← Book details Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 27

Sashe 5

Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Musanman Sarki Barde yasa aka farauto driver da motarsa, ya sami wata biyar yana ko yawa mutane uku nan mota bayan sun kware ya korashi daji inda Namun daji sukayi watanden namansa bayan ya turawa 'yan matan Tsibirin sun gama zuk'e masa ruwan jiki da jarabarsu daga nan labarinsa ya zamo tarihi.

Sarkin ya sama musu motoci uku lafiyayyu inda suka soma shiga cikin gari suna mu'amala da su ta hanyar fitar da amfanin gonansu su siyar su siyo wanda basa shukawa tare da sutura irin tasu sai dai duk in zasu shiga gari sukanyi shiga irin na makiyayan usul wani zubin kuma suyi irin na kabilun da suke hurd'a da su shi yasa abokan huld'an kasuwancin nasu basu gano daga inda suke fitowa ba balle su zama abin tsoro.

Duk wannan lamari da ake ciki Tsibirin baida magaji domin matar Sarki Barde bata ta
a yin bari ba, ganin haka sai ya dukufa yin tsafi akan ya samu haihuwa inda kakanshi Gunu ke tausarshi da cewa zai haihu da zarar lokaci ya yi.

Kwatsam bayan shudewar wasu shekaru matar sarki ta sami rabo inda ta haifi 'yan biyu dukansu mata masu kama d'aya tamkar an tsaga kara, ranar suna anyi bidiri na gaban kwatance daga bisani aka sanya musu suna Lina da Lima inda suka ci gaba da girma bisa kulawan mahaifansu da kakan mahaifinsu wato tsoho kaka Gunu.

Sai dai tun suna tsumman goyon suka taso da bambancin ra'ayi inda Lina mai tausayi ce Lima kuma muguwa, hakan yasa basa ga maciji da juna.

Lima ta soma cutar da 'yar uwanta Lina tun kafin su san kansu sai Mahaifiyarsu wanda suke kira da Mah ta maida kulawarta ga Lina shi kuma Abun ya maida nasa kulawan kan Lima inda Tsoho Guna ya mara mashi baya.

Sadda suka soma tasawa sai Kaka Gunu ya killace Lima ya soma koya mata dabarun tsafi da yak'i ya yin da itama Lina ke amsar horon wurin d'an sarkin yak'i Buda a b'oye batare da sanin kowa ba wanda ya kamu da sonta batare da ta san yanayi ba, dalilin da ya k'udiri aniyar horar da ita kenan domin yana sane da wariyar da Kaka Gunu ke nunawa tsakaninta da yar uwanta sai dai abinda bai sani ba horarwan baiyiwa Lina amfanin komi saboda kafin ta dawo gida Kaka Gunu zai lalatashi idan ta dawo nanma mahaifiyarta kan cigaba da koya mata tsafi domin tasan ilimin sosai wanda shi ne ke amfanarta domin Kaka Gunu bai lalatashi bisa wani dalili nashi na daban.

Ganin sun soma taka makakin girma sai burin Sarki Barde ya koma kan tagwayen 'ya'yan dan yana aiyana wata rana d'aya daga cikinsu zata jagoranci jama'an Tsibirin domin su kad'ai ya mallaka saidai burinshi yafi karkata akan Lima saboda muguntarta da k'arfinta tamkar babban sadaukiya sabanin Lina da ke da sanyi tare da gudun zalinci dan lokacin suka shiga shekaru goma sha
aya a duniya amma a haka Lima ke iya dambe da manyan sadaukai kuma ta samu nasara akansu.

Tunanin mai Tsibiri daya dana Kaka Gunu duk da a tarihin Tsibirin mace bata ta
a jagorantar su ba.

Lokacin da suka taka matakin cikakkun 'yan mata sai rashin jituwar su ya k'ara tsanani sakamakon ganowa da Lima ta yi
Sadauki Buda na son Lina wanda ta ke ganin bata isa kaiwa matsayin ba alhalin gata wacce ta tara abin so fiye da ita kamar k'arfi da tarin ilimin tsafi, wannan dalili ya tunzurata ta
ara k'aimi wurin murguna mata ya zamo bata jin dadin zaman Tsibirin kwata-kwata, sai ta soma keb'e kanta tana rayuwa ita d'aya inda Lima zata binciko wurin taje ta mallake a cewar ita ce ke da ikon mallakan wurin hutawa sama da Lina.

Tsananin Lima ya soma kai Lina bango gashi bata son suna fada da juna, sai kawai ta koma duk in ta fita rangadi sai ta ajiye kuyanginta a bayan gari ta zama tsun-tsuwa mafi gudu cikin tsin-tsaye ta nufi biranen da ke da nisa da su inda zatayi ta ganin ababen al'ajabi musanman bauta da taga jama'a na yi a killatattun d'akuna masu kyau abin da yafi bata mamaki shi ne ganin yarda suke gudu idan ana magana a abin fitar sauti (Kiran sallah kenan) sai ta lalace wurin kallonsu gami da sauraren muryan da ke fitowa (Karatun Qur'ani kenan) ta kan b'ata lokacin tana saurare tare da son shiga wurin amma sai ta ri
a jin hucin zafi na dawo da ita baya inda zatabar wurin a d'imauce amma idan ta nemi shiga dayan ginin da ake kida da rawa gami da wak'a sam bata jin hucin zafi sai tafi maida hankali a wurin inda zatayi ta binsu suna tikan rawa batare da ta bayyana masu fili ba balle su koreta har ta soma
aunar yaren da suke magana da shi ta soma fahimta ka
an-ka
an.

Wani zubin kuma in ta shigo birnin sai ta tare a makarantun boko inda wannan ya bata damar jin yaren turanci managarci har take fahimtar abinda ake koyarwa a d'akin da ake yin rawa da wak'a.

Sosai ta sami ilimin boko batare da sanin kowa ba sai mahaifiyarta wacce bata boye mata duk abin da ta aikata, sannan tana halarta Masarautu kala-kala tana na
o salon mulkinsu domin wata rana ta shimfida a Tsibirin su da take da burin mulkansa ko da hakan zaizamo ajalinta ne.

A kwana a tashi Lina na nad'o labarai na samun 'yanci sai watsam ta soma
aiwatar da manufarta cikin dibara inda ta kawo sauyi a tafiyar mulkin Tsibiri inda ta soke tsarin hana jama'ar Tsibirin fita lamarin gabansu sai da izini wanda ba dan mahaifin nata ya so ba ya amince rok'onta sai dan manufar da ta gina maganar akai mai amfani ne na abar kowa na fita shan iska duk inda suka so da harkan cinikaiya da kansu saboda ta nan zasu kara wayewa na daga abin da basu sani ba sannan tanan za su iya
arowa Tsibirin sanin da bata da shi ta fannoni da dama.

Ganin ta samu nasara a nan bayan wani lokaci ta sake wargaza wani tsarin inda nanma ta sauya musu shigar sutura ta kawo tsarin 'yan gidan sarauta dole su bambanta da jama'ar da basu da sarauta inda ta ce suna da damar saka suturun da suka so a duk sadda suka ga dama kuma mai tsada da burgewa irin wanda yayi daidai da ra'ayinsu musanman ga 'ya'ya mata ababen ado da kwalliya su kuma jama'ar gari ta ce suna da damar saka sutura masu rufe jiki duk kalan da suka so amma banda irin na gidan Sarauta.

A nan gefen ne tasha wuyar janyo hankalinsa har ya amince da tsarin inda Lima ta yi ta fushi wai Lina na son juya kan mahaifinsu son da keyi mata ya dawo kanta sai da kyar ya iya shawo kanta ta janye ik'irarin sai ta yi ya
i da Lina.

Jama'ar Tsibiri kam sun ji dad'in wannan sauyi dan a take suka soma bata girma sama da wanda suke bawa
Lima dan killace su a wuri
aya yayi mugun takurasu basa da bakin magana ne kawai ya sa dole sukayi biyayya ga abin da iyaye da kakanninsu suka wanzu a cikin shi.

Mrsjmoon ce
Ku daure ku bu
e Arewabooks
*YADDA AKE BU
E ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka
akko ya sauka a kan wayarka.

Za'a cike Form
in kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email
inki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a ta
a *Sign Up* shikenan an bu
e account a ArewaBooks.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a ta
a zata bu
e maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* -
Shine cike form domin bu
e account a ArewaBooks.
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
By Mrsjmoon.

ADABI WRITER'S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.

Page 04.

Sai dai abin da basu sani ba Lina ta yi ya
in k'wato masu 'yanci ne domin kanta saboda gudun kada mahaifinsu ya gano tanayin nisan zango zuwa wani yanki batare da saninsa ba haka tana da burin shiga ta alfarma kamar yarda take ganin a masarautun da take zagayawa da ke birane daban daban sannan tana da burin samo ilimin tsafin da zai bata kariya daga zalinci Lima tare da samun damar shiga fadar da jama'a ke turu-ruwan shiga musaman ranar juma'a suma taga wani kalan bauta sukeyi tare da iya yarensu mai ratsa zuciya. (Masallacin Juma'a da karatun Alqur'ani Lina take magana)
Burinta ya cika inda ta cigaba da fita yawo duk inda taga dama a kuma sadda ta so dan har ta kan kwana a can amma bata wuce kwana
aya zuwa biyu duk tanayin tafiyar ne bisa amincewar Abun tare da neman albarkan Mah.

Lima hankalinta ya tashi sadda ta fahimci yawon da Lina ke fita wani sabon ilimi take samowa wanda nan gaba zai iya zama bara zama a gareta, sai itama ta soma yin nisan zango saidai ita ilimin
zalunci take sake koyowa inda zata dawo tayi ta azabtar da bayi tare da jama'ar gari hakan kuwa na faranta ran Kaka Gunu domin alamomin gadar karagar mulki na ta
ara bayyana a gareta, sai ya
ara mara mata baya tana cigaba da zalintar wanda basu ji ba basu gani ba, har saida Abun ya tsawatar mata tare da nunawa Kaka Gunu illar hakan ya ce a bari ta hau mulkin zaifi wannan kalamin nasa ya fusata Kaka Gunu har ya ce ba wanda ta gaji ruwan tulun albarkansa sai Lima sai Abun ya rokeshi da ya b'oye zancen zai cika masa wannan wasiccin.

A cikin wannan tsakani Kaka Gunu ya mutu, Abun ya tafi dan mallakan Ruwan Tulun da sauran sirrikan tsafi amma ifritan da ke gadin Bukkan suka hana shi da ya matsa sai suka nemi halakashi kan dole ya hak'ura amma yana cike da burin mallakan wannan ruwa na albarka.
Chapter 5 · 0% Book details