← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 104

Sashe 46

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan nisawa yayi yace "I will always love my lawyer, kinsan ciki babu hormone din dabaya tabawa ajiki, to harda na brain dinki yake tabawa saisa kike ganin abu ba'a yanda yakeba, akwai inda very Important zan lallasheki inna dawo" ya shige bayi yafara wanka, yana cikin wanka taji anbude gate, dawani irin sauri ta zabura ta tashi ta yaye labulen dakin Waleed taga motar yayarta Anty Hussaina ya danno cikin gidan, gefenta kanwar Maman su ne dasuke kira da Yakolo, sai back seat dabata gane wayeba tadai tabbatar Anty Hassana ce, salati ta buga. "Innalillahi wa innailaihi raji'un" da sauri tai wajen bayin ta bubbuga tace "Arham please kafito da sauri kasaka kaya su Anties dina sunzo" da sauri Arham yadauraye jikinshi yafito daure da towel, kayanshi Ilham ta tattara ta mika mishi daidai yayinta na kwarara sallama a falo, Anty Husai tace "karkuyi mamaki tanachan sama tana bacci abunku damai ciki kumuje saman mutadota" da sauri Yakolo tace "nifa banison shirme in mijinta na nanfa" "miji, ai mijinta Anty Yakolo tun safe yake tafiya aiki, daman tun bayan jere baki kara ganin gidaba kumuje sama" sukai stairs rawa jikin Ilham yadauka tace "na shiga uku na lalace, nabani Arham mezanyi yanzu sunzo sama" daidai lokacin yakarasa saka riganshi yace "calm down I will handle it" yay wardrobe din Waleed yabude wani jallabiyan Waleed yadauko yamika mata dan tsirara take yace "saka wanan kiga" sakawa tayi ya agurguje ya saukan mata har kasa sanan murya chan kasa yace "calm down" ijiyan zuciya tasauke ahankali sanan yashiga kalle kalle adakin, wani file din Waleed yagani akan side drawer dinshi yadauka da sauri yay hanyar kofa yace "muje" bude kofa sukayi daidai su Anty Hussaina sun hayo saman turus dukansu sukayi suna kallon Arham da Ilham dasuka fito daga dakin yay kaman bai gansu ba yace "mijinki ya isheni da aike, kidinga dubawa kina tabbatar da baiyi mantuwa kafin yatafi ba" dan dariya tayi tace "ai baby sai......" daidai ta juyo tahada ido dasu Anty Hussaina wani irin tsalle ta daka da ihu tai wurinsu. "oyoyo Anty Yakolo" tafada jikin kanwar Maman su datai turus tana kallonta, ganin haka yasa yataho shima ahankali yace "sannunku da zuwa" sanan yawuce yaraba ta gefensu yasauka kasa abinshi boldly and majestically yabude kofan falo yafice, yana fita Anty Yakolo ta fizge ta daga jikinta tace "dan ubanki wanan wani kato ne yafito daga dakin mijinki, sabida ke dakikiya mahaukaciya ce jibi gashinki bako dan kwali ya hargitse kaman na mahaukaciya, dan ubanki waye shi?" kaman zatai kuka tajuya ta kalli Anty Husai, Anty Husai ranta abace tace "badake ake magana ba, dakina Amarya ma haka mukazo gidan muka ganshi, kifada mana uban meyake kawo shi nan gidan, tuntuni muna sallama ba amsa" kaman zata fashe da kuka tace "me kuka nufi da wanan irin tambayan dakuke min? Wani tunani ne aranku? Sabida kun ganni busu busu ahaka? Nima tashina daga bacci kenan, shine ma yatadani daga bacci Waleed ya aikoshi ya daukomai wani abu adakin, shine fa nabude mai dakin ya dauka, banmasan kaina ba dankwali ba" tafashe da kuka sosai dayasa dukansu jikinsu yay sanyi, Anty Yakolo ne ta katse shirun tace "nidai tashi bar kukan ba kyau me ciki na kuka, je dauko dan kwali kisaka, kukuma mu koma kasa kawai" juyawa sukayi itakuma ta tashi tana kuka kaman gaske ta shige dakinta har lokacin gabanta faduwa yake tana godema Allah datasha da kyar.
[11/1, 11:47 PM] Re@l🖤 K@usy 🔐: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫

✍️ M SHAKUR

2️⃣8️⃣

FREE PAGE
Direba ne yace "Waleed kikeson gani Hajiya"? Gyadamai kai tayi hakan yasa yarike ma Ammi hannu yar aikin ma tarike ta suka dagata da kyar ta iya tsayuwa a feet dinta, mai gadi yacema yar aikin. "kawo mata mayafinta da jaka da takalmi" da gudu yar aikin tai sama dakinta ta shiga tadauko mata hadadden mayafinta da takalmin ta da jaka ta sauko kasa yafama Ammi mayafin tayi akan tsadadden lace din dake jikinta sanan tasa takalmin, ta karbi jakan dan tasoma dawowa daidai sukai waje da ita motar ta direba yabude ta shiga baya ta zauna suka rufe ta sanan ya shiga gaba yatada motar gateman yabude gate suka fice, suna ficewa motar Mom na sawo kai tabi motar Ammi da kallo daya wuceta da gudu yar aikin tafita waje taje wajen motar Mom cikeda girmamawa tace "sannu da zuwa Mom, Mom please jibi Hajiya, ankirata awaya bansan me aka fadi mataba amman saida ta sume kuma yayyafa mata ruwa ta farfado tace a kaita wajen Waleed agidan marayu yanzu sun tafi, please kibata I don't want wani abu ya saman mini Hajiya" cikeda tashi hankali Mom tace "karki damu bari na bita" kwana tayi da sauri tabi bayan Ammi itama.

Motar Ammi na zuwa gate kasancewan security sun santa suka fara ihu. "Hajiya Don come Hajiya Don come, open the gate" sukahau jin dadi dan bata cika zuwa gidan marayun ba but duk randa zatazo ruwan kudi take musu, dan yake ta musu ta saka hannunta cikin jakan da yar aikinta tabata rapas din yan dubu sababbi ta dauko guda biyu ta mikama babban su, ihu sukahau yi suna mata godiya direba yaja motar ciki, kafin su rufe gate saiga second Mom, dadi kaman yau ana baki itama kyautan tamusu mai tsoka sanan ta shiga ciki, har gaban office din Waleed inda yake parking motarshi direba yay parking, tsabagen yanda jikin Ammi ke rawa kasa bude kofan tayi saida direba yafito yabude mata tasa kafafunta tafito tana fitowa motar Mom na sawo kai wajen, parking tayo tafito da sauri tai wajen yayanta data tsaya chak tana kallonta tace "Adda meya faru?" kasa magana Ammi tayi tajuya kawai Mom biyeda ita, itama Mom ganin yanda mutane suka taru a tsakar wajen yasa taji gabanta yafara faduwa, ana ganinsu aka fara gaishe dasu. "Barka da zuwa Hajiya, barka da zuwa Hajiya" kasa amsa kowa sukayi Ammi tai gaban asibitin daidai Mama Iyami dake kuka sosai tafito tawani irin zube agaban Ammi tace "Hajiya ku shiga yana ciki, wayyo Allah na mun shiga uku, gatanmu na kwance a asibiti raga raga, rai na hannun Allah" tsallaketa Ammi tayi tasa hannu tabude kofan ta shiga ciki Mom biyeda ita, Nurses din data gani charko charko tsaye agaban reception din tawani irin dakama tsawa. "kuna kallo na bazaku gayamin inda d'ana yakeba" arude duka nurses din suka mata pointing dakin da aka rubuta emergency asama, yanda Ammi ke ihu yasa Mom takama mata kafadar Ammi alamun tai calming down, kabar da hannunta Ammi tayi tai hanyar dakin, tana zuwa batai watawataba tabude kofan tasa kanta ciki, Dr Kemi da Dr Ayo ne akan Waleed din dahar lokacin bai farfado ba, ancire mai riga da singlet, dagashi sai dogon wandon jikinshi da belt anmai dauri akafada ta wajen hammata an hade da hannunshi kaman wanda ya karye, fuskarshi tai jajajir, gefen idon damanshi dama idanun duk sun kumbura, gefen bakinshi ya tsage yanadan jini tsabagen marin dayasha na Arham, wuyan shi tsabagen matsan da riga da necktie din wuyanshi sukamai har ciwo suka jinmai jini nafita wuyan yay jajir kaman an zaneshi da bulalan inji.

Hawaye ne suka cika idanun Ammi takasa rikesu suka shiga zubowa har zafin dukan takeji ajikinta tsabagen tashin hankali, tunda ta haifi danta incident makamancin hakama baitaba samun dantaba, daidai Dr Ayo yagama gyara jinin wuyan yajuyo ganin Maman Waleed yanda jikinta ke rawa tana kuka yasa yace "calm down ma, bawani abu babba bane kashin kafadarshi tadan goce ta sanadiyan buga bayanshi da akayi da bango, saikuma bruises din wuyan nan dakuma na ido, dan jini yataru acikin idanunshi but with time zai washe, calm down Hajiya, nan da dan anjima kadan danki zai farfado" da sauri Dr Kemi data karaso wurinsu itama ta gyada kai tace "yes ma calm down please Ma" sukabi ta gefensu suka fita daga dakin, wani irin juyowa Ammi tayi cikeda wutan bala'i, da kunan rai da tsantsan bakin ciki ta kalli Mom sanan tanuna mata Waleed dake kwance kan gado da hannu tace "kinga abinda Arham yama d'ana ko? Kinga abinda Arham yama d'ana ko, kina gani daiko, yaron da dama kece tun day one kikai approving friendship dinshi da yaron, left to me yarona ya rayu ahaka baida aboki I his mother can be his best friend and his everthing aman kika nace saina barsu sunyi abota, dan haka karma naji kinhanani dauka hukunci dan wlh wlh bazan yarda ba" tai maganan tana dauko wayanta daga cikin jaka da sauri Mom tace "Adda kinga calm down yanda kike tafarfasan nan bai kamata kidau hukunci ba, dan Allah kiyakuri Adda" da wayan hannunta tanuna Mom tace "Zainab ki shiga taitayin ki, na rantse miki da Allah yanda Arham ya jima d'ana rauni ko kwana baza'ai ba shima sai anjimai, wlh saiyasan ya buganmini d'a, shidan ubanshi ubanwa yataba dukanshi haka? Waleed dakoni bantaba daga hannu na daka bane wani kato zai dokanmin wlh wlh saina ramamai, wlh kuwa kinji na rantse miki" Ammi tai maganan tana bude kofa tafita daga dakin tana dailing number Maman Arham.

Ringing daya Mama tai picking call din ganin kira daga Ammin Waleed, kafin ma Ammi tai magana cikeda fara'a tace "Assalamu Alaykum, barka da yamma Hajiya" ko amsa sallamarta Ammi batayi ba cikeda bacin rai tace " please kome kikeyi kibarshi kisamemu a orphanage na Waleed yanzun nan kizo, ina jiranki yanzun nan" tana kaiwa nan ta katse wayan jikinta na vibrating, Mom ma takasa cewa komi tazama yar kallo matsalan yayarta kenan intai fushi batada hankali, kuma bataji bata gani barin ma when it comes to Waleed matter.

Gaban Mama ne ya yanke lokaci guda ya fadi, tunda tasan Ammi tsawon shekaru kenan bata taba tamata irin wanan kiran ba saiyau, tomeya faru? Allah yasa alkhairi ne, ahankali tafara karanto innalillahi wa innailaihi raji'un kota samu natsuwa cikin zuciyarta, dan batada natsuwa ko kadan sabida zuciyarta wani irin mummunan faduwa kawai yake.
Chapter 46 · 0% Book details