inayimaka son da banayiwa kaina,ban tabbatar da soyayyar danake maka na gaskiya bane se yau danake dauke da gudan jininka amahaifata"Dan Allah ya Ahmad kasoni koda Rabin soyayyar danake yimaka,soyayyar ka acikin jinina Allah ya halicceni dashi bana tunanin zan iya rayuwa batare dakaiba ya Ahmad Allah ne shedena kan irin soyayyar danake gwada maka.( _Ina Bukatarka acikin rayuwata Kamar yanda mutum ke bukatar abinci domin yarayu,Ina bukatar ka kamar yanda kifi ke bukatar ruwa domin yarayu,Ina bukatarka kamar yanda tsuntsaye ke bukatar fikafukai domin suyi rayuwa Kamar haka nake bukatar acikin rayuwa ta domin nayi rayuwa me inganci da tsafta)_ Hakika kazamto wani bangare daga jikina Wanda bazan iya rayuwa idan babushiba takarashe hawayen tausayin kanta nazuba daga idanunta!.Sosai kalamanta sukayi tasiri agaresa jiyayi zuciyar sa yakarye shi kansa yasan son datake masa korabi baya mata, hannu yasanya yarungumeta yana bubbuga bayanta alamar rarrashi"Wani irin sanyi taji yaratsa zuciyar sakamakon rungumar daya mata hakan yasa tasaka hannayenta biyu tabaya tasake rungumesa tana cusa kanta afaffa'dan 'kirjinsa tare da sha'kan dadda'dan kamshin sa."Nafa'da butulu azzulumi matsiyaci mekake dashi??"kalaman dasuka shiga yimasa suwwa acikin dodon kunnensa kenan jiyayi zuciyar sa yagaza juran kalamanta,finciketa yayi daga jikinsa atake idanunsa suka rine izuwa 'bacin rai,zuba mata idanunsa yayi cikin kunan zuciya da takaici yace me zakiyi da butulu azzalumi,kuma matsiyaci aganina bekamata kiso irin wannan mutumin ba kamata yayi kisamu Wanda bashida wannan soffofin baniba!!.kuka tafashe dashi tace kayi hakuri ya Ahmad idan muna tuna abinda yafaru abaya baza muta'ba yafewa junanmu ba hasalima idan kace zaka tuna nimafa kafada min kalamai masu zafi akan iyayena"bece da ita komai ba se juyawa dayayi yafice..zama tayi tare da fashewa dakuka me bantausayi....
Chapter 16 · 0% Book details