← Book details Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 27

Sashe 7

Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tsidau zanyi aikin da kaina domin ina tare da Zobben sihiri na Sadauki Gau
u duk da saka Zoben tamkar na yafa mayafin mutuwana ce ga rayuwata amma akan cikan burina zanyi wannan kasadan saboda da in mutu a hannun Lima gara na
are rayuwa a matsayin baiwa a masarautar Sarki Gamji ko ba komi shi
in mahaifi ne ga shugabana Sadauki Gaud'u."
"A'a Uwar gajiyana banayi miki fatar shiga hannun azzalimin Sarkin nan wanda har '
an cikinsa bai bari ba saidai kafin ina baki labarin hatsarinsa zanso sanin sirrin da Zoben ke tare da shi da na kasa ganowa tun sadda mai gidana Gaud'u ke sanye da shi."
"Tsidau bana bu
atar jin komi daga masarautar Sarki Gamji domin Sadauki ya sanarmin da komai sannan Zoben da zan fito da shi yana
asan Tekun Kabobo sirrinshi mai fa
i ne domin duk wanda ke tare da shi a cikin yatsarshi yafi
arfin duk wani matsafi haka duk abin da ya tunk'ara sai ya samu nasara komin
wuyar lamarin, in barka haka."
"Tafdijan amma Shugabana yana da wannan Zoben ya yi sake mugun nufin mahaifinsa ya yi nasara akanshi?"
"Ya sanarmin ya wuce shekaru bakwai da cire ainihin Zoben a yatsarshi jabun ke sanye da shi tare da boyewa mahara Zoben gano jabun ne ke yatsarsni cikinsu har da mahaifinsa domin burinsa ya mallakamin."
"Shugaba ya sanki da jimawa kenan?"
Jim ta yi domin bata son ambatar
addarar da ya ta
a afka mata wanda ya kasa b'acewa a ranta haka ta kasa maida hankali akan gano dalilin faruwar lamarin kamar yarda tak'i amincewa ruhinta a hukunta mai laifin duk da tarin damar da take da shi na aikata masa komeye da ta so amma ganin Tsidau na dakon amsarta sai ta amsa a takaictda " Eh."
"Affuwan Uwar gijiyana, ban gamsu da amsar nan ba a matsayinsa na sirrintaccen Hadiminki bai kamata ki ri
a bani bayani a dunkele ba dukda ina aljani zan iya gano kome kika boye saidai alkawari nayiwa Shugabana cewa bazan ta
a binciko sirrinki ba kamar yarda ban ta
a gigin binciko nashi ba bisa alkawarin da na daukan masa wanda wannan lamarin yasa aka kawo masa hari batare da na nasan meke faruwa ba dan haka a yau ina neman alfarman ki amince alkawarin da na
aukawa Shugabana ya zamo tarihi inda zan ri
a sanin abin da zai sameki na kangin rayuwa kafin ya iso na tareshi na maidawa wanda yayo aiken."
"Godiya nake ya kai Tsidau amma ban amince ka zamo cikin marasa cika alkawari ba, ina son ka yarda komi nawa kada ka binciko sai wanda na baka dama, ka dauwamma a aikinka na
an aike tare da rakiya zuwa inda nake da muradin tafiya da kai."
"Angama ya ke Uwar gijiyana, Gimbiyan gobe bisa amincin mahaliccin tsuntsaye da tsirrai."
"Tsidau ina yawan jin kalaman nan a bakin Sadauki Gau
u sannan duk in ya furta na kanji kaina ya yi girma basirana ya toshe inda nake hango kaina cikin wani duhu tare da haske daga nesa can, shin me hakan ke nufi?

"Uwar gijiyata rayuwar Shugaba na tarin ababen al'ajabi domin duk nacina akan ya bayyamin sirrin da ke cikin kalaman nan ya k'i dan haka ban san komi akai ba domin harshesa nake kwaikwayo har na ambata miki hakan sai dai ina ta tabbacin wani abin bautane mai girma da
arfin mulkin da ya doke wanda su Sarki Gamji ke bautamawa."
"Zanzo sanin shi ko da kuwa hakan zai iya zamowa ajalina ne."
"Uwar Gijiyata kidaina ambatar mutuwa baki zamo Shugaban Tsibiri ba wacce adalcinta zai kewaye Duniya."
Murmushi ya kubce mata sannan ta fuskanci Tsidau tana mai cewa "Ya kai amintaccen Hadimina hakika mun kusa rabuwa domin da zarar na sanya Zoben, zan bacewa ganinka na har abada kai kuma zaka tsinci kanka cikin jinsinka cike da yanci daga nan kazamo yantacce daga bawa ni kuma zan mallaki Tulun ruwan albarka saidai ba zan jima ba akan karagar mulki Tsibiri Sarki Gamji sai aikomin da sako walau irin wanda ya aikowa Sadauki Gau
u ya halaka ko ya
aukeni daga yankin zuwa kurkukunsa na karkashun
asa na tabbata a can har zuwa sadda mutuwa zai riskeni dan haka yanzu
zan koma Tekun Kabobo in d'auko Zoben, ina godiya da taimakon da ka ri
a bani na duk abin da nake son ci da sha tare da sutura, gaisuwata mai yawa zuwa ga iyalenka, sai wata rana."
Momyn Haske ce
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabiban Tsibiri
By mrsjmoon
ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 follow me on Arewabooks.

Tafiya na
ara nisa inda zuwa lokacin Aliyu Malle ya tara iyali mai yawa dan ya auri bafullatanan da ta yi makuwa mai suna Mero haka ya nemi aure a wurin wani Buzu shima da ya fito ci rani yaga dajin
Mungaye ya zama maraya sai ya zauna da iyalinsa, sannan ya koma Asalinsa ya auro 'yar uwarshi Kanuri inda ya auro har guda biyu, a lokacin danginsa suka soma nuna masa
auna tunda suka gansa cikin rufin asiri musamman sarautan da yake da shi yanzu na matsayin Sarkin Birnin Mungaye.

A wannan komawa danginsa da yayi wasu daga ciki suka biyoshi tare da iyalansu sai Masarautan Mungaye ya sake cika da al'umma.

Daga nan auratayya ya cigaba da kulluwa tatsakanin kabilun uku wato Barebari, Fulani da Buzaye.

Wannan auratayya da ya kullu tsakaninsu sai ya tsakud'a ya fitar da wata kalan al'umma masu kyawun sifa gami da kyawun launin fata, fuska dana sura.

Kowa ka gani a cikin birnin Mungaye mai kyawu ne musanman 'ya'yan gidan sarauta domin Sarki da matarsa masu tsan-tsar kyau ne, wasu masu hasken, wasu mai sirki da ja da kuma masu ha
i da duhu ka
an amma duk wanda ka kalla mai kyau ne a Masarautan dan har akanyi masu kirari da Birnin Mungaye mai kyawawan Mata.

Birnin ta sami wayewa bisa ziyartan turawa inda suka gina makarantun Boko tare da kawo malamai suka ri
a koyar da su ilimin zamani duk dama can akwai masu Ilimin daidai misali musanman Sarki Aliyu Malle tare da danginsa, sai dai hak'ar Turawa bai cimma ruwa ba na samun nasarar rabasu da addinin da suka samesu akai wato Musulunci wanda burin sanja masu tunani ne su koma bin addininsu ya sanya suka shigo birnin sai suka samu Sarki Aliyu Mallae ya yi namijin kokari akan al'umman shi na ganin sun ginu akan turban gaskiya na ka
aita Allah Subbahanatu Wa Ta'alah gami da ri
o ga sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, shi yasa har izuwa yanzu Birnin Mungaye cike ya ke da musulmai, malamai gami da tsirarun mabiya addinin Yahudu da Nasara wanda suke zaman lafiya da juna domin tun tarihin kafuwar Birnin babu abin tashin hankali da ya ta
a kawo matshi ziyara ko riciki a bisa bambancin Addini ko wani tarzoma na daban sai dai su jiyoshi a makwaftansu saboda sunyi imani da Allah
aya ne kuma suna masu jajircewa wurin zaman addu'o'in samun kariya ga Birnin tare da zaman lafiya tsakaninsu suma sauran k'abilun nayin irin tasu addu'ar awurin bautarsu.

Wannan tsarin ginin tubalin zaman lafiyar duk ya samune bisa jajircewar mai Mungaye wato Malami, Sarki kuma Limamin Birnin Aliyu Malle wanda ya rasu shekaru masu yawa sai tsa-tsonshi sukayi ta gadan Sarautar har zuwa kan sarki na yanzu Sarki Abdul Hakam.

A dalin jagora tamkar 'yan uwanshi da suka gabata sai dai shi ne Sarki mafi wayewa domin dan Boko ne na gaske wanda ya taka har zuwa matakin Professor, shi yasa hawa karagar mulkinsa ya zo da sauyi wurin shigo da abubuwan Zamani fiye da sarakunar da suka gabace shi.

Abin burgewa ga wannan
asaitacciyar masarauta shi ne ri
Addininsu domin har zuwa yanzu sarakunarsu sune Limamai kuma masu gabatar da tafsirai a lokacin Azumin Ramadan dan haka babban masallacin Juma'a na garin a kofar Fada take kamar yarda mafi yawan masarauta aka sani da gina Masallatai da ake sallar Juma'a a Fadar su, saidai wannan a cikinta ake sallar Idi dan takasance mai girma tamkar wata Masarautan kaso sake ginawa haka a gefen Masallacin wani daji ne da aka killace shi aka cika shi da shuke-shuken kayan marmari wanda ina mutum ya shiga zai dauka a wani yanki na daban ya ke saboda yalwar bishiyoyi tare nisan tafiya kafin a isa k'arshenta, aka ba wurin suna da Mungaye Garden.

Wannan ak'idar da Masarautar ta ginu da shi na son Musulunci da Musulmi shi yasa jama'anta suka kasance masu karamci ga bak'i masu zuwa fatauci da zama na mundun rai.

Dan
asar Mungaye Allah ya hore mata kyawun fitar tsirrai (Amfanin gona) shi yasa Manoma suka cika garin ta ko wani sassa da ke makwaftaka da ita, lamarin da ya kara daga darajar Birnin ta zamo abar yabo ta ko ina haka duk inda
an Masarautar ya shiga yana da alfarma.

Mai martaba Abdul Hakam na da Matan Aure biyu.

Uwar gida Hajiya Hafsatu (Umma Babba) da Amarya Hajiya Murjanatu (Mami Fulani) da yara maza da mata sai dai 'ya'ya matan ne manya domin wasu sunyi aure tare da albarka zuri'a.

A yanzu Mai martaba girma ya soma kamashi, babban burinshi ya yi murabus ya dank'a mulkin hannun
aya daga cikin zaratan matasan 'ya'yanshi wato Ahmad (Sardauna) da Aliyu (Saudauki) Sai dai
urar da ke hangowa ya sa ya tsuke bakinsa akan ayyana wanda zai zamo magajinsa cikinsu, ya zuba masu ido yana sake lak'antar halayyan kowa tare da wanda Jama'a sukafi nuna k'aunarsu da ya zamo jagoransu makar yarda mahaifinsa ya yi sadda aka bashi mulkin duk da baida ra'ayi amma jama'ar gari suka nuna shi ne za
insu kuma ba jayayya 'yan uwansa sukayi masa mubaya'a sai dai a wannan lokacin baijin shi zai sami sauk'in dank'a mulki da
aya daga cikin 'ya'yan nasa ba saboda kowa yana nuna mulkin ya ke so bakin rai bakin fama.
Chapter 7 · 0% Book details