← Book details Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 27

Sashe 16

Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Au, in na fahimta kuna bayan iya shegen da yarik'a aikatawa kenan?"
"A'a fa Mamie amma dai tunda ya wuce to abar d'aga zancen gudun
acin rai kinsan abu ka
an ke sanyashi cikin tunani ya soma wasan b'uya da kowa kuma hakan kan jefashi cikin ka
aici sannan hakan bai kamata ba yana Sarkin Gobe na fuskantan matsin rayuwa."
"Muneera wai nawa Babana ya biyaki ne?"
"Na me fa Mamie?"
"Na campaign mana."
Ware ido ta yi Sadauki ya murmusa tare da russunawa gaban Mamie ya yi mata rad'a wanda ita ka
ai tajiyo abinda ya ambata aikam ta sauke masa dundu tana furta "Allah ya tsare, ya kare, can ga su gada wai Zomo yaji kid'an farauta, wallahi a kul
in ka da wannan lamarin kadaiji na sanar maka in ba so kake mu koma gidan jiya ba."
"Allah Mamie na zama kurna akan lamarin sam banji me kike cewa ba."
"Amsa naka Sadauki, Allah kada naji ko na gani kuma nan da sati biyu ka kawo mana matar aure ko ranka yafi dare duhu da fatan katuna maganar Mai Martaba."
"Mamiena dan Allah ki ami...

"Nagama magana Babana sannan kada na sake ganin ka tasa k'anninka a gaba da zancen baka son suna zance tunda ba jik'asu zamuyi mu sha ba."
"Mamie da dare zan dawo muyi maganar a gaban Abba domin a wannan gab'an banjin zan ja da baya ba."
"Na zama abokiyar wasarka ko Baba Ali?"
"Tuba na ke Fulanin Mai mar...

"Gidanku na ce Sadauki."
Girgiza kai yayi tare da sumbatar hannunta da ke ri
e da shi tun dazun kana ya saki ya iso daf da Neerah ya rage murya ya ce "Iyayi kawai to ban gode ba."
"Gobe ma rana ce da Muneerah kake zancen
an Samari."
"Mamie 'yarki ta rainani fa."
Ya ambata cikin kawo mata duka ta gofce.

Banza Mamie ta yi masa sai ya fice yana cije lips gami da nuno Neerah da yatsa cikin salon wasa ya yin da ita kuma keyi masa gwalo.

Murmusawa Mamie Fulani tayi domin abinda ke saurin sakata farin ciki shi ne ganin walwala a fuskan Sadauki Aliyu.

"Ke kuma taho naji damuwarki da kika tahomin da idanu kamar jan nama."
"Ciwo sukemin Mamiena."
"Kika sake ambatarmin k'aryan nan sai na sa
a miki."
"Affuwan Mamie kaina ke ciwo kuma kin san ban da juriyan ciwo ko ka
an, shi ne nayi kuka Ammi ta koroni wai na dameta da jan hanci kada in saka masu mura ita da yaranta."
"Ayya sannu, kyale Nana ai ciwo na kan kowa, taho kisha magani domin na san halinki na gaba da magani wai kina Likita amma kina gudun magani, Allah ya kyauta kam."
Cikin murmushi ta iso ta zauna gefen Mamie tare da manno jikinta da
afarta, sai ta dafa kanta cike da kulawa take yi mata sannu kana daga bisani ta bawa Lailah umurnin
auko mata maganin ciwon kai a d'akin barcinta, cikin dibara Neerah ta gudu kafin Lailah ta dawo ta nunawa Mami a biyota da shi dakin Lailah saboda abinda Neerah ta tsani shansa shi ne magani.

Hajiya Umma ta ya kika yi wannan waftar na fed'ewa Sardauna biri har wutsiya shin kin manta waye shi akan gaba da bin bokaye?

To wallahi tun wuri ki dawo hayyacinki ki sanja dabara domin ina da tabbacin bazamu ta
a samun ha
in kansa ba tunda kinayi waftar sanar da shi gaskiyan lamarin da muke kai."
"Ki bari kawai Hajiya Kilishi wai a zatona in yaji Aljana na tare da Sadauki zaifi yin farin ciki tare da bamu ha
in kai har mu kai ga nasara."
"Kin manta har kwanar gobe suna fita rangadi tare domin ginuwar
aunarsu kuma
aunar da mai Martaba ya dasa a zukatansu bai ta
a gogewa sai dai zan sanar da ke hanyar gaskiya domin kawo nak'asu a
aunarsu shi ne sai mun tashi tsaye mun sa an raunatashi yarda zasu zamo basa ga maciji ko ka
an shi ne zamuyi nasarar
ora shi akan turban da muke so haka game da son kud'insa sai anyi mana aiki ta yarda kome kika nema ya baki batare da kai ruwa rana ba tunda yana da dukiya kuma ba mai amfana da shi sai makirar matarshi da uwarta ke kuwa sai hange daga nesa to sam hakan ba mai yiwuwa ba ne, yarda kika sha wahalar haihuwar sa gami da rainon sa dole ya zamo ke ce ta farko da zaki mori dukiyarsa tare da sanin duk kan bayanen
addarorinsa."
"Tabbas kinyi gaskiya Hajiya Kilishi, zantukanki masu amincewa ne gareni, yanzu zan baki wuk'a da nama ki zamo idanuna na kai da kawo tsakanin lamarin saboda yawan fitana a b'oye nada hatsari dan idan Mai
Martaba ya sani kashina ya bushe wata k'ilama aurena ya sami tangarda tunda angama da shi bai kallona da daraja sai muguwar Fulanin can wacce ba zata gama lafiya ba."
"Kibari kawai, gata bata jin Asiri."
"Kin manta waye Uwarta kenan?

Ai Hajiya Dada cikakkiyar matsafiya ce domin maganar Malam Sale kenan duk in ya buga
asa Uwarta na tsaye kanta shi yasa sai yarda tayi da Mai Martaba."
"Aikam na yarda Hajiya Dada na tsafi domin dubi zafin Chiroma amma a gaban Nana Safiyya sai ya koma fulawa saboda laushi."
"Uhm ai
arshen su ba zaiyi kyau ba in sha Allah."
Allah ya amsa."
"Amin Aminiyata."
Murmushi Hajiya Kilishi tayi sannan ta maida hiran kan abinda suka zauna a kai, inda cike da kisisina take cewa "Dama ina shirin yi miki wannan maganar fitar da kanki sai nayi nazarin a wakilta Hud yana amsowa tare da sanya Sardauna amfani shi wanda ba sai ya zo hannunki ba kinsan Hud da iya kalaman makirci na tabbata cikin sauk'i zai sakashi yin amfani da maganin hankali kwance, kinga ko wanda zaici a abinci ne duk Hud zai bashi saboda in muna son ya sami farin jinin jama'a sama da wanda Sadauki ke da shi dole sai mun hada na ci a abinci da sha da wanka har da hayak'i."
"To ba matsala hakan za'a yi, zan turo maki sak'o anjima amma kada a amso na hayak'in nan saboda zai harbo jirjinmu."
"To madallah, bari in koma kada mai gidan ya neme ni."
"Yau ke ce da turakar kenan."
"Eh fa."
"Ok tafi nima ina da ba
i anjima ka
an."
"To na wuce, Allah bamu yinin lafiya."
Motsa kai Ummu tayi cikin lumshe ido dan kanta taji na ciwo, harara Hajiya Kilishi ta zabga mata
ta gefen ido tana zund'enta a fakaice sannan ta bu
e k'ofar ta fice cike sak'e-sak'en yarda tsarinta zai tafi batare da samun tangarda ba na ganin d'anta Hud ya haye karagar mulkin Mungaye tunda shima Babansa
an Sarki ne yana da sarautar da zai iya Mulki ba sai lallai 'ya'yan Sarkin dake kan karagar mulki ba
"Wallahi bana son Sadauki domin tuni na kamla rabashi da Masarautar baki
aya lokaci nake dakon ya yi a nemeshi a rasa daga ganan Hud ya zamo Sarki mai iko domin bazan bari Sardauna ya zame masa matsala ba a tafiyar ba."
"A'a Mamma ina mutuwar son Yaya Sadauki kuma shi nake burin gabatarwa Abba a matsayin zab'ina kamar yarda kuke dakon jin gwanina sannan ina tare da ke kan zamowar yaya Hud Sarki saboda lokaci ya yi da za a kawo sauyi ba lallai sai 'ya'yan Sarkin dake mulki ne zasuyi ta gadon sarautan ba, duk da a gefe
aya ina jin kamar ba zai iya ba dan ban ta
a jin mashayi ya hau karagar mulkin Mungaye ba."
A razane Hajiya kilishi ta dubi inda mafi soyuwar 'yar nata
aya tilo mace cikin 'ya'yanta maza hu
u.

Gyara tsayuwa ta yi tare da jinjinawa mahaifiyar nata kai alamun bata tabbacin furucinta tare da cigaba da cewa "Yes Mamma ina yin Yaya Sadauki kuma shi ne mijina da yardan Allah dan na k'udiri aniyar d'aura d'amarar jure zama da shi a duk yarda ya ke, ni ce zan kawo
arshen auri sakinsa insha Allah"
'Wata sabuwa inji 'yan ca-ca, hak'ik'a aiki ya sameni ni jikan Magaji.'
"Momma muje nasan baki rasa shawarar da zaki bani akan auren sannan kada ki kushemin zab'i a kan abinda ya ke zanen
addararshi ne wato auri saki."
Dafe kai Hajiya Kilishi ta yi tana jin wani mak'ak'in d'aci na sauka saman harshenta.

'Tirk'a haka zakiyimin Zuhra?

To wallahi ko zaki mutu ne ba ki isa hanani kora Sadauki duniyar da bazai kuma waiwayen Masarauta ba.'
Ta sake ambata cikin ranta tana dallawa bayan Zuhra harara wacce take shirin shiga d'akin barcinta.

"Hey Doctor Neerah, me ke faru ne har ya sakaki kuka?"
Motsa yatsunta Neerah ta yi tamkar zata furta kalma sai kuma ta tsuke bakinta tare da hayewa saman gado ta juyawa Lailah baya.

"Dan Allah Muneera sanar dani damuwarki ko in had'a ki da Mamie nasan ita zaki sanar da ita."
"A'a Lailah kada kiyimin haka, yanzu taso muje ki rakani gidan Hajiya Dada."
"Asibitin da kikace zaki shiga fa?"
"Na fasa."
"No ki muje na rakaki domin ba kyau sa
a al
awari."
"Na tura masu Dr.

Hassana harma ta isa kinga sak'on da ta turomin yanzu."
"Ok amma gaskiya kada ki sake irin haka tunda kin san ke suka fi bu
ata."
"In sha Allah."
Suka fito bayan Neerah ta gyara fuskanta ya yi kyau suka sami Mamie zaune hadimai kewaye da ita suna yi mata hira cike da sakewa zamowarta mara girman kai irin na mafi akasarin matar sarakuna.

Bayan sun amsa gaisuwar hadimai sai suka sanar da ita inda suka nufa ta tsare gira kafin tayi maga Neera ta rigata da cewa "Please Mamina gidanmu na biyu zan kai ziyara fa Allah daga nan ba inda zamu wuce kinsan halinmu.."
"Muneera bana son yawo ne alhalin kuna 'yan manyan gida musanman yanzu da ake maganar aurenmu"
"Mamie dubo fa sanyin idaniyarki zamuyi ba yawo ba sannan baza mu wuce awa biyu ba zamu dawo in sha Allah."
"Ok to shiga kitchen ki wuce mata sak'onta dama Junaid yanzu zai kai mata kun hutash-sheshi kam."
"A'a Mamie suyi tafiyarsu inyi tawa da Maryam dama na ce ta shirya zamuje gidan tsohuwar Mamie ziyara.
Chapter 16 · 0% Book details