Sashe 20
Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga haka ta b'ace daga jikin bangon Mah ta fuskanci Lima cikin tsuke fusaka ta ce "Daga yau ban son nasake jin kin ambaci tsana ga 'yar uwanki idan kuma kika sake zan nunamiki wacece ni sannan bana son zuwa mashaya da kikeyi shi ke janyo miki tsana ga Jama'ar Tsibiri domin hatta da mahaifinku baya son abinda kike aikatawa, kiyo koyi da 'yar uwanki zaifi miki khairan ko kya samu damar hawa karagar mulkin Tsibiri wanda ya ke babban burinki."
Sai a nan ta saki rai jin ta ambaci hawa mulkin Tsibiri ta dawo gaban Mah ta zauna tana wani langab'ewa kana ta ce "In har kina sona da mulkin Tsibiri to kije d'akin Abun ki tsareshi kada ya biyoni domin mallakan gadona na wurin Kaka Gunu."
"Kunfi kusa Lima ki rok'eshi ya bar maki kayanki."
"Ba zai bari ba Mah domin shima na burin mallakan Ruwan Albarkan."
"To ki gyara mu'amalanki da Lina na san zata taimakeki ki mallaka."
"Idan itama burinta na ta mallaki Ruwan ne fa?"
"Zata bar miki domin adala ce kinfi kowa sanin hakan."
"To zan nemeta mu sasanta."
"Haka na ke son ji 'yata."
Juya kai gefe Lima ta yi tana haskowa ruhinta wani mugun nufi akan Lina sai ta saki murmushi tare da hayewa gadon Mah ta kulle ido ganin haka yasa Mah ta fice zuwa turakar mijinta wannan damar Lima ta samu ta mik'e ta shafi bangon da Mah ke hira da Lina sai kuwa ga Lina ta bayyana saman dutsen kogin Babobo iska na kad'a gashinta na rufe mata fuska tana yayewa.
"Ya akayi Lima?
Na san zaki nemeni shi yasa na tura Tsidau ya taimaki mutanen girjin na dakata jiranki, ina saurarenki."
"Ki zo ki taimakeni na
auko gadona a Bukkan Kaka Gunu."
"Zan zo amma ba yanzu ba sai Abun ya taho nemana dan haka ki nuna mashi kin hak'ura da gadon hakan zai bashi damar barin Tsibiri a sirrance domin yanzu yafi bu
atar mallakan Zoben dake gareni akan ruwan albarkan."
"To sai kinzo ina da abinyi."
Murmushi Lina ta yi tare da mik'ewa ta kalli Lima ta ce "Zan zo mu kwana tare yau sannan zan baki labarin da kike nema na cikin jikina da wanda yayimin."
Cike da zumud'i Lima ta bu
e baki zatayi magana Lina ta d'aga mata hannu tare da b'acewa a take bangon ya dawo yarda ya ke.
Dafe kanta ta yi cike da takaicin b'acewar Lina.
Ta fito zuwa d'akinsu dake saman wani dutse daga gefen turakar Mahaifinsu.
Mah na shiga turkan mijinta ta fahimci yana d'akin sirri sai ta sami wuri ta zauna ta tsirawa wani taswira
ido wanda sai a yau ta ganshi a turakan sai ta shiga mamakin lamarin abinda ya
auki hankalinta har ta shagala da kallonsa sai ta soma ganin tamkar ta koma wani wurin ba turakan take ciki ba, mik'ewa tayi dan isa gaban Taswiran sai taga haske na fitowa daga cikinsa da ta matsa sosai sai taga hanyace ta bu
e daga cikin Taswiran sai taja da baya cike da tsoro amma sai taji ana janyota sai ta soma tattaro tsafintata dan amfani da shi sai dai ya kasa tsiri wurin bata kariya, ihu ta soma dan neman taimako amma sai muryanta ya daina fita illa ita
aya takejin fitar kayanta, tsawon lokaci ana son jefata cikin Taswira ita kuma tak'i shiga duk da tsafinta ya k'i aiki sai dai tun can ita
in mai
arfi dantsen ne.
Mah ta jigata iya jigata har ta sare,
afarta na hagu ya soma shiga hanyar inda takejin hucin zafin wuta na dokar
afar.
Sauka wani abu taji dif!!
Kafin ta tantance meye iskan guguwa ya nad'eta ya jangota.
A take Taswiran ya nad'e kansa ya b'ace b'at, bangon ya koma tamkar wani abu bai ta
a zama ba.
" 'Yata Lina."
"Na'am Mah, kwanta ki huta nadawo Tsibiri bazan sake barinki ba ko da hakan na nufin ajalina ne."
"Me ke faruwa Lina?"
"Mah cin amana yayi yawa, zalunci ya kewaye duniya ya zamo har da na jikinka za'a cuceka."
"Waye ya so aikatamin mugun abun nan?"
"Mah saninsa tarin damuwa ce gareki amma da sannu zaki san ko waye ke farautan rayuwarki domin ya sami cikan burinsa na samun Duniya."
"Lina taho na runguneki."
Ba musu ta iso gaban mahaifiyar nata suka rungume juna, hawaye na zubowa daga ida uwarsu na sauka a gadon bayan junarsu.
"Zan sanja miki wurin zama mai cike da tsaro Mah."
"A'a Lina ki barni a nan mahaifinku garkuwa ne gareni."
"Idan shi ne ke son halakaki fa?"
"Ba zai ta
a faruwa ba Lina, duk tarin zalunci mahaifinku ba zai ta
a sadaukar da abinda yafi so sama da komi ba dan haka ki barni tare da shi tunda kin dawo ba abinda zai sameni."
Janye jikinsa Lina ta yi batare da ta sake furta kalma ba, ta soma zagaye d'akin zuwa can ta tsaya ta dubi Mah ta ce "Ina da aiyuka a gabana wanda ban san adadinsu ba kuma ban san mai taimakamin ba haka ban san ranar kammalasu ba."
"Ki sassautama kanki lamaura ya ke 'yata kada na rasaki."
"Mah banzo duniya dan samun hutu ba, ina cikin matsala tunda nace zan saka Zoben can mai makon naga lamura nayimin sauk'i sai sake rikicewa sukeyi shi yasa nake neman amincewarki da ki yarda na nesantaki da Tsibiri na wani lokaci in komi ya daidaita sai na dawo da ke saboda zamanki anan barazana ne a gareni domin za'a ta
amin ke dan a sami galaba a kaina, Mah ki amince na maidake saman Tekun Kabobo na killaceki ko kogon da gangan jikin Sadauki Gau
u ke ciki nayi miki alk'awarin zuwa ganinki kullum dan
ebe miki kewa haka komi kike so na dangin abinci da bin sha zaki samesu."
"Lina kincemin fa kin dawo Tsibiri to me yasa zaki
aukeni a cikinsa ke ki zauna."
"Na sanar miki da hakan ne dan hankalinki ya kwanta amma ban dawo ba."
"Lina ba inda zanje."
Tamkar zata fashe da kuka take duban Mah sai kuma ta zabura ta nufi k'ofar fita tana cewa "Mah zan dawo anjima kada ki sanar da kowa zantukanmu ko da kuwa Abun ne ko Lima."
Kafin Mah ta yi magana ta fice a gaggauce, hawaye ne suka zubowa Mah na tausayin rayuwar da 'yarta ke ciki domin tana burin rayuwa da 'yarta a kusa da ita tamkar yarda takeyi da Lima.
"Lina dole ki janye son hawa karagar mulkin nan ko na samu kusanci da ke kamar can baya."
Mah ta ambata cike da tarin damuwa.
"Mah."
Da sauri ta waigo Lima ce tsaye.
"Kin ha
u da 'yar uwanki Lima?"
"A'a, shin ta zo ne?"
"Eh."
"Me ta sanar da ke?"
Batare da tuno gargadin Lina ba ta sanar da Lima duk abinda ya faru tundaga zuwarta turakan Abun har tafiyar Lina.
"Ina zuwa."
Itama ta fice da sauri tana fita ta yi girgiza sai ga Abun ya bayyana fuska a murtuke.
"Hak'ik'a Lina kina da wayau dole na san waye Sadauki Gau
u kafin na mallaki Zoben sirihin hannunki ta wannan hanyar na basaja tabbas yanzu zanyi fito na fito da ke duk da ba hakan raina ya so ba."
Ya ambata cike da
acin rai.
Ba jimawa Buda ya isa saman
ingarman dokinsa Abun ya hau ya zabura cikin takon dake motsa
zuwa can ya d'aga sama tamkar tsuntsu ya b'ace cikin gajimare.
Lima da duk abinda da ya afku akan idonta ta shiga mamakin lamarin sai kuma ta saki murmushi tare da shigewa d'akin Mah ta isa gaban bangon da Mah ke hira da Lina ta shafa take kuwa Lina ta bayyana cikin shigar yak'i fuskanta babu d'igon annuri lamarin da ya razana Lima domin bata ta
a ganinta cikin
acin rai irin wannan ba tun tasowarsu.
"Me ke faruwa 'yar uwa?"
Lima ta jefo mata tambayar a rikice.
"Ya wuce
aukan tunaninki Lima, ni dai ina son ki kulamin da Mah, kada sakacinki na yawon zuwa mashaya ya janyo na rasa Mah, domin in hakan ya faru na rantse da ruhin Sadauki Gau
u sai na illata rayuwarki ki zamo baki da mamora balle ki sami damar zuwa timb'ele a mashaya."
"Kada kiyimin barazanar da har abada nafi
arfin sa kawai ki sanar dani abinda ke faruwa ko ina da halin taimakawa akai."
"Ki kula da Mah shi ne ka
ai taimakon da zaki iyayi."
"Kin san shirin Abun kenan?"
"Eh wanda hakan na nuni da rayuwarsa na daf da zuwa
arshe."
"Me kike nufi?"
"Zan tafi idan na dawo zan sanar da ke komi batare da kin tambayeni ba."
Sai kin dawo amma ki sani ba zan zauna gadin Mah ba tunda ba dan shi na zo duniya ba."
"Shi kenan na barki lafiya amma ki kwana da sanin rasa Mah tamkar nak'asarki ce, wata
ila makanta, kurumta ko gurgwanta sai kiyi nazarin abinda zai fish-sheki domin tabbas sakacinki yasa na rasa farin cikina wallahi kema kinyi ban kwana da naki farin cikin.
Ki kula da Mah shi ne
arshen umurnina gareki Lima."
Kafin Lima ta yi magana bangon ya dawo yarda yake tamkar komi bai wanzu ba a mugun fusace ta fice batare da ta kula kiran da Mah ke yi mata na kula da ita ba dan ta shiga rud'anin kalaman Lina har tayi da ta sanin k'in binta da tayi.
Bukkan Kaka Gunu Lima ta nufa ta shige batare da samun tangarda ba.
"Zannuna miki ni ce shugabanki Lina kuma magajiyar karagar Tsibiri, a yanzu banjin ko Abun zaifini
arfin iko balle ke 'yar tsako abar tausayi."
Ta na rufe baki dutsen dake Bukkan ya dare biyu wata gawurtacce mikiya ta bayya ta iso gabanta ta zube tare da rikida zuwa mutum maiji da Sadaukantaka ya russuna cikin cewa "Barka da zuwa magajiyar Tsibiri shalelen mai gida Gunu, raina fansa ne gareki ya ke uwar gijiyata."
"Waye kai?"
Ta ambata cike da izza duk da tana kokwanto ko Tsidau ne ya sanja salon yaudara.
"Ki kwnatar da hankalinki ba mayaudari Tsidau ba ne a gabanki wannan amintaccen Hadimi ne sunana Mutuwa babban
hadimin Kaka Gu...