← Book details Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 27

Sashe 15

Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sun gana cin abinci Momy ta kira Maryam suka shiga bedroom d'inta ta dubeta ta ce "Me ke tsakanin Muneera d Sadauki?"
"Wallahi ban sani ba."
"Ban son wasa Maryam sanar da ni abinda na ke zargi."
"Momy a gaskiya Neera na son yaya Sadauki tun kafin ya soma auri saki karatun da takeyi yasa bata nuna masa alamu ba har zuwa yanzu tana son shi duk da hatsarin da ke cikin aurensa baisa ta sadduda ba sai dai in banda ni ba wanda ya sani hatta kuwa Lailah da Zuhrah ba wanda ya gano k'aunarta gareshi jama'a na
auka
arfin zumuntar da ke tsakanin su ne ya janyo suke shiri da juna dan kema sheda ce kaf 'yan matan Masarauta ba wanda yaya Sadauki ke sakewa fuska har ta gaya masa maganar da taga dama sai Neerah."
Numfashi Momy ta ja tare da cewa "Zanso Sadauki ya furta yana sonta."
"Saboda ne Momy?"
"Saboda duk wanda ya aura ya saki ha
a su akayi wata k'ila nuna ra'ayinsa akan auren wacce ya ke so zai kawo
arshen auri sakin."
"Momy yaya Sadauki na da matsala a fara neman masa magani kafin a sake yi mashi aure."
"Kema kinyi magana anan domin muna tattauna maganar neman masa magani da Mamie Fulani "
"Yawwa hakan dai yafi."
Sai abu na gaba shi ne maganar fitar da miji, shin wa kika tsayar cikin namemanki?."
"Miji fa Momy?"
"Eh Dadynku ya umurceni da in tambayeki saboda ya daina yarda da auren had'i sannan Mai martaba ya soke auren had'i amma in kun ha
a kanku ba ruwansu zasu sanya albarka."
"Momy wani abu na faruwa ne wanda bamu sani ba har akan ya faru?"
"Ko
aya kawai Mai martaba ne da kansa kwanaki ya tarasu ya sanar da su soke auren had'i amma ina jin bai rasa nasaba da abin kunyar da Sadauki keyi na sakin matar da ake bashi."
"Momy bana da gwani saboda ina tsoron abin da ya sami yaya Khadijah ya sameni domin har yau tana begen Mahmud bayarda zatayi ne dole ta karb'i yaya Sardauna duk kuwa da yana kan cutar da ita."
"Ban tambayeki wannan labarin ba sannan tunda baki da gwani sai Dadynku ya zab'a miki ko cikin dogarai ne."
"Momy dogarai kuma?"
"Eh tunda na zama abokiyar wasanki ba."
"Sorry Mum zamuyi shawara da su Neera."
"Ke dai kika sani kuma ina baki shawara da kiyi nazari banda biyewa shawarar zuciya wanda ke haifar da dana sani."
Ganin ta fa
a tunani Momy ta fice daga d'akin cikin yi mata addu'ar samun k'warin zuciya akan duk abinda ta sanya a gaba.

Maryam ta kwanta a saman gado, matsanancin damuwa kwance a fuskanta.

"Yaya Sadauki."
Ta furta a saman lips d'inta tana mai lumshe ido tare da nazarin kalaman Momy na
arshe.

Zuwa can ta zabura tamkar wacce a sokawa Allura ta fito, ganin ba kowa a falon sai ta dauki hijabin sallah ta fice da sauri, Hadiman da ke kai kawo a tsakanin sassan Masarautar suka soma jero mata gaisuwa amma ba wanda ta sami zarafin amsawa.

Momyn Haske ce
*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad.

Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon
afa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848.

Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.

Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye.

Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya
ara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon
Adabi Writer's Association (AWA)
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks
*Ayimin Affuwa kwana biyu ina cikin hidima ce shi yasa ku ka jini shiru.*
Page 10.

Part d'in Mamie Fulani ta nufa ta shiga k'aton falon da sallama, Lailah ce ta amsa cikin dishewar murya wacce ke zaune gaban Sadauki bisa alamu laifi tayi masa.

Da sauri Maryam tayi nufin juyawa ya daka mata tsawa.

"Ke!"
Tsak ta tsaya batare da ta juyo ba.

"Zo nan dama ina shirin kiranki."
'Nashiga uku Allah yasa dai ba masifa Lailah ta janyomin ba.'
Ta ambata a ranta ya yin da a fili ta juyo jikinta na rawa tare da furta "Ni?"
Shiru shi ne amsar da ta samu sai tasami kanta da
are masa kallo sanye yake cikin kayan sarauta wanda yafi ta'amali da su domin kafin ka gansa da
ananan kaya aiki ne sai ko suit wanda da an gansa cikin shigar ke nuni da zaiyi tafiya ne sai kuma a filin motsa jiki inda ke shigar sport wear.

"Please Maryam ki zo kiyi masa bayani wallahi ba ruwana da Muhib, shi ne ke takurani ke biyoni gida."
"Keep quiet!"
Ya ambata a fusace.

"Sorry Yaya, dan Allah ka taimakeni ka saurari bayanin bakin Maryam domin ita, Neera, da Zuhra ne shaiduna akan bayanin da nake yi maka, wallahi Allah ba ruwana da Muhib."
Kallo kin rainani ya auna mata sai ta fashe da kuka ta kama k'afarshi
janye
afar ya yi tare da mik'ewa ya nufo k'ofar fita saboda kukanta ya karya masa zuciya kuma a take ya yarda da gaskiya take sanar da shi.

Maryam na ganin tasowarshi ta runtuma da gudu tamkar zata kifa sai lamarin ya bashi dariya ya murmusa tare da juyowa ya ce da Lailah "Ki fita sabgar mara natsuwar yaron nan idan kuma kina son mu sa k'afar wondo
aya da ke ne to in sake ganin
afarsa a cikin Masarautar nan sannan in har kin san kin kamu da son shi to kiyi gaggawan cireshi a ruhinki domin kinfi
arfinsa ta ko wani fuskan kuma ke mai tsarki ce dan haka ba zan bari ki auri mai cike da dattin najasa ba, a bisa umurnina ki koreshi koro na har abada."
Ya kai
arshen maganar na runtse ido domin yanajin tamkar bayyiwa masoyan adalci ba.

Gyada kai ta yi tana share hawayen da ke zubo mata, ganin na kallonta sai ta motsa baki a hankali ta ce "Nayi maka alk'awarin dakatar da shi daga zuwa Masarauta tare da nesantarshi na har abada duk da dama shi ke haukansa ni bai isheni kallo ba."
"Da kyau."
Murmushi tayi ya maida mata da martani ya juya, har ya fice ya dawo ya ce "Saura ki ha
a baki da wancan mara kunyar ku turomin macizai saman gadona kamar yarda kuka saba aikatawa idan anyi maku fa
"Allah yaya ba ruwana Neerah ce da aikin kasan bana yin Ofi sai da babban dalili."
"Nadai sanar dake kada inga maciji a muhallina."
Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi domin tsayawa zancen nan na nufin ya huce kenan.

"Humm zan gyara maku zama ne musanman ita da ta rainani."
Ya ambata yana barin wuri
"Ka soma gyara kanka Babana domin kai da su duk kanwar ja ce wani fanninma kafisu tsorata mutane da Macizai wai lamarin har kan Mai Martaba dan ya sanar da kai gaskiya."
Da sauri ya dawo falon ya rik'o hannun Mamie yana k'ifta mata ido, alamun tayi shiru.

"Yes, ka soma gyarawa kanka zama kafin ta zo kan wasu wanda basuyi kwatan-kwacin laifin da kake kan aikatawa ba."
"Wayyo Mamiena me na yi kuma?"
"Babban zunubi na auri saki da kuma tsoratar da Musulmi ta hanyar fito da macizai su razanasu akan laifin da baikai ya kawo ba, kwanaki Mai Martaba har kusan fad'uwa
asa ya yi dan tsoro, tabbaas da ba dan ina kusa ba da anji mugun labari sakamakon macizai da suka cika turakanshi marasa kyan gani sannan tamkar almara suka b'ace, ganin anyi binkice ba agano komi ba sai na tabbatar kaine ta turosu, anya Babana hakan ya kamace kuwa?"
"Mamie ya wuce fa."
Ya furta cikin tsare gira ganin Lailah na k'unshe dariya.

"Bai wuce ba, mai jin magana kawai kada a fad'i
ayan."
"Please Mamie ki manta da lamarin, ai natuba da jimawa."
"Anya Babana kai ka
ai ne kuwa?"
"Me nayi kuma Mamiena?"
"Watsi da cikar kamala wato aure sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam.

"Ayya Mamie ki bar maganar auri sakin nan domin yana daga cikin zanen
addarar shi wanda bawa bai isa kufce masa ba saboda rubutacce ne daga Allah."
Duk kallon bakin falon sukayi a tare, Dr.

Muneerah ce tsaye idanu jajur bisa alamu kuka tayi.

"A'a Likita bokon turai, lamarin Babana ko da
addara to son zuciya ya soma yi masa jagora domin ba sau
aya ko biyu ya aikata laifin ba har fa sau hu...

"Mamiena ya tuba ai ba zai sake komawa ga zunubin ba ko yaya Yarima?"
Kafeta da idanu ya yi batare da ya amsa ba.

"Yes Neerah yaya ya yi tuba na gaskiya da yardan Allah ba zai sake komawa ga wannan laifin ba, zaiyi aure ya zauna lafiya da iyalinsa wannan a rubuce yake."
Lailah ta amshe da sauri tana kallon idanun Sadauki.
Chapter 15 · 0% Book details