← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 38

Sashe 3

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

________________________📖Zaune suke a dining area suna dinner,Cike da so da kaunar junansu suke hira,tamkar zasu koma cikin junansu saboda yanda suka mannewa juna."Ahankali Ahmad yamaida kallon sa gareta cikin sweet voice din sa yace my Queen haryanzu baki fada min mekikeso nayi miki Na fadan kishiyaba"murmushin ya'ke tayi tace Honey da kabarshi domin kaga hidin dimu sunyi maka yawa nayafe,'bata fuska yayi yace anma de kinsan hakkin kine ko?,kuma tunda inada halin yi yazama dole nayi miki dabani dashi shine zakice kinyafe dan haka kifadi duk abinda kikeso nayi miki"Shiru tayi kamar me tunanin wani abu,sekuma tace kabani 1million,murmushi yayi yace kintabbata ze isheki?"Kai tagya'da masa alamar eh"tana mejin zuciyarta na kuna tamkar zefashe wai ita Ahmad zeyiwa kishiya,ita Ahmad ze ha'da dawata azuciyarsa,ita Ahmad zerabawa kansa da wata hakika duk wacce tayi gangancin shigowa gidanta seta gwammaci zaman gidan yari akan gidanta setayi rayuwar kunci da bakin ciki acikin Gidan ta.'Karan shigowar massage wayar tane yakatse mata tunanin ta,Hannu tasanya tadauki wayar tare da bude massage din, Alart tagani na 2million daga Ahmad dinta,da murmushi afuskarta tamikewa tabasa peck akuncinsa,thank u so much Honey tace dashi, anma gaskiya kudin sunyi yawa kagafa akwai sauran hidindimu agabanka duk da nasan cewa bawai baka dashi bane anma yakamata inrage maka dawainiya"murmushin jin dadi yayi yanda take tayashi son duk wani abu dayakeso"cikin jin dadi yace kin cancanci fiye da haka my Queen girmankine, inayiwa Allah godiya daya azurtamin ke amatsayin mata burina kuhada kanku da Sukainat kuyi zaman lafiya.
Tamkar yacaka mata mashi akirji haka taji jin yakira sunan makiyiyarta,anma dayake 'yar duniya ce setace dashi haba Honey aibaka da matsala tamkar 'kanwa haka nadauketa inde tazo da zaman lafiya zamuyi ta inkuwa tazo da tashin hankali zatasameshi fiye da yanda tazomin dashi....kallon ta yayi cike da mamaki yace habade my Queen keda bakinki kike fadan haka??,Harta bude baki zatai magana wayarsa tadauki ruri,hakan yasa tayi shiru tana mebin screen din wayar da kallo"Second wife shine sunan dake yawo a screen din wayar"da murmushi a fuskar yadauka tare dacewa Amarya bakyalefi kokin kashe 'dan masu gida,murmushi me sauti Sukainat tayi tace kai ya Ahmad banda kisa de!!Cikin dariyar yace hakanaji masu Iya magana nafadi,uhm suma fada kawai suke tace dashi tana murmushi"hmm hakane kam,yace da ita.Ina yara na da momyn su amika min sakon gaisuwa ta"Duk suna lafiya suna jiran zuwanki domin sun shirya miki tarba ta musamman ya fada Cike da zumudi"Hannu Nadiya tasanya ta kar'be wayar daga hannunsa cikin kissa da Iya barikanci tace 'kanwata muna nan muna sauraran zuwanki nanda kwana ki ka'dan zaki samu tarba da karramawa ta musamman Wanda ba kowacce Amarya kesamun irinsa ba zakiga tattali tarairaya,'kanwata lissafomiki abubuwan dazaki fuskanta acikin Gidan nan 'bata lokaci ne anma duk sanda rugugin so yakaraso dake zakiga abubuwa kala-kala,'kanwata Mr's Ahmad to be fatan alkhairi"tunda tafara magana suky ta lumshe idanu tanajin kalaman Nadiya tamkar saukan aradu aka domin tafahimci da kuna acikin kalamanta,Cikin yanayin ta na sanyi tace Nagode da wannan karramawa taki,Allah ya shiga tsakanin mu da makiyanmu yakuma tsaremu daga sharrin abin ki,dariyan mugunta Nadiya tafashe dashi tace fatan alkhairi kanwata,tanagama fadin haka tamika wa Ahmad wayarsa,tamike tare dacewa Honey zanshiga ciki sekashigo"kar'ban wayar yayi da murmushi afuskarsa yace kinji bani ka'dai kemike tanadin zuwaba Har aunty ki da yaranki tanadi na musamman sukeyi miki a gaskiya kwana ki ukun nan sunyi mana yawa jimuke kamar mujanyosa yanzu, hakika Sukainat kinyi sa'ar abokiyar zama domin samun irinsu Nadiya nada matukar wahala,duk soyayyar datake yimin be rufe mata idanu ba, saboda haka ki kwantar da hankalinki kuzauna lafiya duk danasan cewa kema baki da matsala anma kikore jita jita kawaye da magulmata duk da kasancewar baki dasu kikiyaye kibi ta se kuzauna lfy"Wani irin tukukin bakin cikine yaziyarci zuciyar Sukainat jin yanda yake wani yaba matarsa,anma dayake bamai zafi bace ita din,setace insha Allah zakasameni me biyayya agareku.
Murmushin jin dadi yayi yace toh ya akayi yanzu,?akwai wani Abu dakike bukatane ko za'ayimuku?,Kai ta gya'da masa kamar yana gabanta,kana tace sofi'a tace zamu gabatar da kilisa dakuma bridalshowes,shine nace sena sanarmaka"murmushi yayi yace to keda bakida friends dawa zakuga batar kuma ai lokaci ma yakure yanzu"itama martanin murmushin tamayar masa tace wlh sofi'a ce tanace se anyi wai akwai friends dinmu na makaranta dazatayi inviting dinsu dan baza'ayi biki mukadai ba.
Toh shikenan zanturu Isah yakawo muku kudin daze isa" murmushi tayi tace to mungode,hira sukayi kana daga bisani sukayi sallama Cike da kaunar junansu"mikewa yayi yashiga ciki Inda yasamu Nadiya zaune tana waya,ganin shigowarsa yasanya ta kashe wayar,tare da maida hankalinta kansa cikin kashe murya tace Ango harka gama kenan,?kanwarta wa tabarka takarashe maganan cikin 'kunar zuciya da zafin kishi?murmushi yayi yashafa sajen fuskarsa,yace haka de kikace sauraniyar mata"harara tamaka masa aranta tace munafiki kawai kagama kalamanka da ita yanzu kazo kana fa'da min kalaman banza hadda wani sarauniyar mata,azahiri kuma se tace uhm ai nabarwa kanwata sarautar.
Dariya yayi Wanda ya bayyanar da fararen hakoransa yace"kingama yanzu kiratayi akan program dazasu gabatar,zama Nadiya tagyara tace wani irin program kuwa honey??,Yanda sukayi da Sukainat yafa'da mata kan program dazasu gabatar"Hannunsa tarike cikin nata tace haba Honey wani irin program zasu gabatar kuma??,a gaskiya Honey nibanga amfaninsa ba domin duk anan ne ake haduwa da kawayen banza Wanda zasu hure mata kunne sannan suyi kulle-kulle dan haka gaskiya nibanga amfanin wannan abin ba kawai tahakura dashi inde bawani abin sukeson kullawa da kawayenta ba anma fa shawara ce nabaka"Kai Ahmad yajinjina Cike da gamsuwa da kalaman ta domin damashi duk wannan bidi'oin basu dameshiba dan haka yadauki shawaran Nadiya 100℅ yace haka za'ayi kuma ngd da wannan shawara taki.murmushin jin dadi tayi tace yauwa Honey yakamata kakirata kasanar da ita karta tasaka rai,ta'fada tana mika masa wayarsa"karba yayi ya danna kiran second wife ringing daya Sukainat tadauka tare da sallama cikin sweet voice din ta,lumshe ido Ahmad yayi bayaga jiya dajin muryanta ako yaushe zazzakan muryanta, yakansa shi manta yanayin dayake ciki"Takaicine yakama Nadiya ganin yanda yawani shagala, da'alama yamanta tana wajen,Dafa kafadarsa tayi Cike da haushin abinda yayi,se asannan yadawo daga duniya tunanin daya Lula,akuma dede lokacin da Sukainat kecewa ya Ahmad kayi kobakaji nane!?.
Nutsuwarsa yadedeta yace kina jina,ki saurareni da kyau maganan program dakikace za'agabatar dasu Ku hakura dan banga amfaninsa ba banda yajanyo cece kuce kuma kinsan bana kaunar tashin hankali komai 'kan'kantarsa dan haka inaganin kihakura kawai zefi inyaso se ayi bu'dan kai ko??'yakarashe da alamar tambaya.
Hawayen daya zubo mata tasanya hannu tashare tace anma kuma 'dazun ka'amince zakabari muyi kuma nasanarwa sofi'a,harma anfara shirya komai,anma yanzu kace bazeyi ba,da kasan tunfarko baza kabari ba seka fada min ai kuma...Katseta yayi tahanyar cewa Sukainat nima da farko banyi wannan tunanin ba seda Nadiya tafahimtar dani matsalan dake ciki saboda haka bana bukatar kice zaku gabatar da kowani irin program dan haka kikiyaye.
A'dan fusace tace wani irin magana kake haka ya Ahmad?,taya zatace program dazamuyi zekawo tashin hankali menene abin tashin hankali aciki,da kasan tunfarko baza kabarmu ba da bakayi mana alkawari ba anma yanzu mekakeso nace dasu bakomai ngd da hakan,tanagama fadin haka takashe wayar Cike da bacin rai tanajin zuciyarta na kuna.Aunty Aliyah da shigowarta kenan tahango Sukainat tadukufa kai tana hawaye,dasauri takaraso wajen Cike da kulawa tace suky me aka miki?,wayasa ki kuka?,dagowa tayi tare da share hawayen ta kana tazayyane wa Aunty Aliyah,yanda sukayi da Ahmad tunfarko kana ga abinda yasake fada mata yanzu.
Kai Aunty aliyah tadafe Cike da takaicin hali irin Na Sukainat komai kankantar Abu seta zubar masa da hawaye,wannan saurin kuka nata nakona mata zuciya"Cikin takaici tace wai ke Suky meyesa bakida tunani ne??atunaninki wannan koke koken dakikeyi shine mafita,kizauna kinayiwa kishiya kuka bazakiyi abinda yadace ba!toh tin wuri gwanda kigyara rayuwar ki inbahaka ba kina tare da aiki,tana gama fadin haka tafice dan Sukainat bakaramin takaici take bata....
"Da kallo yabi wayar Cike da mamaki shi Sukainat takashe wa waya tabbas seya nunamata kuskurenta setayi danasanin kashe masa waya da tayi" dafa kafadarsa Nadiya tayi tace lafiya kuwa Honey?, Cike da bacin rai yace ni wannan yarinyar zata fadawa bakaken magana hadda kashe min waya yafada Cike da matsanancin 'bacin rai"Sassauta murya Nadiya tayi tace kayi hakuri Honey kasan akwai yarinya ta atare da ita,aharzu'ke yajuya yace wani irin yarintane atare da Sukainat inbanda rashin kunya"hmmm irin abin danake fada maka kenan duk irin wannan abin kawayen banza ke ziguta kan tayi maka rashin kunya,kuma nasan ba Iya kanka abin ze zatsayaba nima seta sanyani aciki
Bece komai ba se 'kwafa dayayi shi ka'dai yasan matakin daze dauka akanta mikewa yayi ya shiga toilet tare da banko kofar bayin....

******
Yau kimanin kwanaki biyu da samun sa'banin tsakanin Ahmad da Sukainat"tunda ga wancan rannan besaki kirantaba,koda takirasa bedagawa ganin haka yasanya tahakura dakiransa"anma acan kasar zuciyar ta wani irin tausayin kanta takeji ganin shariyar dayake mata,gashi tana bukatar jin muryarsa anma dole tahakura tare dadena kiransa.....
Chapter 3 · 0% Book details