← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 104

Sashe 88

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Juyawa Arham yayi yaballa mata harara ganin yanda take kuka tadaura hannayenta aka yawuce wanshi wajen kofa inda Waleed yake tsaye walking majestically daidai zaibi ta gefen Waleed yawuce Waleed yawani irin fizgoshi azuciye ya buga kanshi da bango da saida Ilham tai ihu danta zaci kanshi yafashe taga bai fasheba amman ya sume, shakeshi Waleed yayi amugun haukace Waleed ya jashi wani irin dagashi yayi yajefashi abene kaman ya jefa kara Arham ya shiga gangarawa yana tumble har kasa, cikeda wani irin zuciya idanun Waleed sun juya yana wani ihu yace "how dare you sleep with my wife, how dare you! Yauzan kashe ka nahuta Arham, I will kill you" yana karasa sauka yay wani ball da Arham da saida bayanshi ya bugu da kofar falon goshinshi na jini kanshi ya kumbura suntum, kofar falonshi Waleed yabude yaja hannun Arham din baya iya motsi kaman yakarye Waleed na ihu yace "yau saina kashe ka, I will kill you Arham" ihun da Waleed keyi yanajan Arham kiii akasa jini nabin interlock yasa gateman dake kofar gida tareda abokanenshi yadan bude gate kadan ya leko ganin abinda ke faruwa yasa yawani irin zabura tareda buga salati yashigo gidan dagudu abokanshi biyeda shi yayi kan Waleed dahar lokacin jan Arham dat was liveless yake yana kaishi towards wani karfe dake compound din da aka bishi da flower decoration Mai Gadi yace "yallabai meya faru tsakanin ka da aminin ka ai kullum saiyazo nadaika kaike aikoshi saisa bansa ido alamarin ku dan kashaidi nafarko dakamin kenan bayan kabani aiki bakasan sa'ido da gulma aikina nabudema duk wanda yazo gate daganan shikenan kuma kowayasanka da Mr Arham yana ganshi"? Cikin wani irin murya kaman namahaukata yace "kwarto ne, Kwarto ne, da matata yake kwanciya yausaina kwasheshi" "innalillahi wa innailaihi raji'un" dukansu masu gadinan suka dauka daidai Waleed nakase igiyan da aka daure awajen na shanya da hannu bai damu da ciwon ma dayajiba hannunshi na jini ya fizgo igiyan ya daga Arham dabaya iya budema ido bayaji da kyau sabida yanda kunnuwan shi suka bubbugu da bango ya mannashi da karfen yashiga daure shi da igiya duk su mai gadi na kallonshi dan zamasu tayashi cin ubanshi ne, gama daureshi tsirara rass Waleed yayi kaman wanda yasami tabuwan hankali yay generator house dinsu ya kinkimo 25litres gallon dinsu dake cikeda fuel yataho wajen, kafinma yakaraso Mai Gadi yatareshi da sauran abokanan shi yace "yallabai dan darajan Allah a'a ba wanan ba, kagamu zamamu tayaka likimar jakin kwarton, mumishi dan bura'uban duka mu kakkarya shege, amman banda kisa, bazamu taba barinka ka kona mutumin nan daranshi ba wanan irin hukuncin ubangiji kadai keda ikon yinshi badan adam ba yallabai ba'a hukunci da wuta" wani irin kallo Waleed yamai shida abokinshi da saida maigadi yaji cikinshi ya hantsire saiga wata tusa tazomai yace "koku bacemin daga gaba ko wlh nahada daku nakona, wanan yaron, wanan butulun, wanan wanan I don't even know the gaddamn name I will call him with yau sainaga karshen shi I want to set fire on him and watch him scream, beg me and finally burn down to ashes, I want to kill Arham nahuta, I made you this lemme kill him also" yay maganan yawani watsar dasu yay kan Arham, abokin mai gadi ne yace "wlh yallabai dinka baya hayyacinshi, na rantse da Allah baisan ma meyakeyi ba muka bari yay kisan kai harda mu hukuma zata dauka, bama hakaba yajuye ma yaron nan wanan man fetir din hatta shi, da gidan gabaki daya damu duka konewa zamuyi" kaman jira suke yay maganan dukansu su biyar sukai kan Waleed suka kamashi da kyar suka danne amman ina yafi karfin su, ganin haka yasa mai gadi yabarsu dashi yay dakinshi da gudu wayarshi yadauko yafita kofar gida kasancewan yanada number Ammi ya danna mata kira, ringing biyu Ammi tadauka, cikin wata irin muryan tashin hankali yace "Hajiya Ilu ne mai gadin gidan danki, Hajiya kiwa Allah kome kike kibarshi kizo gidan danki yanzun, danki baya hayyacinshi yana kokarin aikata abinda zaiyi nadama, Hajiya kizo kawai" bai tsaya amsa tambayan Ammi ba ya katse wayan yadawo ciki yay kansu inda har lokacin kokawa suke da Waleed suna dambe sosai suna cewa yallabai bazaka kasheahi ba shima ya shiga cikinsu ya danneshi.
Chapter 88 · 0% Book details