← Book details Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 38

Sashe 1

Kishiya Ko Baiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/KqGEmawxDbT8UchuTqyC4g
*KISHIYA KO BAIWA???.*
(TRUE LIFE STORY)

*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD* _Realeshaa~_

*_Ya Allah Ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani._*

```Labari me cike da tsantsar soyyayya cin amana,ban tausayi,zalunci sarkakiya,se kunbiyoni acikin wannan labarin nawa zakuji yanda zata kasance inafatan zakubiyoni danjin wannan labari mecike da ilimantar nishadantarwa uwa uba fadakarwa.```

```Banyarda wani ko wata yasauya min labarina takowacce siga ba batare da izinina ba aikata hakan babban kuskurene. Wannan labarin yafaru agaske abinda akacanza kadan ne anma baki 'dayan labarin gaskiyace

HAPPY BIRTHDAY N-YARIMA INATAYAKA MURNAN ZAGAYOWAR RANAN HAIHUWARKA UBANGIJI ALLAH YAKARO SHEKARU MASU ALBARKA```.🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭🍭

_Bismillahir rahmanir rahim_

*PAGE 1&2*🖊️

___________________________________📖Ke karamar karuwa,yar talakawa,dangin matsiyata,Wanda basugaji abin alkhairi arayuwarsuba dangin jaraba 'yar anace yar masu jaraba da 'kwalafaci,wlh karki sake kiran wayar mijina inba hakaba wallahi,wallahi,wallahi, rantsuwa uku ki kasake kuskuren kiran wayar mijina sena cimiki mutunci shegiya matsiya ciya karuwa.
"Cikin sanyin muryan ta tace dan Allah aunty kiyi hakuri bansan yana gidaba da bazan kiraba bare har in bata miki rai,kuma miss call dinsa nagani shiyasa nakira anma Allah yahuci zuciyarki tunda kiran danayi ya bata miki rai takarashe cikin rawan murya irin na wanda ke gab da zubda hawaye.Wani dogon tsaki taja tace munafukar banza kawai annamimiya niba aunty ki bace kije can kinemi aunty banason kalen dangi da Neman gindin zama"tana gama fa'din haka takashe layin,tare da zama abakin tangamemen gadonta,Wanda yacinye rabin dakin,kafa 'daya tadaura akan daya tana girgiza wa tare da hura kofofin hancinta kamar Wanda iska kemata wari.
"Wani kyakykyawan matashine me yabude wata kofa yafito da'alama toilet ne,a'kalla shekarunsa zasukai arba'in anma baza kafahimci hakanba saboda hutu da naira dasuka zauna masa,yanada matsakaicin tsawo,da faffa'dan kirji na kiran jarumtaka,bakine,irin black beauty nan yanada madai-daitan idanu da kwantaccen sajen daya kawata kyawun fuskarsa,sekuma gemun daya ajje Wanda yasake fitar da ainihin kyawun fuskarsa tare da dimple daya lotsa agefen sajen dake kwance luf luf afuskarsa.Gabanta yakara so ya tsugunna da towel daure akugunsa Wanda bewuce gwiwarsaba,akan gwiwoyinsa ya tsugunna yana kare wa fuskarta kallo daya ke Iya hango damuwa bayyane aciki" Cikin daddda'dan muryarsa me tafiya da imanin kowace diya mace,yace what's wrong with you my Queen??kuka tafashe dashi tare da rungume sa tace,honey shin menayiwa wannan baiwar Allah datakeso ta musgunawa rayuwata?me natsare mata arayuwar duniya daya zamto batada buri se son ganin bayan farin ciki na dakuma jin dadina,aganina niyakamata inyi kishi da ita,bawai ita tayi daniba!? anma narasa mena tsare mata datake neman addaban rayuwata da munanan kalamai masu zafi azuciyar duk Wanda akayimasu"akan wakike magana??ya tambayeta da alama be fahimci inda maganarta ta tadosaba dan haka yayi gaggawar katseta"Sake marerece murya tayi tace wace kuwa inba matar dazaka auraba kullum cikin cimin mutunci da zagar min da iyayen take, atake ya'daure fuska yace wani abin yafaru??Cikin sheshe'kan kuka tace kawai dan takira wayar ka nadauka nace,da ita kana toilet shine tafara zagina tare da fadamun bakaken maganganu haddacewa wai ban isa in hanata shigowa cikin Gidan nanba inde malamai nanan kota wani hali se tashigo kuma ta fitar dani"afusace yasanya hannunsa gefen beside drawer yadauki hadadditar wayarsa kiran iPhone 11 yayi Dearing, number second wife,tsaki yayi tare da wurgi da wuyar jin switch off se huci yake yana taunar lips dinsa nakasa.Lallausan tafin hannunsa yasanya abayanta yana
bubbuga alamar rarrashi,cikin sweet voice dinsa yace am so sorry my Queen nakira wayarta switch off anma,zandau mataki dan ba zanyi tolerating din nonses din nanba bata isa tarenakiba in kyaleta"peck tabashi akuncinsa tace thanks Honey that's why nake alfahari dakai nasan bazakataba bari wata ta wulakantani ba"murmushi yayi tare da janyeta ajikinsa yace u deserve more.mikewa yayi yabude sif din kayansa, masha Allah kamar wani shagon seda kayan saboda yawansu kowani kalan kaya da bangarensa,wani farin gezna me kyan gaske yadauko tare da yasanya wa anyimasa dinkin zamani irin na matasan dakeji da naira dakuma sji,kayan bakaramin sake fitar da ainihin kyawunsa yayi na,turarukansa masu dadin kamshi yafeshe jikinsa dasu tare da taje lallausan sumar kansa Wanda kesheki da yalki,fitowa parlour yayi yana zabga kamshi tamkar wanda akayi barin tulare ajikinsa.
Dawani irin sauri,Nadiya tatashi tarungumesa,tana me sake manne kanta afaffadan kirjinsa tare da shakar kamahinsa,cikin kissa tace honey kakulamin da kanka jinake kamar inbika domin banason wasu sakarkari sukallamin kai nafiso dagani se kanwata zakuga wannan wankan"murmushi yayi yalakace mata hanci yana jin kaunarta nasake ratsa duk wani lungu dasako dake ajikinsa,saketa yayi yace my Queen karnayi letti sena dawo"yana gama fadin haka yajanyeta daga jikinsa tare da yafice wa,da kallo tabisa haryafice kana tana jin son sa nabin kowani lungu da sako najikinta"Direct inda yake parking Din motocinsa yanufa wata 'bakar mota me kyawun gaske ya shiga,Cikin motar na fidda wani sanyayyan 'kamshi me dadin gaske,key yayi wa motar tare da Hong dasauri gateman yawangale masa gate yacinna hancin motarsa yafice daga Cikin katafaren Gidan sa....

"Switch off din wayar tayi tare da ha'da kai da gwiwa tafashe da wani irin kuka mutsuma zuciya ba Kalmar datake furtawa face innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,wai shin wannan wace irin masiface?,wani irin rayuwane wannan?,shin me wannan baiwar Allah tamaida ta??shin talauci haukane?ta tambayi kanta cikin 'kunar zuciya, hakika datana da yadda zata gujewa wannan auren toh ba shakka data guje masa sede kash!!bakin alkalami yariga da ya bushe yau saura sati daya adaura aurenta da Ahmad Ajmi"Wanda tunda ga yanzu take Iya hango kalubalen dazata fuskanta agidan sa"Kuka tasake fashewa akaro na biyu me tsuma zuciyar duk wani mai tausayi cikin gunjin kuka tace ya Allah karka jarabcemu da abinda bazamu iyaba ya Allah kakawomin sauki acikin rayuwata Ya Allah idan wannan auren alkhairi ne Allah katabbatar idan kuma babu alkhairi ya Allah kasauya min damafi alkhairi ya Allah kawargazar inde babu alkhairi acinsa...

Jitayi andafa kafa'darta tana juyawa taga mahaifiyarta,rungume ta tayi tanajan zuciya,cikin sanyin muryan ta tace dan Allah Ummi afasa wannan auren!! wallahi bansan wace irin rayuwa zanfuskanta agidan Ahmad ba, matarsa batasona tatsaneni,Ummi bakiji irin zagin cin mutum data yimin ba hadda yimin gorin talauci shin mumu kabaiwa kanmu talauci ne takarashe tana jan zuciya.Rungume ta mahaifiyarta tayi cike da tausayinta tace insha Allah ba'abinda zefaru se alkhairi ki kwantar da hankali ki,kinji kidinga addu'a komai ze zo da sauki sannan inaso duk maganan data fada miki ki kyaleta da halayyarta,ganin baki shiga Gidan bane anma da zaran kin shiga zaku zama daya duk wannan abin zewuce" kai tagyada mata alamar "toh" batare datace komai ba,Wayar ta dake yashe agefe inda takashe Ummi tasanya hannu tadauka takunna,matashi" kamar jira'ake takunna kira yashigo.
Mika mata wayar Ummi tayi,ahankali tasanya hannu takar'ba tayi picking tare da sallama"batare daya amsa sallamarba yace kisameni awaje ,yana gama fadin haka yakashe wayar yana huci tamkar namijin zaki...

Dan Allah inkun karanta kuyi shearing dinsa👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻

1/1/2021

_VOTE_ ✅
_COMMENT_
_And_
_SHARE_

*_ESHAA CE~_*🤙🏻
[3/23, 15:13] ESHA: *KISHIYA KO BAIWA???*
_(TRUE LIFE STORY)_

*NA MARUBUCIYA*
*REAL ESHAA ~*

*WATTPAD* _Realeshaa_

*_Ya Allah ubangiji kajikan mahaifina ya Allah kagafar tamasa kurakurensa ya Allah kakai haske kabarinsa ya Allah kajikan dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa innamu yazo mucika da imani_*

*PAGE 3&4*🖌️
Chapter 1 · 0% Book details