← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 104

Sashe 53

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Duk suna zaune adakin Dr ta shigo ta duba Ilham sanan tabasu sallama tawuce tafita, ahankali Mummy tace "aminiya natafi da ita gida tai jego ne?" ada Ammi tai alkawari bazata je jegon gidaba amman sai kawai taji gwara sun tafi, gyama Mummy kai tayi tace "eh kuwuce kuma a kulamin da matan d'a da jika da kyau, suna arba'in zanzo na kwashi abuna wlh" duk akai dariya Mummy tace "nina nafi kowa sanin bala'in ki ai bazanyi wasa ba yallabiya" tai maganan tana kallon kofa ganin anbude Baba ne da Waleed da idanunshi sukai jajir da sauri Mom tai wajen Waleed din tace "sannu Dan Yaro an gyara" gyadamata kai yayi, Baba yace "bama karaya bace ashe gocewar kashi ne yanzu an gyara an shafamai magani, Allah yabashi lpy" ahankali Mom tace "angode Alhaji" Mummy tace "Allah baka lpy" itadai Ammi tai kaman bataji su ba, Mummy ne tace "Alhaji an sallamemu mutafi dasu gida, agida zatai jego" da sauri Baba yace "to bari nakai kayan mota" daukan kaya yashiga yi Waleed yaje zai tayashi da sauri Baba yace "kaga jeka zauna kaida hannu ba lafiya ne zakadau abu jeka huta" yay maganan yana fita, ganin haka yasa Mom ta shiga tayashi suka kwashe komi sukakai mota, sanan Waleed yadau hijab yabama Ilham tasaka ahankali yace "test me all that you need zan aiko miki dashi" murmushi tayi ya gyadamai kai ganin yana wani ji da ita kodan ta haifamai d'a ne, kofa yabude mata tafita suka jera atare tana tafiya ahankali har motar Baba ta shiga ta zauna sanan ya matsa ganin Ammi tazo baby ta shiga ta bama Mummy sanan suka rufe musu motar suka tafi Ammi tajuya tai motar ta ta shige direba yajata banda Waleed daya tsaya chak awajen, ahankali Mom tace "mutafi" daga kafa yayi yawuce ya shiga motar ta suka tafi, gida sukaje yana fitowa flat dinshi yaje kwanciya kawai yayi, yaciro wayarshi number Arham yakira amman harta gama ringing bai dauka ba, 3 miss calls yamai ganin bai dauka ba yasa yamai message.

_"Hey blood, I called no answer I guess you are still angry with me, I called nafada maka Khadija ta haihu, an sami baby boy, yaron yay kama dakai sosai blood, and do you know what's even} great? Yaci sunanka, sunanshi Arham Waleed Warbai, blood you mean alot to me, u make my life colourful, I am sorry idan maganan dana maka jiya kajita somehow I was just trying to know what you've been up to lately, and I am also sorry akan abinda Ammi na tamaka please forgive us, take care, anjima zan shigo_"

Yaturamai sakon tareda lumshe ido bacci na saceshi kafin baccin yay nasaran daukeshi.
[11/1, 11:48 PM] Re@l🖤 K@usy 🔐: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫

💫💫_*DUNIYA BIYU MABANBANTA*_💫 💫

✍️ M SHAKUR

3️⃣2️⃣ & 3️⃣3️⃣

END OF FREE PAGE
Wuraren karfe biyun rana ya farka, sosai yaji karfin jikinshi kawai gajiya yakeji bawani abuba, tashi yayi dagakan gadon yaje gaban madubi ya tsaya ya kalli kwayar idanunshi na dama ganin har yanzu akwai jini aciki yasa yabar gaban madubin yana tunanin inya fita anjima zai tsaya a pharmacy yasai maganin dazai saka jinin idanun ya washe, bathroom ya shiga, wanka yayi yasake yin brush sanan yafito, wardrobe dinshi yaje yadauko wasu native, farin yadi ne mai taushi da akamai jumper yasaka sanan yadau turare yafeshe kanshi dashi, dadduma yahau yay sallan azahar sanan ya zira takalmi bayan yadauki wallet dinshi yafito, side din Ammi yayi gabanshi nafaduwa, ahankali yabude kofar ya shiga hada ido yayi da Ammi dake zaune kan dogon kujera hannunta rikeda remote ko taji zai shigo ajikinta ne oho dayasa take kallon kofar oho, suna hada ido ta ijiye remote din ta tashi daga kan kujeran da sauri ya shigo dakin yamaida kofan yarufe yace "Ammi, Ammi please wait" sama Ammi tayi da sauri yabita kafin yakai harta shige dakinta tarufe da key dan bamata son ya shigo, tsayawa jikin kofar yayi yay shiru, yakai kusan 5min ahaka sanan yace "Ammi please listen to me, kiyakuri kinji please Ammi na" yay maganan ahankali yana knocking kofarta yakai kusan 10min ahaka awurn ganin bamata da niyyan bude kofan yasa yawuce ya sauka kasa, dinning yaje yazauna sabida shegen yunwa yakeji, warmer yabubbude, tuwon shinkafa yagani da vegetable soup, zubawa yayi baima wani iyaci da yawaba yasha ruwa yamike tsaye key motar Ammi dake kan centre table yadauka yawuce yafita, motar ta ya shiga ya zauna sanan yaciro wayarshi ganin har lokacin Arham baimai reply din message dinshi ba yasa yatada motar direba yabude mai yawuce yafita daga gidan.
Chapter 53 · 0% Book details