← Book details Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 27

Sashe 23

Hatsabibin Tsibiri Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana maganin Infection, asma, limoniya, mura, ciwon basira ciwon kai, ciwon baya, ciwon
afa, ciwon mara, kaikayin jiki dana matse-matsi, yalwatuwar ni'ima tare da samun gamsuwa a turaka da sauransu, muna saida
aya ko sari mai so zai iya tuntubar number nan ta WhatsApp ko kira. 08132166848.

Yarda ake amfani da shi za a jik'a Lipton sai a d'iga man ayu a ciki a shanye da d'umi-d'umi za a iya zuba zuma ko siga a ruwan Lipton d'in dan gudun d'aci haka za a iya zubawa a ruwan Tea a sha.

Masu asma da limoniya kuma zasu jajjaga tafarnuwa su matse ruwan su zuba ruwan d'umi da man ayu su shanye.

Masu Infection duk in suka wanke wurin da ruwan zafi sai su saka man ayu haka masu kaikayin jiki idan sun fito
wanka sai su shafa amma zasu sha da ruwan Lipton, Allah ya
ara mana lafiya Amin.*
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: Hatsabiban Tsibiri
By Mrsjmoon.

Adabi Writer's Association.

"Dan Allah Dr.

Neerah ki taimakeni na sami amincewar yaya Sadauki domin shi ne muradina mahad'an ruhina a bisa igiyar aure."
Sabbin zantukan Zuhrah suka dawo da Neerah hayyacinta, sai da ta saita kanta kafin ta soma magana cike da kamewa "Kiyi hak'uri, Muneerah bata cikin sokayen matan da so ke kaisu aikin zubar da k'ima dan haka kai tsaye bazan iya taimakonki ba, hausawa suka ce iya ruwa fidda kai, tunda kin iya kamuwa da
aunarsa ai banjin tunk'ararsa domin fayyace masa karatun ruhinki zai zamowa abin wahalarwa ba da har sai kin kama
afa da ni saboda tsaban kin rainamin hankali, foolish girl, mitcheww!."
Ta kai
arshen maganar ranta a mugun b'ace tana maijin tamkar zuciyarta zata faso k'irjinta saboda zugi da takeyi maka.

"Hey Malama me ye na b'ata rai har da zagin cin mutunci daga neman alfarma."
"Kanki a jeji sokuwa kawai kuma wallahi kada ki sake tarana da wannan maganar banzan idan kuma kina son ranki ya
aci ne to ki sake jaraba tarana da maganar."
Daga haka tayi gaba, duk da Part dinsu taso tafiya amma sai ta nufi Part din Mami Fulani tama ha
a hanya domin bata ganin gabanta sosai.

Ita kanta mamakin zafin da ta
auka akan maganar Zuhrah takeyi, anan ta sake gasgata
aunar da takeyiwa Sadauki.

Tana shiga suka d'ago suka zuba mata ido da sauri ta sauke kai
asa ta iso gaban Mami ta zauna gefen
afanta ta ri
o hannunta tana sauke numfashi da sauri da sauri.

"Lafiya kike kuwa Muneerah?"
"Mami ina s...

Sai kuma ta fashe da kuka ta mik'e da sauri ta nufi d'akin Lailah, ta fa
a saman gado tana cigaba da rera kuka tamkar wacce akayiwa dukan tsiya domin tanajin idan batayi kukan ba jininta zai iya hawa.

"Babana jimin wani shiri-rita dai."
Shafo sajensa yayi cikin jin rashin da
in ganinta a damuwa, ganin Mami na dakon cewarsa sai ya saita kanshi ya tab'e baki ya ce "Ita ta sani ai, tunda ita ba yarinya ba ce sannan tafi kowa sanin illar jefa kai a damuwa dan haka ki barta har sai ta sakko da kanta tanemi kiji damuwarta amma dan Allah kada ki saka kanki a sokancinta hawan jininki ya motsa."
" A she baka da imani Babana?"
Da sauri ya kalleta ta zabga masa harara zaiyi magana ta d'aga masa hannu "Gara da hakan ya faru na gane waye kai, daga yau Jabir ko Junaid zan soma kira baya goya marayu, Ubannin k'annensu ba kai ba."
"Mami wai me na...

"Sai da safe Babana zan tafi jin damuwar d'iyata yanzu bazan fahimci tatsuniyar nan naka ba."
"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai me nayi da zafi ne haka Mami?"
Tashi ta yi ta barshi da baki bu
e.

Sosa goshinsa yayi cike da mamakin zafin da Mami ta
auka akan abinda bai kai ya kawo ba.

Maimakon ya tashi sai ya gyara zama ya jingina da Cushing d'in da ta tashi sautin kukan Neerah nayi masa amsa amsa kuwa a cikin kunni hakan ya
ara dagula masa lissafi inda ya tashi da sauri ya nufi wurin da zuciyarsa keyi masa jagora, tura k'ofar yayi a hankali idanunsu ya sarke da juna wacce take lafe a kafad'ar Mami na taping bayarta da ido yake tambayarka me ke damunta tura baki tayi tare da lumshe ido, k'ofar ya
an buga saboda ya lura Mami b'ata san da shigowarshi ba dan ta bama k'ofar baya.

"Babana ko maciji ka zama ka shigo a silale kana tunanin ba zan san da isowarka wuri ba ne?"
"Mami affuwan na janye kalamaina."
"Ya wuce Babana amma ga kanwarka nan ka tabbatar da ta sanar da kai abinda ya sakata kuka."
Daga haka ta fice, da ido suka raka bayanta sannan suka kalli juna na seconds, Sadauki ne ya d'age mata hira cikin tambayar kurame na meye damuwarta.

Harara ta cilla mashi tare da hayewa saman gado ta rufe jikinta da bargo har saman kanta.

"Kin hutar da ni yanzu zan tafi in sanar da Mami kishin wanda baisan kina dakon son shi ba kikeyi."
Ai kafin ya rufe baki ta diro daga gadon ta cukumeshi ta baya tare da fashewa da sabon kuka mai sauti wanda ya janyo hankali Mami ta shigo a hanzarce ganinsu haka sai ta nuna Sadauki da yatsa cikin gargad'i batare da ta furta kalma ba.

Murmusawa yayi ya janyo Neerah ta dawo gabanshi ya kalli Mami dake cillo masa harara ya kauda kai tare da cewa "Kiji tsoron Allah Doctor N ki sanarmin da gaskiyan damuwarki in har ba akan kishi ba ne"
Duka ta soma kai masa a k'irji ya kalli Mami ta watso masa dak'uwa tare da barin wurin ganin Neerah bata lura da wucewar Mami ba sai ya saki Murmushi mai sauti tare da janyota ya jefa cikin k'irjinsa ya matse da
arfi dan ji yake tamkar ya tsaga k'irjinsa ya tura ta cikin zuciyarsa.

"Wash! my boobs."
Ta ambata tana mai son kubcewa.

Sassauta ri
on yayi mata ta zame
asa ya bita suka zauna saman rug, ta tura kanta tsakanin cinyoyinta sai lamarin ya bashi dariya, ya kai bakinsa daf da kunninta ya hura mata iska ta zabura ta mike tsaye ya nunata da yatsa nayin dariya mara sauti mai bayyana cikar kamalarshi a fili.

"Yaya Yarima me ye haka?

Allah bana so."
"I love you so much Dr.

N, do you love me?"
Idanu waje take kallonsa ya tsare gira tamkar bai ta
a dariya ba ya sake maimaita tambayeshi cikin dakon jin amsarta, tayi tsit kanta sunkuye tana mi
a godiya ga Allah na jin furucin bakinsa.

"Baki so na saboda na zamo mai sauri saki ko?"
Da sauri ta d'ago ta zuba masa idanunta har lokacin ta kasa furta kalma, girgiza kai yayi cike da damuwa kana ya mik'e da sauri ya fice tare da bugo k'ofar da
arfi.

"Your are stupid Neerah."
Ta ambatawa kanta hakan tare marin fuskanta cike da takaicin barin damar da ta samu ya kufce mata.

"Amma ai kunyarshi naji."
"Kunyar Babana ko saurayin da kike kishi?"
A firgice ta kalli Mami ta gya
a mata kai cikin rashin walwala tare da shigowa d'akin ta kamo hannunta suka fito ta nufi
aya daga cikin d'akunar barcinta.

"Shiga kiyi wanka ki fito mu kawo
arshen maganar munafuncin nan taku."
"Kaina ciwo Mami kuma barci nake ji kuma walalhi bamuyi munafuncin komi ba ki yarda dani Mamina."
"To kwanta zuwa gobe mayi maganar kuma ki tabbatar da gaskiyan ruhinki zaki sanarmin domin ta nan ne zan gane abinda ya kamata inyi akai duk da ba'a son raina lamarin ya zo a haka ba."
Kai ta motsa tana kulle ido sanyin ac na son saukar mata da zazza
i sannan ruhinta cike yake da tambayoyin inda zantukan Mamu Fulani suka dosa na abinda take ambata da ba a son ranta zai faru ba.

Ac Mami ta kashe tare da rage mata hasken wutan dakin ta fice, ajiyar zuciya ta sauke natsuwar ruhi na rab'arta saboda yarda kalaman ina sonki sosai Dr N, shin kina so na?

Ke amsa kuwwan a cikin kunnuwarta, juyi tayi tare da furta "I love you too Yaya Yarima."
Tana rufe baki taji motsin tafiyar wani abu a jikinta daidai saitin zuciyarta ta lalibo da sauri sai ga
atuwar kunama jajur da ita, ta tsira mata ido sai kai da kawo takeyi tsakanin tafin hannunta zuwa tsin-tsiyar hannunta ba tare da tayi mata illar komi ba, murmushi ta yi tare da matseta da
arfi tana jin yarda bugun zuciyarta ya k'aru, ta lumshe ido tana mai furta "Where are you Yaya Yarima?

Dan nasan kana kusa da ni tunda ga kayanka a hannuna."
"Yes I'm here my Doctor."
Da sauri ta kalli bakin k'ofan cikin hasken da bai wadaci d'akin ba, shi ne tsaye yana kallonta fuskansa ba d'igon annuri, murza idanu tayi dan tabbatarwa sai taga wayam ba kowa komawa kwance ta yi ta tsirawa kunaman nan ido da ta koma jikin bango tana ta shawagi sai sanja color takeyi from black to red, yellow, blue, brown and so on dan wani color d'in bata ta
a ganinsa ba tsawon rayuwarta.

Murmushi kawai take binta da shi, har bata san sadda barci ya
auketa ba ta kife ruf da ciki barcin da su Mami ke yak'in ta daina yi saboda rashin alfanunsa ga Bil'adam.

'Na yarda da zancen Bokanki Mamma hak'ik'a ya sanar da ke gaskiya cewa ina da kishiya a kusa da ni, in ko haka ne wallahi sai dai kowa ya rasa Yaya Sadauki domin bazanyi kishi da ke Neerah ba kamar yarda nasan kema bazakiyi da ni ba saboda girman zumuntarmu ya wuce wasa, kai bama zai yiwu hakan ya kasance ba, tabbaas kai nawa ne Yarima Aliyu, ruwa da iska banga mai yimin shamaki da aurenka ba, Neerah wahalar banza kikeyi, ke da Yaya Sadauki sai zumunci na yan uwantaka da Allah ya ha
amu.'
Duk cikin zucci Zuhrah keyin zantukan idanunta na kan sashin Mami Fulani tana auna masa mugun kallo tamkar shi ne Dr.

Neerah.
Chapter 23 · 0% Book details