← Book details Haramtacciyar Soyyaya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 39

Sashe 11

Haramtacciyar Soyyaya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daurewa kawai nakeyi amma banda wani choice ne bayan hakan kidaina min zancen wani namiji baby zuciyata zata buga inada mugun kishi musamman Akanki.

Bazan daure ganinki awajenshiba banason ganinki kusa dashi pretty shiyasa na daìna zaman gidan nan Amma kinsan bazan taba daina sonki ba sonki yariga yashiga cikin jini na tundaga ranarda nafara dora idona
Akanki

cikin murmushin tsokana yace ranarda nafara ganin Safeena real dinta ranarda ta hana ni bacci baby kinsan aranar nasan inada sha awar kasan cewa da mace baby look at your structure yana me bin jikinta zuwa kugunta da kallo dasauri tayi baya tareda rufe ido tunawa datayi Aranar daga ita sai towel Sageer yaganta

Dagudu tayi cikin gida tana maijin kunyar Abinda tayi Aranar dakuma yau batareda tasaniba tajitayi karo da mutum cikin hanyarta tashigowa falon cikin firgici ta ja da baya ganin wanda ke tsaye yana kuma binta da wani irin kallon da takasa gane me hakan yake nufi?

_Shin yaganta ne Ajikin Sageer ko yaji Abinda suķe cewa? ........_🖊

*SANNU BATA HANA ZUWA FANS MUJE ZUWA*
[2/19, 2:43 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)

💫FAGEN MARUBUTA WRITERS ASSOCIATION💫

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar

*godiya mara adadi HARAMTACCIYA SOYYAYAR FANS Kunayin yanda yakamata*

_UMMU JIDDAH.. mema zance miki ne kincika masoyiya ta hakika Allah yabar mu tare Yaraya mana JIDDAH_

1⃣4⃣
Duk tarude Abinka da mara gaskiya ya kalleta yace ina zakije haka Safeena kiķe gudu haka?

Hmm Ajiyar zuciya tasauke saboda tagane baigansuba kafin tace wani Abu shima yashigo cikin falon sai takuma tsurewa,

Abinka danamiji sai yawani waske tareda rabewa zai wuce yana cewa sannu Auņcle, yabishi da kallo kafin yace son inason ganinka yanzu,

Yace ok Auncle da sauri ta karasa cikin dakínta tareda dafe kirjinta gudun abinda zai faru kodai Auncle yagansu shiyasa yake kiran Sageer ?

Suna zaune Alhaji mu azzam yakira Aunty Nena Awaya itama tazo duk sun natsu wanda shi Sageer ko Ajikinshi baya shakkar duk Abinda zai faru Ahalin yanzu.

Indai Akan zancenshi da Safeena ne saida Alhaji yace Khadija! tace na am.
Kinsan watan nin baya kafin Sageer yakoma new york nayimai maganar Aure Anan surin ko?

Tace kwarai yaya yace ok zaki tuna meya fadamin Alokacin? Eh yace kayi hakuri har yadawo nija gaba daya. Alhamdulillah yanzu yadawo.

Kuma idan ban mantaba kanada yarinyar da kuke soyyaya da ita cikin tsunkewar zuciya da kuma kaduwa yama kidime yarasa ta cewa.

Saida yakuma cewa inajinka son lokaci yayi da yaka mata ace ka ajiye iyalinkanka yanzu, tsabar rudewã yace ok Auncle zanyi tunani akai kaban kwana biyu ,

Badamuwa amma fa kasani ina nan Akan bakana idan kashirya sai in samu Aminina muje gidan su yarinyar ko ? Cikin dauriya yace na gode Allah yakara daukaka sannan yawuce

Aunty Nena tace yaya kana ganin yarinyar nan yakamata Ahadata da son kuwa? Meyasa kikace hakan ? Saboda naga ita take sónshi ba shike sonta ba

To ke kinganshi da wata yarinyar ne bayan itan? Aa amma yaya anawa tunanin da anbi ahankali ko.

Khadija ku mata lokuta da dama tunaninku sai Ahankali duk cikin maganar da kikayi baki ban wata kwakkwaran hujja ba

Shikanshi da baya sonta zai fàda Amma baice komai ba so kema kiyi shiru kawai, tace shikenan yaya Allah yashige mana gaba Ameen.

Duk wannan maganar da sukeyi Akunnen menal gaba daya hankalinta yatashi bros zai yarda da Auren Humaida?

To ita kuma fa?meyasa dady zai mata haka? Cikin matsanan cin kuka tasan yanzu dadynta zaice tayi karama da Aure Amma ita gaskiya tanason brothern ta

Duk da yanzu tashiga sixteen years amma dayake goyon hutu ce zaka dauķa takai twenty tsabar cikar da takeyi Ayanzu

Ita ta inama zata iya furtawa Sageer wannan zancen tasan ko banza kallonta yakeyi a karamar yarinya bare kuma har ya yarda Ya Aureta

Kuka takeyi irin mai ban tausayin nan gaba daya tarasa wanda zai taimaketa can ta tuna Safeena tamike da sauri zuwa dakinta

Tana kwance tun lokacinda tashigo dakin tana faman tunanin ya akayi ta kasa controling kanta ne wai har tabari yafahimci itama takamu

Hartakaita ga rungumeshi tafara istigifari cikin zuciyarta tana tuna yanayin datashiga lokacinda tafada cikin kirjinshi

Jitąyi kamar anyi mata rahama gabadaya taji kamar batada wata sauran damuwa Arayuwarta Hmm ta sauke Ajiyar zuciya mai sanyì tana cikin hakan

Menal tafado dakin cikin kuka tareda fadawa kan jikinta saida taji tsoro don bataji shigowarta ba cikin kidima tace Menal lafiya?

Meya sameki? Cikin kuka tace Aunty bros zaiyi Aure🙆‍♀ dum kirjin Safeena yabuga da karfi cikin firgici dakuma mugun tsoro tace bangane ba kimin bayani please

Cikin kukan take gaya mata komai Ai tashin hankalinda tashiga na Menal wasa ne kafin kace me itama sai kuka tareda rungume Menal

Kukan da Safeena keyi shiyasa Menal tayi shiru cikin matukar mamaki take kallonta tareda sakin baki tasan dai wannan ba kukan tausayinta take ba,

Gaba daya tamanta da wata Menal tausayin kanta takeji tunda Gwara Menal tana da hope Amma ita fa? Menal zata iya Auren Sageer ko A yau Amma ita fa?matar Aure ce da igiyoyin wani Akanta

Saida Menal ta dafa ta tareda cewa Aunty lafiya ? Sannan ta saita kanta tareda saurin wayin cewa tace natausaya miki ne Menal,

Cikin dauriya tace kiyi hakuri hakan bazai yuwuba ma bazai Aureta ba kinji ki daina kuka cikin mamaki tace Aunty Aini nayi shiru Amma ke mezai saki kuka har haka?

Tace banason ganin kukanki ne shiyasa tace ni ai nayi shiru kema kiyi shiru haka nan tana share mata hawaye _tofa wata sabuwa_

Aranar mutum uku sunkwana cikin damuwa ko barci barawo saida yabar Sageer da Safeena Menal dai ita ta runtsa Abinta tunda Auntyn ta tabata hope

Tunda sassafe yafita Agidan sai gidansu Yusuf shima saida yatsorata don rabonda su hadu tun Asibiti dasuka rabu da fada Akan me zai kira mai Humaida shikuma yace yayi saboda gujê mai fadawa halaka

Kuma koyanzu shiyazuga Auncle Akan zancen Auren Amma bai mai baýani bã kawai yafada mai yana soyyaya dawata baturiya don haka gwara Auncle yamai Aure kila zasu rabu

*Yusuf yabarota*koda yaganshi yasan kwanan zancen amma yamatse yace mai ya akayine Dude naganka da safiyar nan ?

Cikin rudu yace kaji me Auncle yace waifa in Auri Humaida wannan yarinyar yazatayi dani? bangane yazatayi dakaiba? Batada Abinda zai burgeni Ajikin macen da nakeso

Gabadaya bata cikin tsarin matar da nakeson Aura cikin mamaki Yusuf yace to kai meya hana tunfarko ka bude ido kazäba duk matan dake cikin Abujar nan ba wacce tayi maka?

Ai ba dole saika Aureta ba kawai ka bude ido kazabo matar Aure kafita hanyar wannan *HARAMTACCIYAR SOYAYYAR* daka jefa kanka ciki.

Cikin mutuwar jiki yace bazaka ganeba Dude na rasa ta yanda zanyi incireta Azuciyata how? Inason Safeena fiye da kaina Yusuf,

Yace naji what Abaut Menal itama kasani fa tana sonka duk dabata fadaba yanayinta kawai yanuna itafa? Mtsww yayi tsaki wanʼnan jaririyar

Sokakeyi inkashe musu yařinya? So ita Safeenar ce kadai kenan zata iya dakai Sageer ba araina mace duk kankantar ta tana iya daukar nauyin mijinta,

Bazaka taba fahimta taba Yusuf duk wata mace kallon da nakema irinshi nakema sauran mata banga macen da tataba burgeni ba sai safeena i love Safeena oñly

Hmm Yayi Ajiyar zuciya don Abin yafi karfinshi sai shiru har suka rabu bawata mafita da yasamu awurin Yusuf

Karfe goma na ranar da yake Asabar ne ba aiki duk suna gida har yaran Alhajima yana hutawa Adakinshi dàga Aunty Nena Sai Safeena da Menal Afalon yaran na leson

Humaida tashigo cikin yanga tareda sallama tana wani karkada jiki gajikin sai Ahankali ba Abinda yake motsi irin wanda ke haukata oga Sageer

Tana karasowa tasamu gefen Aunty tareda gaisheta Aunty ta amsa cikin sakin fuska tareda tanbayarta muta nen gidan sannan tadan wani juya tace masu Safeena hy duk ba wacce ta ko kuma kallonta

Hartagama fi ilinta ta ce Aunty Sageer yana ciki tace gaskiya bansaniba Am Menak ki duba min brothern ki ko yatashi cikin turo baki tace baya gidan tace banson shashanci banaji dawowarshiba dazu?

Bayanda ta iya haka tamike tashiga dakin yana aikin wato tunani tashigo tareda dauke kai bros Anakiranka kafin ma yace wani Abu tayi waje yabita da kallo yakai minti biyar kafin yafito

Cikin takunshi yana sanyeda amles din riga dakuma treequater duk farare gaba daya yatafi da hankalin mata ukun dake zaune Afalon kowacce na aika mai da nata irin kallon

Amma shi hankalinshi yatafi wurin rabin ranshi bakuwar ma bai gantaba yasamu wuri saitin da zai rika ganinta don gaba daya ganinta da yayi saiyaji duk damuwarshi ta yaye

Saida Humaida ta taso tazauna gab dashi tareda rike mai hannû sannan yaganta cikin kwarkwasa baby naji shiru shiyasa nazo inkara ganin jikinka cikin jin haushinta yace tnks

Itako Safeena Hmm jitake kamar tashaketa yanda ta wani rike mai hannu kamar zata shige jikinshi shikuma harara da kallon Akwai yaki mai zuwa take jefa mai Menal da Aunty tuni sunbar falon

Aunty cewa tayi irin wannan rashin kunya budurwa kibiyo saurayi har gida kuma ki na shigemai? Tom Allah yaraba mu da zamani

Cikin tsananin kishi ta mike tareda shigewa cikin dakinta ta banko kofar yana kallonta harta kule sannan yakalli Humaidan yace Wai yaushe zaki daina zubarwa da kankiAji kina zuwa nan gidan?

Nan fa ba turai bane kigane hakan kuma ni nasan Al adana ok so just go and tank you for d visit cikin rashin kuzari tareda rashin zuciya takeson takuma rikemai hannu ya mike yace muje cikin matse rai

Yata iya dole tawuce yana binta Abaya hartakai wurin motarta yabude mata tashiga duk A idon Safeena tana kallonshi ta window tana fita da motar yashigo cikin gidan

Hango shigowarshi datayi yasata fitowa daga dakin domin wani irin bala in kishin shida yatokare mata kirji jitake inbata tunkareshiba yanzu Akawai matsala.....🖊

*To Allah dai ya kyauta Safeena kishin Sageer*?Hmmm
[2/19, 2:50 PM] Aysher D Yuguda: 🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
*HARAMTACCIYAR SOYYAYA*
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
(romantic love story)

Story writing by
_NAFISA SANI HASSAN_
maman Ammar

FAGEN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION

Gidan zaman lafiya, Aminci had'in kai da yardar juna insha Allah🤝

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*Bismillahir rahamanir rahim*
Chapter 11 · 0% Book details