← Book details Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 27

Sashe 24

Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cin tayar mota da akayi yasa ta kalli wurin a hanzarce hango
anta Hud cikin maye yasa ta bu
e robar ruwar hannunta wanda ke da sanyi ta nufeshi a fusace ta watsa masa ya saki a jiyar zuciya yana kallonta idanu jajur sake juye masa ragowar ruwan tayi a fuska aikam ya rarumota ta kwasa da gudu ya rufa mata baya yana huci.

"Mamma kizo danki mara amfani zai illata miki ni."
Abinda take ambata kenan tana
maimaitawa sadda tayi nasarar shiga falonsu, Mamma ta fito zani na kufcewa dan tunda tajiyo kalaman Zuhrah ta san ita da Hud ne wanda tayi imani ya koma ruwane na shigowa Masarauta cikin maye lamarin da Zuhrah ke adawa shi kuma hakanne yasa tayi mugun rainashi duk da ba ita ce sak'onshi ba domin a kwai mutum biyu tsakaninsu kafin ita.

"Me yasa ne Hud? kamanta tijarar Abbanku Chiroma ko?

Shin kana ganin wannan gaulancin zai kaika zuwa ga hawa karagar Sarautar Birnin Mungaye?"
Da sauri Zuhrah ta anshe da "Ina kuwa domin wallahi ko ni sai na yi sanadin rashin hawarsa domin mu ba 'yan maye ba ne balle ya hau ya maida giya ruwan fanfommu duk mu lalace, kanmu ya kwance kamar yarda nasa yake a kwance."
Tama rufe baki ta k'wallah ihu domin a fusace ya jefota da zobbesa mai kama da k'ashi, ya ko sameta a goshi a take jini ya wanke mata fuska, Mamma ta yi kanta tana rafka salati fadi take "Hud kiramin Dr Neerah ta bata taimakon gaggawa domin ban son Masarauta susan wannan abin kunyar da ka aikata."
"Sai dai ta mutu wallahi Mamma indai sai na kira an bata taimako ne."
Ya ambata cikin rabewar murya irin na 'yan maye.

Wani a shar Mamma ta mulmulo ta antaya masa ko ajikinsa sai ma ya kwashe da dariya ya tura kai d'akin Zuhrah ya fa
a saman Cushing yana sunbatun sai ya illata rayuwar Zuhrah tunda ta rainashi, daga haka barci yayi gaba da shi.

"Mamma jijiyar idanu zasu tsinke kiyi wani abu kada na rasa idanun gani, wayyo!

Na shiga uku na lalace, walalhi ba zan yafewa
anki mara amfanin can ba."
A gigice Mamma ta kamota tare da tara d'ankwalinta a goshin tana zabga salati gami da toshe mata baki dan ta daina aibata
an uwanta tare da gudun kada wani ya jiyo.

"Mamma kaini Mungaye Clinic kada in rasa idanu cikar ado da k'walliyar duk kan mutane musanman mata."
Bata da za
i zai fito da ita zuwa Clinic duk da bata so hakan ba saboda bata son labari ya fito cewa Hud ne ya jima shalelenta ciwo domin a bayyane nakasu ne gareshi akan burinta na ganin ya haye karagar mulkin Mungaye.

Tsibiri.

Iskan bai tsaya a
auke masu gani ba har da halaka jama'a, a cikin abinda bai wuce mintoci biyar ba ya halaka mutane masu yawa.

Tsibiri ya hautsine da iface-iface na neman dauki, cikin fushi Sarkin ya
i wato mahaifin Buda ya aika sak'o cikin aikin alk'aliman sihiri zuwa ga Abun akan su dawo Tsibiri zai kama da wuta sannan ya soma
arin tsaida guguwan cikin kwarewar tsafi sai dai lamarin ya sha
arfinsa, suka taru suka ha
arfi kamar yarda sukayima na farko nanma bata sanja zani ba sai kawai suka soma neman matseta tare da bawa jama'a taimakon wurin b'uya.

Rugugi ne ya doso Tsibirin abinda ya sanya iskan nan lafawa, tamkar k'iftawar ido iskan ta
ace, zuwa can Lina ta bayyana fuska a daure, kafin su ankara ta soma huro sanyi wanda ke fitowa daga bakinta na shiga jikkunar Jama'a inda ke warkar masu da raunin da suka ji tare da tashin wanda suka jikkata, ta
auki tsawon mintoci goma tana huro iskan kafin ta dakata tana kallon al'umman da duk suka samu natsuwa suka sakata a tsakiya suna yi mata kirari da Gimbiyarsu mai tausayi.

"Kuyi hak'uri da matsalar da 'yar uwana ta janyo muku, yanzu ku tafi ku kauda wanda suka mutu tare da cigaba da harkokinku zanyi bakin iyawata wurin kare lafiyarku domin wannan shi ne burina kuyi rayuwar 'yanci wata rana."
"Mungode shugaban gobe, Sarautar Tsibiri naki ne Gimbiya Lina."
Suka ambata a tare cikin daga murya.

Jinjina kai tayi ciki da alfahari da su.

Suna watsewa Abun ya bayya tare da Buda, Lina na jin alamun takunsu ta
ace ta bayyana cikin Bukkan Kaka Gunu inda ta sami Lima sunkuye kan Mah tana aikin ceto ranta.

"Sakacinki ya janyo Mah zata mutu, wannan bak'ar ranar nake jiye mana har na umurceki da ki kula da ita amma saboda son zuciya irin naki kin kasa zama da ita kin taho neman cikar burinki, to ki zauna a nan tare da ita domin fitowarki kiran ajalinki ne domin Jama'an Tsibiri sun fusata da kashe masu dangi da kikayi sanadi sannan Abun yana farautanki kamar yarda yake faraunata da Mah."
"Me kike nufi da Abun na farautanmu?

Alhalin mu ne ka
ai sanyin idanunsa."
"Lima yanzu Abun ya sanja dan shi ne ke wasa da rayuwar Mah domin ya samu hankalina ya dawo kanta inda zai hilace ni ya mallaki Zoben da ke hannuna wand zai bashi damar samun
arfin tsafin da ya zarce na kowa dake zamanin nan haka ya fiki burin son mallakan Ruwan Albarkan Kaka Gunu domin shima na
auke da sirrika masu girma akan tsafi da cikar mulki, ki sani a yanzu mu ne damuwarshi akan haka ya kudiri halakamu baki
aya indai zamu kawo masa tangarda a samun tsawon rayuwa akan mulki."
"Ta ya zan yarda da gaskiya kike sanarmin ba yaudarar da kika saba yimin ba ne?

"
"Ifritu Mutuwa zai gasgatani."
"Tabbas zantukan yar uwanki Lina ba
arya duk da itama tana son shan ruwan albarkan domin ta sake finki komi dan hawa karagar mulki, ko ba haka ne manufarki ba ya ke Gimbiya Lina?"
"Tabbaas haka ne kuma har a yanzu ina cikin muradin rigaki mallakan ruwan albarkan sai dai ba yanzu shi ne a gabana ba domin haka kaima Mutuwa dole ka dakata da taimakonta na mallakan Ruwan har sai na kammala da abinda ke gaba in yaso sai kayi mana k'uri'a duk wanda ya ci shine mai mallakin gadon Kaka Gunu."
"Baki isa ba Lina, ni ce ke da gadon Ruwan Albarkan Kaka Gunu dan haka ki fitar da ranki akansa."
Murmusawa Lina ta yi batare da ta furta kalma ba ta isa gaban Mah da ke shimfida tamkar gawa ta sunkuya ta shafi fuskanta wani haske ya sauka a fuskan zuwa ilahirin jikinta aikam sai ta soma tari tana kiran sunar Abun da ya zo ya taimaketa.

"Mah kina tare da 'yan biyunki kuma bisa kulawarsu kika tsira daga ba
in iskan da Lima ta yi jagoran shigowarsa cikin al'umma, yanzu zan barki a wannan Bukar ta Kaka Gunu Lima zata kula da ke zuwa sadda zan dawo na maidaki inda duk
arfin tsafin matsafi yayi ka
an ya iya zuwa wurin."
"Ki dawo lafiya Ruhin Sarki Goma ya baki kariya."
Motsa kai tayi tare da mik'e ta kalli Lima da ta tsare giran sama da
asa ta hurama fuskanta iska kan dole ta murmusa saboda tunowa da lokacin baya da take azabtar da Lina da iskan bakinta.

"Yawwa kin tuna muguntarki na baya ko?

To ki natsu kiji me zan sanar da ke, ki zauna a nan kamar yarda na sanar da ke a farko, ki kulamin da Mah, Ifritu Mutuwa zai kula da ku sannan zan batar da Bukkan Kaka Gunu a idanun Abun wanda ke nufin isowa bada jimawa ba."
Lima zatayi magana Lina ta daga mata hannu tare da cewa "Kada kiyi yunkurin barin Bukkan nan dan zuwa watsewarki domin yin hakan wasa da rayuwarki ne domin kina fita zaki tsinci kanki a akurkin sihiri ko na Abun ko na Ifritu Baushe kuma ki sani bana da lokacin taimakonki saboda lamarin Mah d'ita ya fiyemin komi, in kinji gargad'i ruwanki, ni zan wuce ba zan jima ba zan dawo dan bana son na wuce kwanaki biyu rak ban kammala abinda naje yi ba."
Kafin Lima ta furta kalma Lina ta zama farin hayaki ta b'ace kallonta ta sauke kan Ifritu Mutuwa sai ya jijjiga kai tare da bude tafin hannunsa saiga wurin ya sanja, ya dawo dauke da kilisai masu laushi da makeken gadon alfarma, jinjina tayi masa ya gya
a kai tare da b'acewa, ta doshi gadon ta hau ta kwanta ba jimawa barci ya dauketa cike da burin sai ta fita wurin nan taga abinda zai faru.

Mah itama gadon ta hau cike da tarin damuwa.

Lina na fitowa ta jiyo takun Dokin Buda sai ta zama balbela ta haye saman bishiya suna wucewa ta sakko ta watsa haske a baki
aya Bukkan ta lula sararin samaniya.

Abun tsaye a turakansa yana kai da kawo cikin tarin damuwa zuwa can ya ja iska ya fesar tare da zama akan k'ok'on kan Giwa ya na cije lebe, ya sharce Gumin da ya feso masa a goshi tare da mikewa a fusace ya kaiwa bango duka cikin ambatar "
arya ne, saina Mallaki Zoben hannunki Lina sannan yar uwanki zata kasheki a gaban mahaifiyarki, a yanzu bana da abokiyar gaba sama da ke, zan nuna miki ta yaro kyau take amma bata k'arko, ki sani ba zan barki ki Mulke ni ba alhali ina rayuwa, tabbaas a yau na musanta kalman cewa bazanyi fito na fito da ke ba haka na gasgata kalamin Kaka Gunu da ya ce samuwarki cikinmu masifa ce domin zaki karya k'adarinmu ki sanja tarihinmu ki watsa mana Martaban Tsibiri hak'ik'a dana sani na bashi dama a can baya ya sanya kinbi rariya ya zamo Lima kawai zata zo duniyarmu."
Momyn Haske ne
*Muna saida ingantaccen man ayu wanda ya zo daga Chad.

Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon
afa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848.
Chapter 24 · 0% Book details