Sashe 8
Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A fannin Yarimomin Mungaye kuwa duk sun can-canci hawa karagar mulkin sai dai jama'ar gari sunfi nuna ra'ayinsu akan Sadauki sama da Sardauna duk kuwa da matsalar da ke ga Sadaukin na auri saki domin a shekaran da ya gabata sukayi auren fari amma zuwa yanzu ya mata hu
u ya aura ya saki batare da sanin laifin da suke aikata masa ba domin ya k'i yin bayanin da yasa ke aikata sakin haka suma matayen idan an tambayesu amsar
aya ce suke bayarwa ita ce basuyi masa laifin komi ba ya sallamesu ba tare da ya ha
a shimfida da su ba.
Cikin matar na ya saka akwai ta farko 'yar kanwar Sarki mai suna Mubina wacce aka aura masa tana da k'arancin shekaru domin
kammala secondary dinta kenan a ka yi mata aure cikin rashin son ranta inda shi kuma Sardauna aka aura masa 'yar Waziri wanda shima ya ke kani ga sarki kuma har wayau k'anwa ce ga aminin Sadauki wato Abubakar ana yi masa alkunya da Imam, wacce ta kasance babba mai yalwar komi na cikar halittar mace sama da Mubina, wannan bambancin da ke tsakanin matan nasu yasa sadda Sadauki ya saki Mubina a washegarin kaita gidanshi yasa hankali bai wani tashi ba musamman da ita Mubinar ta yi ta murna har aka
ora laifin akanta ganin yarda ta yi ta boren bata son auren sai ake zargin ita ce ta nemi sakin da kanta.
Matarsa ta biyu 'yar Aminin Sarki ne wacce ta zamo mai wayewa domin ita tana da degree har biyu amma kwanarta uku a gidanshi ya saketa hankali ya tashi a wannan karon amma Sadauki ya nuna ko a jikinsa, akan haka Mai Martaba ya ce ya gama samo masa matar aure.
Bayan watanni Mamie Fulani ta matsa sai ya amince da auren 'yar aminiyarta inda ya amince bisa takurashi da tayi saidai shima auren kwanarshi daya ya bata sallama inda kafin ta isa cikin Masarautar da labarin ya tsere gidanshi da ya gina a b'oye da ke dajin Tekun Kabobo wurin da ba wanda ya sani sai amininsa Imam da turawan da sukayi aikin.
Bayan wasu watanni ya dawo ya sha fa
a tamkar Sarki zai dukeshi ya yi ta basu hak'uri, anan suka rutsashi sai ya sanar masu da matsalarshi Amma yak'i magana akan dole suka rabu da shi, daga nan bai sake aure ba sai wata
aya da ya wuce inda Na'ibin Sarki ya bashi sadakar d'iyarshi mai wadataccen ilimin addini sai dai yana jin labarin ya hankalinsa ya tashi inda Mami Fulani ta rufe shi da fa
a tare da gargadi akan kada ta sami labarin ya saki yarinyar inko ya kuskura ya aikata mai rabata da shi sai Allah wannan
kalma ya hura wutar jin rabuwa da Sakina wacce a ranar da aka kawo mashi ita ya bata saki wanda faruwar haka ya saka Masarauta shirya taron zama na musamman akanshi a karan farko tun soma wasa da auren da keyi gami da son zubar da Martaban Masarautar su domin lamarin na ta
a ran manyan masarautar musanman Baba Chiroma da yafi kowa zafi haka ansha mamaki da har zuwa lokacin bai nemi ganawa da Sadauki ba shi yasa yanajin sakon kiran da yafito daga bakin sa sai ya gudu mab'oyarshi tare da gargadin Imam akan kada ya sake ya tona inda ya ke.
Sai da ya sami wata
aya da kwana biyar wato sati biyar kenan sannan ya dawo inda ya ke kan fuskantar fushi daga mahaifanshi ya yin da dan uwanshi Sardauna ke yi masa shagub'e na kiranshi da kalman mai auri saki mara godiyar Allah
, duk da kalaman nayi masa ciwo amma ko kallo bai isheshi ba balle ya tsaya bashi amsa wanda ke kallo a matsayin bata lokaci sannan duk da hakan kauanrshi ga Jama'ar gari bai rage komi ba wannan lamari ya rage masa damuwar da ke ciki na fushi da mahaifanka keyi da shi.
Duk da b'oye halin da ke ciki da ya keyi amma kallo
aya zakayi masa ka gano yana cikin matsanancin damuwa wanda Amininsa Imam ke aikin bashi baki.
Aliyu Sadauki.
Tsaye ya ke a bakin window dake bedroom dinsa inda ke kallon kai da kawon hadimai bisa alamu manyan ba
i ne zasu halarci Masarautan.
Bushe-bushen da aka soma ne ya sashi barin wurin ya koma saman sofa ya kwanta idanunsa na kallon sama zuwa can ya tashi zaune ya furzar da iska mai huci tare da kaiwa k'irjinsa duka ya rintse ido da hanzari jin yarda zafi ya ziyarci wurin da ya duka.
Ya juya kai cikin furta "Why ta zamemin masifa a rayuwa?
Shin aina zan sake ganta?
Shin ita din mutum ce ko aljana?
Me yasa na aikata mata haka?
Shin har sai yaushe zan fita daga wannan rayuwar na fitinuwa da son kasancewa mace amma ko ta zo gareni sai naji banda mak'iya irinta?"
Kwalla ne ya taru a kwarmin idanunsa ya kai hannu ya goge tare da tsirawa ruwan hawayen ido da ya shafo.
"Narantse duk ranar da na sake ganinta sai na wulak'antata fiye da yarda take kan wulak'antani yarda zatayi jinya tare da shiga damuwa sama da wanda ta jefani ciki."
"Wacece ita Aliyu?"
Kallon Imam ya yi wanda bisa alamu ya jima tsaye bai sani ba.
Ganin da Imam ya yi ba zai sami amsar tambaya ba sai ya tako ya zauna gefenshi ya kamo hannunsa cikin sanyin murya ya soma magana "Please Sarkin gobe ka daure kayimin bayani yarda zan fahimta wanda zai fitar da su Mamie Fulani daga zargin sihiri akayi maka wanda ba dare ba rana suke mik'a kukansu ga mai warware k'ulli batare da gajiyawa ba akan abinda ke jikinta ya fita ka yi aure ko saga jininka kafin su koma ga mahalicci su."
Shiru bai tanka ba saima kwanciya da ya yi yana jin mararsa na kartawa tamkar yarda ya saba ji duk in ya shiga tunanin sanin wacce ke alak'anta silar rashin zamanshi da matarsa na aure.
"Yar gidan waye?
Me ta ke tak'ama da shi?
Shin zan iya samun wadannan tambayoyin daga bakin Aliyu Abdul Hakam?"
"No."
"Why?"
"Imam ban santa ba haka ban san me zance maka akanta ba."
"Ikon Allah, wato ta tabbata Aljana dai kenan?"
"Ina tunanin hakan."
"To aina ka gamu da ita?"
"A Barci."
Ya samu kanshi da ambatar hakan alhalin ya san ba hakan ba ne.
Shiru Imam ya yi na kallonshi ya yin da shi kuma ya kauda kai gefe,murmushi ce ta kufcewa Imam har da zarcewa da guntun dariya lamarin da ya fusata Sadauki ya mik'e ya nuna masa kofar fita sai kawai ya kulle bakinsa da tafin hannunshi ya cigaba da dariya har da fitar kwalla.
"Na haukace ko Imam?"
"No Brother kawai dariya k'aryar da ka yanko ne ya bani domin k'arara ka tona kanka ba gaskiya ka ambatamin ba."
"Me kake nufi da kalamanka?"
"Nothing, but sit and tell me the truth, dan wallahi ba zanyi kaffara ba, ba gaskiyan kenan ba."
"Nagode da maidani mak'aryaci da kayi kuma ka fice alamarina, bana son sake ganinka kusa da ni, yes na amince na rayu cikin ka
aici kamar yarda Mamie ta furtamin, Abba ya bawa sokon danshi mulkin Mungaye, Umma ta cigaba da kirana mara amfani."
"Innalillahi!
Sadauki yaushe Umma ta ambata maka wannan mugun kalman?"
"I said get out!
Malam."
Ya ambata tare da jan hannun Imam ya mik'ar ya soma ja har zuwa bakin falonshi sannan ya sakeshi ya koma saman Cushing ya zauna ya rik'e kanshi gam wanda ke jin tamkar zai fice daga muhallinsu.
"Affuwan A...
Hannun da ya daga masa yasa Imam gintse ban hak'urin da ke nufin bashi.
Tsawon mintoci uku ba wanda ya yi magana sannan Sadauki ya mik'e ya doshi hanyar bedroom saida ya tura kofar sannan ya yi magana cike da izza ya ce "Ka shirya idan anyi sallah zaka rakani sake bawa su Abba hak'uri a turakarshi dan yau Mamie ke da girki kamar yarda Lailah ta sanarmin."
"Ok Allah ya kaimu."
"Amin."
Ya amsa can
asar mak'oshi wanda ko Imam bai jiyoshi ba.
Durk'ushe suke gaban Mai Martaba Abdul Hakam da Mamie Fulani.
Imam ne ke ta ban hak'uri ya yin da Sadauki yake ciccira hawaye nayi masa zarya na bak'in cikin jin kalaman da Mamie Fulani ta ambata sadda ta ganshi gabanta.
'Ban son sake ganin fuskanka Babana domin k'unci nake shiga a duk sadda ka ziyarceni dan haka kada ka sake zuwa inda nake na rok'eka.'
Toshe kunnuwansa ya yi tuno kalaman, ya d'ago kanshi hawaye wani na bin wani duk da zamowarshi mara saurin kuka amma kalaman Mami ya sakashi kasa jurewa.
Ya sarrafa cikin sarsarfa ya isa bagan Mamie Fulani ya sauke kanshi a saman k'afafunta yana furta "Ki yafemin Mamiena wallahi ina cikin iftila'in rayuwa ne domin fushinki guba ne gareni dan ba zan tab'a sake yin tasiri ba har abada."
Sai ya fashe da kuka mai sauti wanda rabon da ya yi irinsa ba zai tuna ba.
Ganin haka sai Imam
ya tashi ya fice da sauri yana goge hawayen tausayin Amininsa.
Momyn Haske ce
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabibin Tsiri
By Mrsjmoon.
ADABI WRITER'S ASSOCIATION (AWA)
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.
Page 5.