← Book details Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 27

Sashe 18

Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinta a sake ta sanya sannan ta iso gefensa ta tsaya ya kalleta idanu jajur lumshe nata ta yi sannan ta juya ta soma tafiya ya riko hannuta ya matse ta kallo
ara ya kalleta cikin kaushin murya ya ce "Wannan shi ne karo na farko da zan sake ganin kina bayyana tsiraicinki tunda baki da tunani sokuwa kawai."
Ya cillar da hannun ya nufi inda alkyabbarsa ya ke ya saka ya nufi bakin k'orama ya fa
a ciki tunjim!!.

Duk suka zabura saboda sautin ya razanasu.

"Nima abinda zan sanar da ke kenan dan Allah kada ki sake aikata hakan Neera, ko ba komi ki tuna matsayinki na 'yar Masarauta kuma mai tarin sani ga addini."
"Baza ta sake ba Yaya Imam."
Lailah ta ambata a hankali.

Motsa kai ya yi ya nufi bakin k'oraman cike da tarin tambayoyi game da abinda Sadauki yayi wanda bai ta
a aikata kwatan-kwacinsa ga d'iya mace ba wato rungumarta cikin nuna tsan-tsan kishi.

"Muje ko?"
Girgiza kai ta yi.

"To me zaki tsaya yi tunda giyan k'aunar ya kaiki aikata abinda baki ta
a yi ba."
"Me na yi Lailah"
Neerah ta furta cikin rawar murya mai nuni da tana daf da fashewa da kuka.

"Ni taho muje kada ki sake bada kanki har ki shafamin."
"Ya gane ina son shi wai?"
Tafi Laila ta sanya gami da fashewa da dariya lamarin da ya dawo da Neerah hayyacinta ta dafe goshinta cike da takaicin fallasar karatun ruhinta.

"Nagano karatun ruhinki Sister sai dai abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa haka fagen da 'yan hamayya sai kin nemi makaman ya k'i domin Zuhra da Maryam na cikin filin dagan."
"Maryam?

Wacce Maryam?"
"Maryam tamu k'anwar yaya Imam d'iyar Momy da Abba Sarkin Fada."
Wani dum taji, jiri ya ziyarceta tayi baya zata fad'i, daidai Hud ya iso wurin sai ya tareta da sauri yana ambatar sunan Allah, lumshe ido tayi tana nanata sunar Maryam aminiyarta itama na son Sadauki domin sam jin Zuhrah na ciki bai d'aga mata hankali ba.

Ruwar da taji an fesa mata a fuskan yasa ta bu
e ido tana sakin ajiyar zuciya, tundaga saman sumar kansa ta soma kallonsa har ta dire a fuskanshi wanda ke d'igan ruwa.

"Yaya Yarima."
Ta furta a saman lips d'inta tana sake lumshe idanu.

Harara ya zabga mata tare da fizganta daga hannun Hud ya nuna mata hanyar waje "Maza ku b'ace min dagani tun ban karya ku ba kuma daga yau na haramta muku sake shigowa lambun nan sai da izinina, idan kuma kun isa in sake ganin sillayen
afafunku cikinsa."
Da sauri Lailah ta ja hannun Neerah suka fice, wacce jikinta yayi mugun sanyi.

"Malam ba da haka ake nuna k'auna ba ka natsu mu buga game d'in duk da ba ni kad'ai ke cikin 'yan wasan ba, Ni, kai, Sardauna wata k'ila har da d'an korenka Imam na ciki ko da yake na san kai baza ka haye ba saboda warin kashin kajin dake manne da kai na auri sa...

"Ya isheka Hud bama son rashin tunani, dan haka ka kiyaye kalaman da zai sake fitowa a harshenka."
"In ank'i fa?"
Kafin Imam ya bashi amsa Sadauki ya janyo hannunsa na girgiza masa kai alamun kada ya sake magana, tsaki ja tare da nuna Hud da yatsa alamun gargad'i sannan ya biyo Sadauki na bambamin fa
ar bai son hanashi gogewa masu kawo masa raini hadda da keyi.

"Aikin banza da wofi wallahi sai na zama sarkin Mungaye ko da hakan zai zamo fansa ne ga ruhina."
"A she muna da yawa masu fansar da ruhunan namu akan hawa karagar mulkin Masarauta Mungaye."
A razane Hud ya kalli inda maganar ya fito ya yi raba da Salis d'an Babban Dogari kuma d'a ga Jakadiyan sirri.

"Ai wai cin dank'o har da su Kaza?"
"Eh sai dai na wuce Kaza sai Jimina."
"To mu zuba shege ka fasa."
"Tam zaka sha mamaki kuwa."
Saboda takaici Hud bai sake magana ba ya bar wurin, Salis ya rakashi da harara daga bisani ya
auki Basketball d'in ya soka bugawa shi ka
ai cike da nishad'i.

Nagaji Imam!

Nagaji na ce!

Wallahi zanyi hijira, zan tafi inda ba wanda zai sake jifana da kalman auri saki sannan auren ma na fasa yinsa, ka zamo shidata insha Allah ni da aure har aba...

"Kul!

Baban Mamie, kada ka sake ka shiga hurimin Ubangiji, auri saki na cikin zanen
addarar ka dan haka kada ka yanke k'auna daga samun rahamar Ubangiji, ka sama ranka zakayi aure kuma zaka rayu da matarka batare da saki ya shiga cakaninku ba."
"Banjin hakan zai tabbata gareni ba Imam."
"Na ce ka saka a ranka zakayi aure ka yi rayuwa tamkar yarda kowa keyi."
"Ta yaya hakan zai faru, alhalin wancan shed'aniyar na bibiyan bad'ini da zahiri na, shi yasa zan koma inda babu mutane na k'arasa rayuwata hankali kwance."
"Aliyu ka dawo hankalinka, wai me ke damunka ne?"
"Damuwa mai tsanani."
"Nasar da ni Please."
"Not now Imam domin baka da abin magancemin shi."
Yana ambata ya mik'e ya shige dakin barcinsa ya murza key.

Cike da tarin damuwa Imam ya fice domin tunda yaga Saudauki ya kulle kansa ya tabbatar ba zai ta
a saurarensa yanzu ba dan haka cikin Masarauta ya nufa, direct turakar Mai Martaba ya nufa yana addu'ar samun nasara a k'udirinsa wanda ke hasko samun yayewar damuwa ne ga
Amininsa.

'Tuni na jima da sanin kana tare da aljannu, In banda aljana ta aureka taya zaka ri
a zancen ganinta a zahiri d bad'ini, kai wallahi da sake ba wanda ya isa ta
amin amini ya kwana lafiya ko da kuwa Aljan ne.'
Shigowar sak'o a wayarshi yasa ya katse masa zantukan zuccin da keyi ganin daga Sadauki ne sai ya waigo ya kalli volcany ya hangoshi tsaye hannaye rungume a k'irji sai ya maida kallonsa ga sak'on.

"Ban amince ka sanar da Abba komi ba domin baza su fahimta ba, ka tafi wurin iyalinka zaifi maka."
Kallon inda Sadauki ya ke ya sakeyi har lokacin na nan tsaye sai ya girgiza masa kai tare hawa barandar sashin Mai Martaba, wayarshi ya soma ringing sai ya maidata silent ganin Sadauki ne ke kiranshi, yana zama gaban Mai Martaba ko gaisar da shi baiyi ba sallamam Sadauki ya doki kunninsa waigowa ya yi a razane domin bai isa ya iso da hanzari haka ba duk kuwa saurinsa.

'Anya aljannu ba su maidamin da Amini jinsin su ba?'
"Imamundeen ya dai kake kallon k'ofa?"
Murza idanunsa ya yi babu Sadauki tamkar yarda ya gansa cikin 'yan sakonni da suka wuce.

"Uhm kana lafiya kuwa?"
Ya katse masa tunani.

Maido kallonsa kan Mai Martaba ya yi kafin ya furta kalma ya jiyo Muryan Sadauki na gaisar da Mai Martaba.

"Au ka ce tare kuke shi ne ina magana kana kallon k'ofa tamkar warkewar makanta."
"Abba anyi lafiya?"
Ya sami kansa da furtawa.

"Alhamdulillah Imam."
Ya amsa tare da mik'ewa ya nufi d'akin barcinsa ganin su Imam nata mazurai ya ce idan sun shirya magana da shi su sameshi a ciki dan bai shirya kallon shirmensu na fama ba.

"Kai Sadauki ban son iskanci wato Ofin naka har kanka amininka zai sauka?"
Imam ya ambata cikin fushi.

"Tashi muje ko ranka ya b'aci."
"Ban zuwa sai na bada labarinka da Aljannu."
"Zakuwa ka zama bebe nan bada jimawa ba, tunda baka ji magana."
"Aliyu me kake aikatawa a b'oye? tsafi ko me?"
"Amsa wannan mara jin magana kawai."
Aikam kafin ya ankara wani dum ya shiga kanshi ya tafi luw zai fad'i Sadauki ya tare shi zuwa jikinsa tamkar walk'iya suka suka b'ace daga falon.

Tun Mai Martaba na dakon shigowarsu har ya gaji ya tashi ya shiga toilet ya d'auro alwalla ya zauna gabatar da azkar d'in marece cikin rashin damuwa da lamuran shiri-ritansu domin sunar da ya bawa lamarin kenan.

TSIBIRI.

Tsidau ya sauka a wani tsauni mai yalwan bishiyoyi wanda suka taimaka wurin
ara duhun da tsauni ke da shi, amfani ya yi da haskensu na junnu ya cike tsaunin da haske sannan ya samu hango Tsibirin da ke nema wato fadar Ifritu Baushe wanda ya zamo Bil'adam amma yafi Aljani shed'anci ta ko wani fuska shi yasa ake yi masa lak'abi da sunan mugayen Aljannu wato Ifritu.

Tsibirin sai fitar da bak'in hayak'i keyi hakan ya
ara munana dutsen da ya zamo fadar Baushe,
asan dutsen kuwa wuta ne ke ci cikin fitar koren harshe, da ganin wurin zuwarsa sai an shirya baga Bil'adam ko Ajani ba.

"Lallai ka ci sunarka Baushe domin ko a itatuwan daji, itacen Baushe ba mai saukin k'onawa ba ne kamar yarda na ke hango shiga fadarka ba mai sauk'i ba ne."
Tsidau ya ambata yana nazarto yarda zai shiga fadar domin ganawan sirri da Ifritu Baushe akan uwar gijiyarshi Lina.

Bai samo mafita ba ya jiyo ruguji a bayanshi bai waiwayo ba ya bu
e zafin hannunshi domin sanin me ke faruwa, wani dutse ne ke fitar da wuta ya nufoshi irin dai wanda ya so halakashi a fadar Kaka Gunu kwanakin baya.

A gigice ya juyo tare da neman hanyan tsira sai dai ya makaro domin dutsen ya cimmasa ya bangajeshi a take ya cillashi
asan tsaunin inda ke kai inda farin hayak'i ke fitowa mai kama da tafiyar giragizai a sararin samaniya.

Kafin ya sauka
asa yaji anyo sama da shi wani iska mai
arfi ya nashe idanunsa.

Bayan wuce mintinan da basu wuce biyu zuwa uku ba ya ji an saukeshi ya zabura sai ya yi ido biyu da Ifritu Baushe, ya bushe da dariya mai fitar amo tamkar cidan hadari ya jima yanayi kafin ya dakata ya soma yiwa kan sa kirata...

"Sai ni Baushe mugun itace, Baushe mai hayak'in masifu, Baushe bai san na gida ba tunda ya zamo ajalin ubanshi mahaifi, Baushe k'i sabo dan ko hadimansa bai d'awa
afa ba, ko ank'i ko amso sai nayi mulkin sarkin sakakunar Aljanu da Mutane."
Ya dakata yana kallo Tsidau da ya koma tamkar d'an tsako a gaban giwa.

Momyn Haske ce
Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad.
Chapter 18 · 0% Book details