← Book details Haramtacciyar Soyyaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 39

Sashe 13

Haramtacciyar Soyyaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke kawai nake muradi ke kadai ce burina idan nasameki na gama hada farin cikin rayuwata please Safeena kikawo mana mafita

Bazan iya rayuwa bake ba please ki tausayamin ta mike da sauri don bata da amsar da zata bashi kuma yariko mayafinta bata shiryaba mayafin yafita

Cikin kaduwa da ganin yanda dinkin jikinta yawani kamata ga dukiýar fulanin nan kamar sufito suyi magana Abinda yafara firgitashi tun farkon ganinta da yayi

Cikin jin kunya tafara kokarin kare kirjinta don duk yanda tayi dresing sai komai nata ya bayyana don tanada kirar da ake kira karuwan jiki

Idonshi har ya canja kala tsabar yanda yaga kiran jikinta
Shiyasa dama tasa mayafi mai kauri gudun faruwar hakan don tasan yanda take
Gaba daya Sageer yayi loosing control yafita Ahayyacinshi kafin tayi wani Abu ya fisgota kan kirjinshi yafada kan tree seater da ita cikin zafin nama da rawar jiki......🖊

_baruwana nidai Sageer kar akirani sheda bani awurin atan bayi su Ummu Ammar da ummun jidda sunsan komai_

07062906225
*For cmnt*
[2/19, 2:54 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)

Śtory writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar

💫FAGEN MARUBUTA WRITERS
ASSOCIATION💫

_(gidan zaman lafiya da yarda da juna🤝insha Allah)_

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*Bismillahir rahamanir rahim*

1⃣6⃣
Kafin tayi wani yunkuri ya cafke lips dinta yafara tsotso cikin matsanancin rawar jiki da shauki gaba daya yagama sakar mata da kasala cikin jikinta duk ya motsa lafiyarda ke jikinta

Kafin tayi Aune kawai taji yana kokarin zuge mata zip din riga😳cikin tşoro da tunawa da hakan bai dace ba haramun yake shirin aikatawa ta mike don baida kuzari sam

Cikin wata irin murya yace nooo pretty please don't leav me like this tayi saurin gyara rigarta tana gode ma Allah da baikai ga taba mata kirjiba duk son da yake mosu hmm kafin yadawo hayyacinshi tuni ta fisgi gyalenta tareda key tayi waje da gudu

Shikam Sageer yana faman jinyar kanshi don ta fama mai ciwon da ya dade yana wahalarda shi gashi ko Abinda yafiso baisamu ya dan rage zafi dasu ba

_Kigodema rigarki Safeena yau Hmmmmm_

Ana kiran magrib tashiga cikin gidan tana fakawa tashigé taji dadi bawanda yaga shigowarta harta fâda dakinta tana shiga cikin mutuwar jiki tafada kan sofa tana tunanin moment dinsu da Sageer!

Hmmm Ajiyar zuciya tayi gaskiya Sageer karshe ne ya iya rikita mace yasan takan romance yanzu ji yanda yajefata cikin wani yanayi duk da ba wani Abun kirki yayi mataba only kiss Hmmm

Inaga yawuce hakan? Gaskiya da batayi karfin halin hanashiba idan yacigaba komai zai iya faruwa dón ko yanzu dakyar ta iya kwatar kanta Awurinshi,

Wai dama itama tanada bukatar da namiji har haka? dakyar ta saita kanta sannan tamike tawatsa ruwa kafin tayi Alwala tayi sallar magrib.

Yayi kusan minti talatin yana juyi awurinda tabarshi yakasa tashi yana rike da cikinshi saida kyar yafada bathroom din gidan yasakar ma kanshi shower kafin yadanji natsuwa yayi Alwala sannan yafito duk marar shi ta daure

Ranar bai dawo gidan Auncle nashiba Agidan hutawarshi ya kwana don har zazzabi rufeshi yayi,

Safeena kuwa ta dade batayi bacci ba tana leke ko zataga shigowarshi gidan Amma shiru har bacci ya dauketa ko Abinci bata nema ba adaren

Dasafe tana fitowa ba Abinda take dubawa sai kofar dakinshi Allah yasa ba fushi ya kuma yi da ita ba irin nakwanaki

Har tagama shirya table sannan su Al amen suka fito tareda rungumeta suka hada baki wurin cewa good morning Aunty tace morning guys how are you all? Suka ce fine Tace dats is very good

Kafin Menal ma tafito cikin dabara bayan ta gaisheta tace banga sauran mutanen gidan ba Menal cikin zakuwa tace Aunty Nena nazuwa bari inga dady da Bros tana mikewa Alhajin yashigo

Kawai tawuce dakin Sageer ta fito tareda cewa bros baya gida fa cikin faduwar gaba tafara tùnani kaddai bai dawoba Ajiyan? Yanzu iďan wani abu yasameshifa?

Har kowa ya gama karyawa ya bar table din dakyar ta lalabo natsuwarta ta danyi nata breakfast din sannan ta koma dakinta ta dauki wayarta tana tunanin takirashi ko aa?

Tagwada dialing tana katsewa ba adadi daga karshe dai ta daure ta danna har yashiga tayi saurin katsewa Alokacin har yafita office yaga call dinta saida yayi murmushi

Sannan yayi calling back tana gani tayi saurin dauka kafin mã yace wani Abu tafara cewa ware are you? Ina ka kwana? Meye kake nufi da ķwana awaje? Duk atare tajero mai tanbayar

Cikin jindadin yanda tawani rufeshi da tanbaya yace madam wannan irin țuhuma haka? Kece kikaja na kwana awajen da kintsaya kindawo dani da bazan kwana Acan ba tayaya kike tunanin zan iya dawowa gida?

Bayan kin gudu kinbarni ayanayinda bai dace ba shiyasa na tsaya kawai na nema ma kaina natsuwa gabanta yace wani ras kaddai mace yanema suka kwana ?

Cikin kidima tace bangane ba me kake nufi da hakan? Duk abinda zuciyarki tafada miki hakan nake nufi

Safeena!kinsan ayanayinda kika barni kuwa? Any way ina office sai muntashi zandawo gida anyting for me? Naga andamu da rashin ganina Agidan so zandawo

Kit takashe wayar tareda dafe kirjinta tana jin wani irin mugun sonshi nakara shigarta tana tuna yanda ya birkice mata jiya Hmmm
Amma yanzu ķamar bashiba

Namiji kenan shi baruwanshi da wata aba wai kunya ita gashi tasan duk Abinda sukeyi baidace ba amma yazatayi zuciyarta tafi karfinta gäbadaya takasa sarrafa natsuwarta kamar yanda yace itama yanzu jitakeyi kamar komai dake faruwa daidai ne

Bata ganin HARAMCIN hakan kokadan soyyayarda takeji nashi gaba daya yasauyata

Har gidan yakasance ita kadai kamar kullum sannan tarasa mema zatayi gidan ko ina masu aiki sungyara itama nata dakin ta kimtsashi kawai tasamu kanta da mikewa tashige dakinshi tafara gyarawa duk da ba datti haka ta sauya mai tsarin dakin duka

Ta cire bedshit ta bude sif dinshi tagyara mai ko ina ta canja wani bedshit data ciro a sif ta dakko buner ta turare ko ina kafinta feshe da room fresher dakin nafitarda wani irin kamshi bai kwantarda hankali

Harta gama ta janyo kofar sannan tadawo falon takunna kallo tanayi tana chat awaya zuciyarta na tuhumarta meye tayi haka? Mijintane shi da zata yimai wannan aikin?

_nimadai tanbayata kenan Safeena kin zake dayawa_

Tadauki lokaci Afalon tana kallo kafin daga baya tamike zuwa daki takwanta gaskiya dole tanemi aiki tagaji da musu gadin gida haka bari sudawo dole ma Alhajin ya ýarda tunda Auren baida Amfani

Tana bacci taji karan wayarta tamike kafin ma ta dauka yatsinke kafin taduba kiran yakuma shigowa tana picking taji muryarshi kitashi haka sleeping beauty tayi sauriň kallon dakin don tana mamakin yayasan bacci takeyi?

Kamar yasan tunaninta yace zuciyata tabani hakan don nasan kingaji da gyaran dakika mun tace wane gýarã kuma cikin basarwa yace gyaran dakin Sageer ko bake bace tace ni bansan me kake fadaba kit takatse kiran yabi wayar da kallo kafin yatura mata text

_Kifito kikarasa ladanki kowa yaci Abinci Agidan mukadai ne bamuciba kifito muci Abinci yunwa nakeji nasan kema kinaji_

Tayi saurin duba time taga karfe kusan biyu kenan duk mutanen gidan sundawo kenan ta diro daga kangadonta tafada wanka tayi tareda dauro alwala tafitõ saida tayi sallah kafiņ tayi shafe shafenta tashafa powder da wetlips kawai Amma tayi mugun fitowa takama sumanta atsakiyar kai tayi dougnut dashi sannan tabude sif ta ciro wata doguwar riga baka da ake yayi taji stones gashi rigar tabude daga kasa

Tayane kanta da mayafin rigar tafesa turaruka masû kamshi sannan ta dauki wayařta tafito falon tana zama Alhaji da Sageer nashigowa falon

Dama duk su Aunty na zaune Tamusu sannu da zuwa Aunty tace Yazaman kadaici ? Taçe akwaishi gaskiya har nafara maganar fara aiki nima nagaji da zaman gidan nikadai,

Wani irin kallo Sageer yabita dashi wanda itabata ko ganshiba Alhaji yace badamuwa Zamuyi maganar inna natsu tace nagode ba Abinda Sageer yakeyi sai aikin kallonta dakuma hararar ta yanda take magana da Auncle

Alhajin yayi gyaran murya tareda cema sauran yaran sushiga daga ciki har Menal da Safeena sunmike yace no Safeena ta zauna ita takoma ta zaùna yace zancen Auren Sageer ne sunyi magana da dadynta zasukai gaisuwa gidan su ita yarinyar gobe

Cikin mummunan tashin hankali yace Auncle gobe yayi kusa ,yace no gai suwa ba daurin Aure bane sai sunzauna andaidaita tukun kafin ayi maganar Auren cikin mutuwar jiki yace ok

Safeena kuwa saida takusa fadowa akujerar datake zaune cikin tashin hankali take kallonshi irin kallon am finish tawa takare yana girgiza mata kai Alamar relaxed nõting will happend

Cikin kankanin lokaci duk ta firgice tarasa madafa kawai tamike takomadakinta duk suka bita da kallon mamaki
Meya tashi hankalinta ko sunfadi wani abu badaidai bane yanzu?

Shikadai yasan meyasata cikin yanayin Allah kazama gatanmu yafurta azuciya nace Ameen har suka gama tattaunawa yamike yawuce dakinshi yakasa zaune yakasa tsaye yana tunanin halinda take ciki

Yasan itama tana sonshi suna kaunar juna amma basuda wata mafita ya dauki waya ya danna mata kira bata ko tsayaba ta dauka cikin sanyin murya yace kizo dakina please

Batada wani choice don gaskiya tanason kasancewa dashi tamike cikin sauri tafito duk suntashi Afalon tawuce kai tsaye tana tura kofar yatashi da sauri don yatarota

Cikin kukanda dama shitakeyi tace kadaina tabani nace yace bazan iyaba saidai kiyi hakuri jikina yana hade danaki jinake kamar magnet idan kina kusa dani

Sai inji kamar jikinki nakokarin mannewa danawa koda banshiryaba jikinmu kamar mayen karfe yake indai zamu hadu dole sai mun manne ajikin juna tokima daina hanani taba jikinki

Cikin kuka tace kaida zakayi Aure, yace aini namiji ne konayi Aure inada yancin karawa Amma kinga ke yanzu Akwai Auren wani Akanki bamuda mafita

Ya kikeso inyi Safeena ina Azabtuwa Abubuwan sunyi min yawa cikin sanyin jiki yakarasa kusa da ita tasulale kasa ta tura kanta cikin cinyarta taʼna cigaba da kuka

Yace Safeena kinason kisamin ciwon zuciyane?kinsan yanda nakejin kukanki kuwa acikin zuciyata? Please kiyi shiru haka yaduka tareda dagota yafara goge mata hawaye yana kallon yanda lips dinta suke kyallin man bakinda tashafa

Tareďa bin duk jikinta da kallo yana ganin irín kyawon halittar da Allah yayimata komai nata yaji Hmmm.........🖊

_Kar amaimaita Sageer_
[2/19, 3:08 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYÝAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)
Chapter 13 · 0% Book details