← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 104

Sashe 101

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Abyyyyyyy, Amaaahh" tasake kwalamusu kira da duka muryanta tana kara nitsar da jikinta cikin ruwa ganin namiji agabanta yana kallonta haka, ganin situation dinta yasa yagane she just recall her past, hannu yadaga zai mata magana cikin tattausan murya yace "calm down le......" ihu tamai hawaye na gangarowa daga idanunta tace "man ant? Who are you"? Shiru yayi yama kasa amsata jin clearly larabci tamai bama turenci ba, cikeda tashin hankali tana kalle kallen bayin tace "aina ana? Wa aina walidaiyna? Ina nake ina iyayena suke"? Tasake wurgomai larabci, hannu yadaga mata yace "listen Saheeba I....." da sauri tace "Saheeba? Ismy Widad! Widad bin Othman Benjelloun" anatse yace "alright Calm down Widad, finish bathi....." da sauri batare data bari ya gama maganarshi ba tana kuka sosai tace "khuzni ilaa Waliday, ka kaini wajen iyayena" Allah ne kawai yasa yadan iya larabci dabaisan tayaya zai dinga jintaba gyadamata kai yayi yace "okay I will but stop crying ki gama wanka kufito muj....." dawani irin sauri kaman wacce ta tuna abu tace "Ah.....Ah...Ahmad, aina Habiby Ahmad, zaujy Ahmad" wani irin mummunan faduwa gabanshi yayi yamata wani irin kallo saikawai yatashi dawani irin gudu ta runtse idanunta gamgam ganin namiji agabanta tsirara saida taji yafita daga bayin sanan tabude idanunta ahankali, tashi tayi da sauri daga cikin ruwan tafito wani iri luuu taji tayi ko kadan batada karfi kaman zata fadi da sauri ta dafa bango ta tsaya tana sauke ijiyan zuciya, takai kusan 2min ahaka sanan ta iya mika hannu tazari towel tadaura tafito tana tafiya ahankali ahankali tana kallon ko'ina jikinta har rawa yake, ganin babu kowa adakin yasa tai wajen wardrobe budewa tayi ta shiga nema neman kaya, wani jallabiya datagani na larabawa baki ta zaro ta shirya tsaf cikinshi sanan ta nannada gyalen tasaka takalmanta da sauri bata tsaya neman komiba tai wajen kofa tafito da saurinta kaman zata tashi sama, su Ammi tagani a falo da Waleed daya sanya jeans da t-shirt, tsabagen tashin hankali ko boturan rigan yakasa rufewa sun tsaya charko charko, gani tafito daga bedroom dinsu yasa duk suka bita da kallo, kallo daya tamusu tadauke kai ganin bakaken fata da batasan meya hadata dasuba, hanyar kofar falon tayi da mugun saurinta tana kaiwa tafice ta kwasa da gudu tai Gate, da gudu shima Waleed yabita daidai gate yacinmata riketa yayi ta kwakusa wani irin bala'in ihu tana kwalama Babanta kira. "Abyyyyyyy, Abyyyyyyy, Abyyyyyyy" ta shiga dukan hannun Waleed dake jikinta alamun yasaketa, girgiza mata kai Waleed yayi yace "please Saheeba listen to me dan Allah, is me your Waleed, am not gonna hurt you stop being scared kinji Saheeba" tureshi tayi ta bubbuge hannayenshi looking at his face cikeda tsana irin yanda yake tabata dinan tace "don't touch me, stop touching me, and my name is Widad am not Saheeba, stop calling me Saheeba" tafashe da kuka sosai tana goge fuskarshi da gyalen data nannade cikin harshen larabci tace "menakeyi anan? Meneke yi daku? Is it all part of Umm's plan, I want to see my father and my grandmother" ganin yanda take kuka and Waleed is not in anyway helping the matters yasa Ammi ta tako wajen har kusada ita hannun Widad din takama tarike ahankali tace "Widad I know you understand English so I want you to listen to me please daughter" tsaigaita kukanta tayi tana kallon Ammi, ahankali Ammi tace "muje ciki mu zauna saimunyi magana ba anan gaban gateba" girgizama Ammi kai tayi tace "ni wajen Aby zani" tasake fashewa da kuka sosai, tausayinta Ammi taji tama kasa magana tadaga kai takalli Waleed da idanunshi harsunyi jajir yana kallonta hankalin shi tashe, tausayi shima yabata sosai duk abinnan tai tunani lokacin daya kawomata zancen zai aureta, da ace tahanashi da yanzu yana ganin bakinta yace tahanashi auren wanda yakeso hakama auren farkonshi tahadashi da wanda bayaso saisa ta barshi, ijiyan zuciya ta sauke tace "listen Widad, nasan bakisan muba amman one thing I can assure you is that I can never hurt you so now kizo muje daki kifada mana koke wacece sanan daga ina kike sanan muzo musan yanda zamuyi mu maidake wajen iyayenki dan munsan suma suna nemanki sabida kinfi shekara daya damu a Nigeria, muje ciki" ganin yanda yarinyar take dar dar dasu yasa takai hannunta tarike mata hannu sukai hanyar babban falo, zaunar da ita kan kujera Ammi tayi sanan kowa ya zauna, anatse Ammi tace "now I need you to calm down kidena kukan nan, we are ready to help you zamu kaiki wajen iyayenki" anatse itama Widad takai hannu ta share hawayenta tace "where is this place, how do I end up in Nigeria?" anatse Ammi ta nuna mata Waleed dake kallonta har lokacin idanunshi sunyi ja, kallo daya tamai tadauke kanta da sauri danta ganeshi shine wanda tagani abayi dazu tareda ita tsirara, ahankali Ammi tace "that's my son, Dr Waleed Warbai, yanada babban orphanage a Zaria, acikin wani jirgi aka kawoki garin nan aka jefar dake a ruwa, a ruwa aka tsinkeci aka kaiki gidan marayun d'ana dan yanada Big orphanage, he took you in sabida yanda kanki ke bleeding saida yamiki aiki akai, at first wasu irin behaviour kike abnormal ones sabida fluid din dake cikin kanki sai daga baya kuma kikazo kika dena har akai auren......" girgiza matakai Waleed yayi alamun karta fadi mata tsallake wajen Ammi tai nandai tabata labarin komi dayasa meta tas tas harda abinda yasa Waleed bai bada sanarwanta ba sabida karyazo koma waye yaso kasheta yadawo ya kasheta, kasa dena kuka tayi ahankali Ammi tace "kinsan waye keson kasheki, me kika tuna last na past life dinki"? Cikin wani irin muryan kuka tace "abinda natuna?" gyadamata kai Ammi tayi, shiru tayi kaman mai tunani sanan tace "ranan aurena da Ahmad komi yafaru" ba Waleed kadaiba kowa nadakin saida gabanshi ya Yanke yafadi, tacigaba. "Allah kadai yasan wani hali mijina yake ciki, kunce nayi morethan a year tareda ku anan, omg Ahmad, Aby da Amah must be super worried" tai maganan ahankali tana fashewa dawani irin kuka, Ammi bata hanata ba dan itama yanzu kukan takeso tama danta jin Widad nada miji wanan wani irin tashin hankali ne, takai kusan 5min tana kuka sanan tai shiru tace "sunana Widad Bint Othman Benjelloun, ni haifaffiyar yar Morroco ce, iyayena komi nawa daga chan ne, ina karatun mass com a Egypt ina shekarata na biyu agarin nema na iya wanan yaren nasaran dakukaji ina muku magana dashi, Mahaifiyata tarasu" taidan shiru tareda share hawayen dasuka zubomata sanan tace "cancer yakasheta, ni kadai mahaifina ya haifa step Mom dina Umm bata sona, ranan aurena bansan maiya faruba nadai farka naganni cikin wani jirgin awani daji......." nan tabasu duka labarin abinda yafaru sanan tace "yanzu I need to see Aby ku kaini wajenshi I need to tell him abinda Umm tamin karshima ta kasheshi sabida Umm is just after dukiyan Aby, please ku kaini gida yanzu" shiru Ammi tayisanan tanisa tace "Widad muba yan kasar morroco bane, koda yanzu zamuje garin dole muyi yan shirye shiryen takardun shiga kasar, bankuma son ki kira mahaifinki matarnan zata iyaji tayi wani mummunan abu in taji kina raye, gwara muje abazata saidai kawai ta ganmu, yanzu kiyi hakuri kibamu nanda kwana biyu zuwa uku muyi yan takardu sanan saimu dunguma mu maidake gidanku kinji" ahankali tace "to mijina fa shina kirashi Ahmad can keep secret inaso hankalinshi ya kwanta" wani irin tari Waleed ya shigayi da sauri Ammi ta tashi dagakan kujeran daga ita harsu Mom sukai kanshi, tari yake sosai Ammi batasan lokacin data saki salati ba. "Innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, kai Waleed sha ruwa" aka kai ruwan da Abdul yadauko bakinshi amman kaman bashi ake bamawa ba sumewa kayi yayi warwas ya sandare awajen, haukane kawai Ammi batayiba da sauri Mom tarike Ammi tace "Adda ki kwantar da hankalinki dan Allah" cikin wani irin yanayi na kaman wacce ta zare Ammi tace "wlh in Waleed yarasa yarinyar nan mutuwa zaiyi mutuwa zaiyi" kallon Abdul Mom tayi tace "daukeshi mukai mota" ta kalli Ammi tace "ke ki zauna da ita kinsan itamaba lfy gareta ba, ki kira Babanshi(Uncle) yazo asan me ake ciki, Asma'u zauna dasu kema" gyadamata kai tayi suka dauki Waleed itada Abdul sukafitada shi sai mota Widad na binsu da kallo tana zaune inda take dan ba gane hausar dasukeyi takeba, zama Ammi tayi ta kalli Asma'u tace "kawomin wayata Ma'u" wayar Ma'u takawo tabama Ammi kira daya Uncle yadauka Ammi ta shiga sanar dashi abinda ke faruwa, shi yamafi Ammi rudewa da sauri yace kwantar da hankalin ki gani nan zuwa, am leaving office yanzun nan duk jirgin danasamu binshi zanyi ya katse wayan ya tashi xumbur.

Itama Widad din zazzabi ne yarufeta tadinga amai da kyar Ammi da Asma'u suka samu bacci ya Kwasheta bayan tasha magungunan ta, Mom takirasu tacema Ammi jikin Waleed da sauki dukdan hankalinta ya kwanta nanko har lokacin bai farfado ba.
Chapter 101 · 0% Book details