← Book details Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 27

Sashe 6

Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan wasu shekaru burrin Lina ya cika domin ta samo ilimin da take burin mallaka wato tsafin da ya doke na Lima wanda yanzu take shirya fito na fito da wanda ya nemi kawo mata cikas a cikin manufarta na zamowa magajiyar karagar kujerar HATSABIBIN TSIBIBI domin shimfid'a mulkin adalci gami da samar masu da abin bauta su daina zama kara zube, su sami ilmomi mabambanta haka tana burin ganin wayewar su ya zarta na biranen da take shiga tana ganin cigaba da suke tare da shi mai burgewa haka babban burinta shi ne su sakko daga kan Tsibirin (Tsauni) su gyara dajin ya zamo birni mai zaman kan shi tare da kayan more rayuwa in yaso saman tsibirin ayi masa gyara ya zamo wurin shakatawa na musamman da jama'a daga birane daban-daban zasu ri
a zuwa yawon bu
e ido ku
in shiga na halal na samuwa ga Tsibirin daga nan
arshen zalincinsu ya zo su kowa rayuwar 'yanci mai cike da farin ciki tare da zumuncin ga kowa, ba
i su zamo abar karramawa a tsibirin.

Tarihin Hatsabiban Tsibiri da Sarki Goma ya gina ya zamo ya tarwatse sai wanda ta ingana da kanta, sunarta ya zagaye Duniya da tambarin Adalci.

Saidai a gefen Lima duk kishiyar burin Lina shi ne nata wanda a kullum da shi take kwana da tashi.
*Wannan shi ne asalin labarin Tsibirin da rayuwar jama'ar cikinsa gami da burikan tagwayen Gimbiyoyin.*
Cigaban labari.

Lima a Bukkan Kaka Gunu.

Ta tura kai cikin Bukkan bayan ta yi amfani da alkaliman sihiri k'ofar bukkan ya bu
e, cikinsa katon wuri ne da ya cika da k'okunar kan namun daji kala daban-daban a can daga nesa wani kilisa ne mai daukan ido samansa da kujerar na alfarma ce, wurin Lima ta nufa ta hau saman kujeran ta
zauna tana fesar da iska cikin nuna izzar jinin sarauta.

"Barka da isowa uwar gijiyata, me ke tafe da ke?"
Kallon tsamurmurin tsohon ta yi cike da mamakin bayyanarshi ba neman iso daga gareta.

"Affuwan uwar gijiyata na kasance zaune a wannan bigire shekaru masu yawa domin tun sarki na biyu nake a matsayin hadimisa sannan nine sirrin dukkanin sarakunan da suka shude dan haka kema nine idonki akan komi umurninki kawai nake jira yanzu kiga aiki da cikawa."
"Me ye sunarka?"
"Tsidau uban yan binciken wannan fada."
"Madallah, yanzu na zo ne domin sanin abin da 'yar uwata Lina ke boyemin game da tafiyarta da duk abin da ya faru gareta tun kafin tafiyar har zuwa yanzu."
"Kwanta ki huta uwar gijiyata kina tashi na yi alkawarin bayyana miki duk abin da ya shige miki duhu akan Gimbiya Lina."
"Tsidau bana jin barci domin bashi na zo yi ba."
"Dole kiyi shi uwar gijiyana."
"Kada ka kawomin wargi na hukunta ka y kai Tsohon wofi."
"Tuba nake Sarauniyar Gobe, fushinki kukan yaro."
Tana shirin sake magana ya hura mata iskan bakinsa a take ta zame daga kujerar kanta langabe alamun barci ya
auke ta, da yatsarshi ya nunata sai gata kwance saman kilisar ta yi matashin kai da wani filo mai zanen fatar jakin daji.

"Shin ta ina zan soma boye miki sirrin
abin da kika zo bincike?"
"Bar wurin don ka gama aikinka kafin ta farka na nade sirrin da aka barmata gado."
Muryan Lina ya ratso.

"Na barki lafiya Gimbiya mai jiran gado."
"Ko da yake kafin nan zauna da ita ya kai amintaccen hadimin Sadauki Gau
u bari in koma na sallami wancan lalataccen kada maikon kogin
da ya yi jagorar samar da shi ya halaka shi."
"A dawo lafiya ya ke adalar Sarauniyar Duniya."
Murmushi ta yi tare da b'acewa shi kuma ya gyara zama gaban Lima ya tsirawa hawa da saukan numfashita ido tamkar mai irgawa.

Rugigi ya ji a bayanshi kafin ya tantance dalilin afkuwan lamarin Bukkan ya
auki rawa wani gaton dutse ya d'ago daga
asa inda ke zaune ya nufo inda ya ke yana fesar da koren wuta, tamkar walkiya Tsidau ya b'ace a daidai lokacin Lima ta farka a firgice sai dutsen ya koma mazauninshi tamkar bashi ba.

Abun ne ya shigo a rikice ta tashi da hanzari ta isa gabanshi ya rik'o hannayenta ya soma magana.

"Ya ke farin cikina wannan binciken yafi karfinki dan haka ki lamuncemin amsar gadonki domin na samu damar taimakonki."
"Abun zan iya, kabarni da kayana."
"Bazaki iya ba tunda ga shinan an sakaki barci bisa hila wanda saninki da ilimin tsafi bai amfana miki komi ba a wannan gab'an."
"Abun waye Tsidau?"
"Hadimin ne ga 'yar uwanki Lina."
Ware ido ta yi cikin cewa "Lallai Lina ta shiryawa taran aradu."
"Biyoni kawai domin sanin ta inda zaki bullowa lamarin."
Biyo bayanshi ta yi cike da zantukan zuccin wanda ta sanyawa ranta sai ta nemo sanadin afkuwansu dan hatta Abun ta soma wasi-wasin a kansa.

Lina ce tsaye a saman ruwan Tekun Kabobo fuska a ha
e ta watsa wani haske da ya fito daga babban yatsar hannunta na dama,a take maikon da ya b'ata ruwan ya soma tafiya har ya b'ace amma launinsa na yellow bai sanja ba.

Ta sake tsuke fuska tana fitar da huci zuwa can ta yi gunji ta soma tafiya a saman ruwan a hanzarce har ta isa tsakiyarshi kujerarta ga gold ya baiyana a saman dutsen da ke tsakiyar Tekun inda wasu halittun ruwan sukayi dandazo domin gudun hijira daga halaka, ta zauna tare da tsirawa ruwan Tekun ido da ya ke
sake komawa yallow mai duhu, zuwa can dokin Buda ya taso sama ruwa ya yi tartsi tare da fitar haniniyarshi mai firgitarwa inda halittu suka sake rudewa da neman mafaka sai kuma ya koma ciki tsundum!

Tamkar an janyoshi, kimanin mintoci biya ya sake tasowa sama wannan karan Buda na kwance saman bayarshi tamkar Gawa, tafiya yasomayi a saman ruwan cikin jan
afa saidai kafin ya kai bakin gab'a wani igiya daga kasan ruwan ya fito kamar walk'iya ya maidashi ciki sai ruwan ya sake rukid'ewa zuwa bak'in-k'irin tare fitar k'ugi tamkar rugugin hadarin damina.

Lina da ke kallon komi ta mik'e tsaye da sauri tare da kulle ido ta nuna ruwan a ta ke dokin da Buda suka taso sama ta tura hannunta gaba suka tafi a guje tamkar tsintsaye suka zube a saman yashi da ke gefen Tekun.

Ta sauke numfashi ta re
bud'e hannayenta ta nuna ruwan ya dawo launin shi fari k'al yana murdewa yarda ya keyi a tun farko, ai kafin kwabo Halittun nan sun soma rige-rigen komawa muhallinsu, ido ta zuba musu tana sakin murmushi ta sunkuya tamkar zata fad'a cikin ruwan sai kuma ta tashi tsaye tana mai shafan gefen fuskanta cikin cewa "Na sami cikar burina na taimakon dabbobin ruwa tare da sokon can Buda, mulkin Adalci ya soma sauka daga hannuna, godiya gareka Sadauki Gaud'u da kayimin komi na ganin na mallaki ilimin tsafin da ya zarce na ko wani matsafi dake nahiyar nan harma da waje ta, hak'ik'a zanyi aiki da Adalci tamkar yarda hakan shi ne cikar burinsa, ganinan tafe zuwa mik'o gaisuwa ga ruhinka abar girmamawata, tabbas idan na zama Sarauniyar Tsibiri kogon da kabarinka ya ke nan ne wurin bautarmu."
Tana kulle baki ta rikid'a zuwa k'aramar tsuntsuwa mai shegen gudu ta lula sararin samaniya ta
ace tamkar kibiya sai dai tana sauka a cikin kogon dutsen da kabarin Sadauki Gau
u yake idonta ya sauka kan Hadimi Tsidau kansa sunkuye cikin tsantsar ladabi ya soma magana.

"Uwar gijiyana ayimin gafara lamarin ne ya sha gabana domin na kusa halaka kuma a faruwa hakan na gano ma'adanar tulun sirrin da kike burin mallaka sai dai zamowa mallakinki da kamar wuya saboda manyan iffiritai ne ke gadinsa kuma mahaifinku shima na burin mallakan tulun ya tura 'yar uwanki ne domin ta binciko Tulun sai ya tabbatar ta nemo sai ya taho ya amshe cikin hikima saboda ya san iffiritan da ke gadin Tulun ruwan albarkan baza su yi mata komi ba sabanin da in shi ne zai iya rasa ranshi dan ya ta
a jaraba mallakansa ya sha da k'yar."
Numfashi Lina ta sauke tare da bu
e idanunta da suke kulle tun soma maganar Hadimi Tsidau ta kalleshi na sakonni ta jinjina kai batare da ta furta kalmar ba ta matsa gaban Kabarin Sadauki Gau
u ta russuna gabansa ta mi
a hannunnta na dama ta
ora saman Kabarin kanta sunkuye, ganin haka sai shima Hadimi Tsidau ya taho da sarsarfa ya russuna a bayan Lina tare da sauke kansa
asa, ta sami mintoci goma sha biyar a haka sannan ta mike tsaye shi kuma Hadimi Tsidau na nan sunkuye cikin girmamawa.

Murmushi ta yi kana ta soma magana cikin tsantsar isa da mulki inda kallaman ke fita
aya bayan
aya.
Chapter 6 · 0% Book details