Sashe 3
Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A razane ta tashi zaune tana sosa bayanta cikin son tuno abin da ya faru amma ta kasa kamo komi tsaki taja ta dubi bangon d'akin tare da hura iskan bakinta sai ga Lina ta bayyana tana zabga murmushi yamutsa fuska ta yi tare da mik'ewa ta ja hannunta tana cewa "Nagaji da wannan wahalar narantse duk inda kike sai na nemoki domin hakan ya tauyemin jin dad'in rayuwata na tabbata Lina kin aikata min hakan ne dan murgunamin tare da hanani fita holewata amma duk ranar da na yi ido biyu da ke bazakiji da da
i ba."
Duk yarda taso jin basaja fushin da ke fuskanta ya koma irin murmushi fuskan fake Lina ta kasa saboda yau ta fusata sama da kullum, ga shi Abun bai nemeta ba taji son zuwa gareshi.
Wani tsakin ta kuma ja tana dokawa dake Lima harara ita kam sai murmushi dake dokawa abinta.
"Wallahi ba dan rabi ruhina da ke nanne jikinki ba da yau na kasheki na huta."
Gurnani tajiyo a bayanta ta juyo cike da masifa amma bataga komi sai sake jan tsaki zuciyarta na
ara shiga
unci.
Fadar mahaifinsu ta nufa kai tsaye, tana shiga fadawan suka soma mik'o gaisuwa cike da tsoro ba wanda ta kula ganin haka suka watse aka barta da mai Tsibiri.
Ta iso ta sunkuya gabanshi ya mik'a hannu zai dafata ta tashi da sauri tana dariya fake Lina da ke bayanta duk'e itama ta tashi tana dariyar girgiza kai Dattijon ya yi tare da kaiwa wani tulu duka a ta ke dake Lina ta nufi jikin Lima ta shige suka zama a bu d'aya, ya kalleta ta sunkuyar da kai ya nuna mata hanyar fita cikin fushi sai ta iso gabanshi ta zauna tare da kamo hannunshi.
"Kada kice komi Lima na jima da gano Lina bata wannan tsibirin sai dai tsawon lokacin na kasa gano inda ta b'oye duk da bincikena yana nunamin tana rayuwa cikin walwala da 'yanci amma na kasa samun natsuwar ruhi akan inda ta ke da dalilin aikata mana wannan munafuncin sannan ina hango wani haske mai son maidani makaho a tare da ita amma a yau Buda ya gano mab'oyarta a k'asan Tekun Kabobo kamar yarda bincike ya bayyanarmin mintoci biyu kafin shigowarki, yanzu haka ina dakon isowarsu ne duk da ina shakkar isowar sa tare da ita."
"Saboda me Abun kake shakka?"
"Lina ta soma bani tsoro da gaske ba wasi-wasi."
"Abun me ya razanaka da ita haka, alhalin ko tsun-tsun Tsibiri bata iya kamawa saboda sokancinta da rashin amfani?"
"Kayya Lima, ki bi a sannu domin wannan sabuwar Lina ce mai cike da sadaukantaka ta fannoni da dama haka bincikena ya haskomi halin nan nata na tausayi shi ne zaiyi sanadin kawo k'arshen Hatsabibin Tsibiri mai dogon tarihi domin ba'a gina shi dan adalci da tausayi ga bak'i ba amma ita ce ta farko da zata shigo mana da sauyin da dole mu amsa kamar yarda taso yin nasara a baya."
"Ta ina hakan zai sake faru Abun?"
"Ban sani ba Lima amma ina lalibo hakan a lokuta da dama tun kuwa kuna tsumman goyo shi Kaka Gunu ya keb'eki ya rik'a nuna miki sanin ilimin tsafi fiye da ita ya kuma raini ruhinki da rashin tausayi wanda kika rik'a wahalar da ita mahaifiyarku na yi miki kashedi kina watsi da kamarin saidai a yau na hango alamun ta samo sanin alk'aluman tsafi fiye da wanda kike tare da shi dan na kalli artabunku na d'azun duk da ta yi dubarar
b'oyewa cikin iskan guguwa dan ta san zan gani sai amma ta makaro dan komi ya bayyana gareni tamkar kuna gabana."
"Abun dama ba mafarki na yi na had'u da Lina ba har muka goge raini?"
"Eh ba mafarki ba ne, tabbaas kin had'u da Lina wanda hakan ya bawa Buda damar gano inda ta ke ta
bayan b'atan dabon da ta yi na tsawon
shekara d'aya da watanni ta hanyar jiyo k'amshinta wanda ta nan mafi akasarin jama'ar Tsibiri ke ganeku.."
"Abun me kake son sanar dani akan 'yar uwata Lina?"
"Babu komi 'yata illa hatsarin da Lina zata zame mana musanman ke domin zuciyarta ya ginu da tausayi ne ya yin da na ki ya ginu da tsabar mugunta, Kaka Gunu ya sanarmin d'abi'unki na kamanni da kakan-kakanninmu wanda shi ne silar samuwar Tsibirin nan wato Sarki Goma na farko."
"Abun rabani da wannan zantukar gaibun na Kaka Gunu yanzu babban damuwata shi ne sanin gaskiyan abin da Lina ke b'oyewa."
"Nafiki son gano lamarin da ta birne wanda bokayenmu suka kasa gano shi hatta kuwa da ni sarkinsu kuma jagorar wannan tsibiri."
"Abun, shin yanzu Lina tafika k'arfin tsafi kenan?"
"Bata isa ba Lima."
"To meye yasa ka kasa gyara Mata zama?"
"Har abada bazan tab'a fito na fito da ita ba saboda ina son 'yata haka itama bazata tab'a yin gaba da gaba da ni ba domin girman da ta ke ganina da shi ya wuce tunaninki tana kawai nuna miki tafi damuwa da mahaifiyarku ce kamar yarda kika fi nuna damuwa da ni sannan zan baki aiki wanda na san akanshi kike wato na son gano lamarin Lima baki dayanshi na tsawon tafiyar da ta yi."
"Ina saurarenka Abun."
" 'Yata Lima a yanzu nake son ki shiga bukkan Kaka Gunu kiyi wannan binciken."
"Abun yau da kanka ka amince in shiga taskan sirrin Kaka Gunu wanda ya ke kulle tun bayan mutuwarshi?"
"Eh na baki damar shiga ya ke 'yata, dama can gadonki ne dan ya tabbatar min ke kad'ai ya mincewa shiga bukkar amma bisa babban bincike shi yasa na baki umurnin shiga dan gano mana abin da Lina ta b'oye da kuma wanda ya koyar da ita dabarun ilimin sihirin da ya ke son doke wanda muka gada Kaka da kakanni."
"To Abun kasan da wannan wasiccin ka barni ina ta wahala tsawon shekara d'aya da rabi akan wancan sokuwar yarinyar?."
"Akul Lima!
'yar uwarki ce bana son wannan tsanar da kike nuna mata wanda na yi imani shi ne silar b'oye miki sirrikanta ga shinan zai wahalar da ke a banza."
"Abun bana sonta tunda Mah ta nuna da ita take yi ba ni ba."
"Lima kin sanfa an raba ne ke ce nawa ita kuma na Mah
in ku."
"Na barka lafiya Abun gobe da safe zan taho maka da bayanai wanda na amince tono sirrin Lina ce kaf d'inshi."
Ta ambata tare da mik'ewa bayan ta subbaci bayan hannunshi.
"Baburdo ya taimakeki 'yata."
"A'a Abun ruhin Kaka Gunu ya bani sa'a zakace domin Baburdo Dodon gadin Tsibiri ne bai isa bani taimakon komi ba saima ni ce keyi masa alfarma na sha
ar ni'imar Tsibirin."
"Haka ne Lima to ki fito lafiya cikin kiyayewar Ruhin Kaka Gunu."
"Amin."
Ta fice cikin sauri tana yarfe hannaye cikin salon mugunta inda yarfin ke fitar da iska na watsar da mutanen da duk ta ci karo da su a kan hanya wasu tsoffi ne da yara k'anana ya yin da masu
arfin tsafin ke kare kansu tun kafin ya iso inda suke, ganin jama'a na neman wurin buya saboda giftowarta sai tayi amfani da wuta da kunna a tsakiyar Tsibirin a take mutane suka soma kulle gidajensu masu sana'a suka tsere wutar ta soma bin kayansu tana lashewa, sai hakan ya wadata k'irjinta da nishad'i tayi ta zabga murmushi, batare da ta kula da illar da wutar takeyiwa jama'ar ba tayi gaba abinta tana dariya.
Ruwan
ara ne ya sauko a cikin minti
aya ya kashe wutar tare da
aukewa batare da sanin Lima ba hakan ya afku, jama'a suka dawo bakin kayansu suna tsinewa Lima a cikin zukatansu.
Tafiya mai tsayi Lima ta yi kafin ta isa bakin bukkan da ke cikin kogon wani dutse duk a saman Tsibirin.
WAIWAYE A DON TAFIYA.
*Asalin Tsibirin da mutanen da ke rayuwa a cikinsa.*
Hatsabibin Tsibiri, Tsibiri ne mai dogon tarihi domin sarakuna masu dama ne suka shud'e a cikinsa kuma dukkannunsu abisa turba d'aya suka ginu wato tsafi da kafurci domin basa da abin bauta balle wurin bauta, gasu nan dai kara zube domin ko Dodo Burda da ke TSIBIRIN basa bauta masa dan a mai gadi suka ajiyeshi ta hanyar yin bishara idan bak'o ya shigo ko samun wanda ya karya doka na yiwa mata fyad'e dan duk da wannan duhun da suke ciki suna kyamatar ketawa mata haddi.
Mafarin TSIBIRIN ya samu ne bisa jagorancin sarkin farko mai suna GOMA wanda aka ci shi da ya k'i inda ke mulkin al'uma masu yawa, sakamakon rashin nasarar da ya yi ne ya yi hijira da iyalansa ya yada zango a Tsibirin lokacin wurin sansanin miyagun namun daji ne da suka kashe
dajin mafarauta da makiyaya suke tsoron haurowa samansa,.
Saukan sarki Goma ya sa suka koma gefen TSIBIRIN suka kewayeshi cikin yi masa mubaya'a domin k'arfin tsafinsa kad'ai ya isa zamowa bara zana ga rayukansu.
Sarki GOMA ya yi nasarasar k'awata TSIBIRIN cikin alk'aluman sihiri yarda kowa ya keto cikinta sai ya burgeshi kuma ya zamo ganimansa in ya so ya maidashi bawa in kuma ya so ya kasheshi musanman idan ya bincika yaga mai addini ne.