← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 104

Sashe 60

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Flat dinshi ya shiga ya maida kofan yarufe bedroom dinshi ya shiga ya zauna akan gado yanzu ne komi yake kara dawomai fresh, kaman zai fashe da kuka yakeji, wani irin ciwo yakeji da bazai iya misiltawa ba, baison yana tunanin Arham ne yay mishi all this abubuwan saiya kawar da tunanin kawai dai yasan yarabu dashi, tashi yayi da kyar ya shiga bayi wanka yayi yafito ya shirya cikin wata Ash color shadda gizna datamai bala'in kyau kaman bashine ke cikin matsala ba, turare ya feshe kanshi dashi sanan yadau dark shade yasaka dan idanunshi sunyi ja, yadau wallet dinshi yafito, bude kofa yayi yafito ahankali yake tafiya haryay wajen da motarshi take a pake ya kwalama Ammi kira da Mom. "Ammi, Mom kufito am outside" yay maganan yana juyawa ya kalli gate jin anyi horn gateman yafito da gudu yana bude gate din, wata brand new ferrari ne yaga ta shigo compound din da baima iya hango na cikin motar glass din motar is tinted, dawani irin gudu mahaukacin motar ta taho harsaida gateman yace "kai" saura kiris motar ta buge Waleed a inda yake tsaye amman ko matsawa baiyiba sabida hakanan ranshi ya fadimai Arham ne, daga kofar akayi Waleed na kallon kofar daga inda yake, kashe motar akayi aka sawo kafa akasa, kafanshi na sanye da wani tomford mai bala'in tsada sanan yafito daga cikin motar, Arham ne yana sanye dawasu hadaddun suit ajikinshi baki idanunshi sanye da bakin glasses yana kallon Waleed yana wani irin murmushi sanan yafara taku daidai yana tahowa gaban Waleed din daya tsareshi da ido yazo har gabanshi ya tsaya yace "call me Mr Arham Abdallah CEO of Arham jikan Malamai orphanage home and home of the disables, Mr Waleed I heard what happen to your orphanage saisa nazo nan, I come to offer you a job agidan marayuna".
[11/1, 11:48 PM] Re@l🖤 K@usy 🔐: 💫💫 _*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_💫 💫

💫 _TWO DIFFERENT WORLD_💫

✍️ M SHAKUR

*This novel na kudi ne, idan kika karanta baki biya ba banyafe ba🤷🏻‍♀️*

_*This novel is 500 Fanmily*❤_
_How to Subscribe to TWO DIFFERENT WORLD_
_zaki turo 500 to account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting DUNIYA BIYU MABANBANTA_

3️⃣8️⃣

Dan murmushi yasake yi yakai hannunshi ya zare bakin glass din kan idanunshi ya kalli Waleed din yace "am willing to offer you a Nani job a boys section dina, idan irin kananun yaran nan dabasu iya magana ba sunyi kashi ko fitsari ajiki saika wanke musu, am ready to pay you 100k monthly for just that Waleed" daidai lokacin Mom da Ammi dasukaci gayu sosai sun fito yar aikin Mom biyedasu takwaso wasu hadaddun kaya dazasu kaima Ilham, hango Arham yasa da sauri Ammi tace "Arham!" juyowa Arham yayi yazuba mata idanu da sauri Ammi tayi wurin Mom biyeda ita tana zuwa ta tsaya kusada Waleed sanan ta kalli Arham din cikin fushi tace "how dare you step into my house with those your filty legs, ubanme kazoyimin agidana" wani irin kallon Ammi yayi sanan ya kalli Mom kafin yatabe baki ya nuna mata Waleed da hannu yace "nazo nabama danki aikin Nani ne idan yanaso agidan marayu na" wani irin sake handbag Ammi tayi akasa ta chakumo rigan Arham tace "how dare you Arham? Kasa an rufemai gidan marayu har kanada gut din shigowa gidan nan eh? How dare you waye kai? Kai dinan waye? Uban waye ubanka waye ya tsaya maka, kasan waye Waleed kuwa? Dan kasa anrufe gidan marayun shi sai me? Bari kaji yanzu haka Waleed nada kudin dazai iya gina gidan marayu dari inyaso, d'ana baida lokacin ka, baka gabanshi yanzu, yabarka har, so I expect you to do dsame stay out of my sons way inba hakaba Arham zan koyamaka hankali wlh" tai maganan tana sakinshi ta tureshi dan murmushi Arham yayi yasa hannu ya kakkabe kwalan shi yace "my expensive suit, anyway is fine" ya kalli Waleed yace "katuna abinda nataba fada maka kwanakin baya Waleed?" wani irin murmushi yayi batare daya kalli Ammi ba yace "nasan ka manta, lemme remind you, Waleed nafadi maka cewa duk abinda kaci sainaci, duk abinda kasaka saina saka" yanuna mai suit din jikinshi dan irin wanda Waleed yake sakawane masu tsada, yace "duk abinda kahau sainahau Waleed" yanuna mai motar sanan yace "duk matakin daka tsaya wlh saina tsaya, meet Arham the newest CEO of orphanage home how does that sound a kunnuwan ku" gate Mom tanuna mihsi tace "munji Arham kayi gidan marayu and muna maka fatan alkhairi the gate is over there kawuce kabar mana gida" girgixa mata kai yayi yace "a'a Hajiya bangama da danku ba tukunna" ya kalli Waleed yace "not all those orphanage student are in my orphanage, kasan kuma wanake cewa nabaka awa uku kasa wanan specific one din dakasan akanta nake magana kasa amaidata gidan marayu na dan ina bukatan ta if not things will get dirty yaro".

"get out butulu kawai, leave my house kafin ka kirga uku matsiyaci dan gidan talakawa," kallon Ammi yayi saikuma ya kyalkyace da dariya yadaga hannu sama cikeda isgilanci yace "I come in peace, you seems angry menene wai? Bari nabar miki gidanki kinsan they can't arrest newest CEO" wajen motarshi yayi ya shiga sanan yasake leko da kanshi ta window mota ya kalli Waleed yace "don't forget my offer and maganan dana maka Waleed I need that girl in my orphanage nabaka 3hrs" yatada motarshi yay reverse yawuce yabar gidan, juyowa Ammi tayi zata rufe Waleed da fada dataga baicema Arham uppan ba Mom ta girgixa mata kai alamun kartayi sanan tace "mutafi Waleed" juyawa kawai yayi yabude gaban motar ya shiga sukuma suka shiga baya suka zauna Waleed yatada motar, Ammi ta shiga masifa tace "wanan irin yaron ne Waleed zai kama danshi ya radamai sunanshi tirrr wlh, tier, I hate Arham with passion my heart is burning with rage, I want to deal with this boy dabazai kara tunanin crossing anylane with my son ba amman kin hanani kina cemin nabarshi da halinshi sabida yaga d'ana karami baida shekaru kamanshi sanan baida fada he is calm shine zai dinga gayamai maganan just look at the gut har gidana zai tako yama d'ana rashin mutunci wlh Arham yaci ganye, yaci ganye sosai, and zai gamu dani" tai kwafa Mom ta shiga bata hakuri, Waleed duk yana jinsu yay kaman baya jinsu at this point ya shafe zancen Arham a ranshi gabaki dayan hankalinshi ya karkata zuwa kan Saheeba, yasan tanachan gidan nan tana musu kuka dan batasan dukansu ba, and maganan da Arham yamai yasan kan itane yamai maganan, and koda zai bada komi daya mallaka ne bazai taba bari Arham ya karbi yarinyar nan ba, sabida yarinyar nan nabukatan kulawa da medication shikuma baidashi dazai bata koma bawanan ba bazai taba bama Arham itaba.
Chapter 60 · 0% Book details