← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 104

Sashe 24

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

FREE PAGE
*_NIGERIA_* 🇳🇬
Wani irin juyawa jirgin yayi kafin kace me jirgin yabace a hazo, kwashe yaran aka shigayi ana lodasu a mota yayinda wajen yacika security personnel da some marine forces dake wajen, wasu mutane guda uku ne sukayo wajen Waleed na tsaye inda yake suka shiga cikin ruwan kaman sune search force, sun duba ruwan basuga komiba saidai suka dawo tareda coffin din, Arham ne yakaraso inda Waleed yake tsaye bayan ya tabbatar da staff dinsu suntafi da yaran yace "meya faru just now blood? Jirgin sama right above our head? That's strange, bantaba ganin hakaba sanan ya jefar da akwatin gawa a ruwa is that even okay no wa.... " hannun da Waleed yadagamai yasa yay shiru ya kalli inda Waleed ke kallo da sauri, mutane biyun ne suka fito daga ruwan rikeda akwatin dayake abude suka ijiye bakin ruwan sanan suka fito da sauri Waleed yay wurin Arham biye dashi, tsayawa chak sukayi suna kallon akwatin da jini yabata sosai garuwa ciki, dayan dake cire kayan ruwan da yasaka ne kafin ya shiga cikin ruwan yace "I don't understand, jirgi kawai yazo yajefo mana akwatin gawa lafiyan su kalau ko bazugani da kyau sun zaci nan bolane" da sauri dayan yace "ni nama zaci gawa aka yardan mana ashema akwatin ce kawai, to Allah dai ya kyauta amman wanan abu haka, we will report to the police ashigar da karan susan inda zasu jefar da waste dinsu jibi yanda suka daga ma bakinmu hankal....." shiru yayi ganin Waleed ya tsugunna yanabin jikin akwatin da kallo yana shafa akwatin da hannu kaman maiso yagano wani abu, kafin idanunshi su sauka kan dan kunne kwaya daya dayake makale acikin hole din shan iskan nan da akayi kaman ramin yatokare dankunen dayakeda fadi dan dankunne yama ramin kadan abinda yanashi fita kenan da ruwa shima yay sweeping nashi away, ahankali Waleed yasa yatsanshi yaciro dankunen yamike tsaye yana kallo daya daga cikinsu yace "wow dan kunnen mai kyau halan yayimoshi yayi a ruwan, muje Bala mutafi da akwatin" daukan akwatin sukayi harzasu tafi da sauri Waleed yace "are you sure kunduba ruwan nan da kyau babu kowa ciki?" "yallabai babu inda bamu dubaba ai indai wanan rafin dakake ganine babu wani lungu da sako dabamu saniba cikinshi, bayau muka fara ceto rayukan mutane acikinshi ba" gyadamausu kai kawai yayi suka wuce suna zance, Waleed yajuya yana kallon ruwan da sauri Arham yace "don't tell me u want to go in da kanka" juyowa Waleed yayi ya kalleshi yace "of course yes, ga dankunne nagani a box din" da sauri Arham yace "this is river Waleed, ruwa ne, the coffin can pick the ear ring anyway aruwan, kagama wuce mutafi dan wlh kana kara making attempt din shiga ruwan nan zan danna ma Ammi kira" wani mugun kallo Waleed yamai yace "toka kira munafuki" yana maganan yafada ruwan da sauri Arham yace "Waleed" gabanshi nafaduwa yana kallon ruwan da Waleed ya nitse ciki, arude Arham yace "Waleed wai me haka sai wani abu yasameka acikin ruwan nan eh? Come out please" kusan 10min Waleed yadauka cikin ruwan sanan yafito ahankali, Arham yace "kagani kaima bakaga komin ba, kafi wayance iya aikinsu ne kawai kaje ka jika kayanka a banza" ballamai harara Waleed yayi yay gaba abinshi Waleed ya bishi da sauri yanadan dariya yace "wlh kacika rigiman banza, kawai daga ganin dan kunne shikenan" Waleed baice mai komiba har sukaje children section din, zai shiga ciki saikuma ya kalli Arham yace "lemme go and get Khadija and change" gyadamai kai Arham yayi Waleed yawuce.
Knocking yayi tareda bude dakin yashiga, daidai lokacin Ilham tafito daga bayi tana sanye da hadadden jeans din daya kawomata as gift jiya da crop top din da hakanan yadauko let's just say he's use to seeing ladies yan gayu dress in them so practically he wants to see his wife dress like that, tana ganinshi ta taho da gudu zata fada jikinshi ta rungumeshi yakoma baya yace "am wet baki gani" binshi tayi da kallo cikeda mamaki zatamai tambaya yawuce bayi, fitowa yayi daure da towel yazo ya chanza kaya, tajowa wajenshi tayi da sauri saikuma tarike waist tamai wani irin juyi tace "bakace nayi kyauba, nayi kyau?" dan murmushi yayi kawai yakarasa bakin gado ya zauna bayan ya chanza kayan yace "is nice" wani irin blushing tayi ta taho da gudu ta zauna kan laps dinshi sanan ta manna mai kiss a lips dinshi tace "thank you" gyadamata kai yayi kawai sukia shiru, ganin yamata shiru yasa tace "Dr jirgin na landing awajen nanne dazu naji karan jirgi kaman akaina" ahankali yace "it just came and yakuma juya" gyadamai kai tayi tana kallon yanda yake maganan yace "get dress let's go out" cikeda wani irin murna ta dagashi wardrobe taje da sauri taciro gyale mai kyau dazai shiga da jeans din sanan takoma gaban mirror ta yaryada uban kwalliya tasa jan baki sanan ta yafa gyalen awuya tajuyo ta kallai yana danna waya tace "na shirya" dagokai yayi ya kalleta dauke kai yayi yace "change into something native" wani iri taji taso sufita ahaka ko Arham yaga shape dinta da kyau saikuma ta share tai gaban wardrobe din dakin wata pink atampa taciro da aka mata riga da skirt ta shirya tsaf ciki kayan sun mugun kamata suranta yafito sosai, tayafa gyalen daya shiga da kayan tasaka flat shoe sanan tazo gabanshi tace "Baby let's go" dagokai yayi ya kalleta sai kawai yamike tsaye yamaida wayan aljihu yay gaba, bude mata kofa yayi tafito sanan shima yafito yamaida kofan yafita, ahankali suke tafiya har zuwa children section atare suka shiga wajen, da Arham tafara hada ido da sauri ta dauke kai kujera yabata tazauna yace "am coming" gaishe da ita staff dinshi suka shigayi tana ansansu ayangance shikuma yawuce inda Arham yake yace "am taking her out blood she has been indoors tunda mukazo" batare da Arham yakalleshi ba yace "saikun dawo" juyawa Waleed yayi yaje wajen ta suka fice inda bodyguard dinshi ke tukasu, cikin Bauchi suka shiga shi bai wani surutu da ita amman kome takeso tana fadi zai siyamata daga bayama supermarket yakaita yasami waje ya zauna tadauki duk abinda takeso sai dadi takeji sanan suka dawo mota, da magrib sukaje wani eatry bayan ya tsaya sunyi salla a masallaci, sosai ranan taji dadi tasamu sunyi pics sosai dashi komi yasai mata saitai snapping asamu na nunama friends a status sai wajajen 10 nadare suka dawo, baje tsaraban ta tayi a kasan dakinsu tana dubawa tana snapping shikuma yatabe fuska ya shiga bathroom abinshi wanka yayi yazo ya shirya cikin pj yakoma kan gado yabude system dinshi yana aiki, harya gama yay bacci yabarta tana daddanna waya ana saka status ana amsa comment din kawaye.
***
Chapter 24 · 0% Book details