← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 104

Sashe 36

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Shigowa tayi rikeda tray mai kyau da flask ke kai da plate da serving spoon da cup dakuma juice da ruwa, tun kafin takaraso gaban falon Mama kebinta da kallo sabida taga kotai shirme ganin takawo komi daidai kaman yanda ta koyanata yasa ta sauke ijiyan zuciya, karasowa gaban Waleed yayi daya saukar da kanshi kasa dariya na neman kwasheshi shiba yarinyar kebashi dariya ba Arham kebashi dariya danhar yafara hango bura'uban da Arham zeyi idan Mama tagabatar mai da maganan, harta ijiye ta juya takoma ciki baima saniba sai maganan Mama yaji tace "ya kaganta fisabilillahi Waleed batayi ba"? Gyadama Mama kai yayi yakai kololuwa wajen damke dariyan shi amman saida yar murmushi ta subuce mai yace "tayi Mama" washe baki Mama tayi tace "Allah sarki Waleed wlh kai dan Albarka ne, yaro maijin maganan iyayenshi, jibi fa kai Ammi ka tacemin tana gabatar maka da zancen auren kai na'am inama ace haka dan uwan naka Arham yake, amman ina Arham baida wanan kawaicin" dan shiru tayi tana kallonshi sosai take farin cikin ganinshi ko Allah yasan tanajin Waleed har ranta sosai, ajiyan zuciya ta sauke tace "Waleed daman inaso nakawo maka karan dan uwanka" shidai kanshi nakasa baice komiba tace "kasan menene dan Albarka abokin ka baya kyautamin, tunda yay tafiyan nan bai kirani ba sai jiya, kasan bani iya fito da sunanshi awayan nan daka siyamin, amman ai shi yanada number ta, saida nafita na shiga nan gidan makotan nawa na nemo danta Aliyu inma karike maka zance har jiran Aliyun nayi yadawo daga gantalinshi dan kawai na ganshi na bashi wayan nace yanemo min Arham shinefa yaciro number yakira nasamu nai magana dashi, wai ina mishi korafin bayi wani kirani shine yahau cewa waini nacika fada abu kadan fada kome yayi fada, wai naje naga yanda akema ba'a maka fada kome zakayi agidan ku" ta karashe maganan ahankali alamun kalman yamata ciwo, bata cika kawomai karan Arham ba amman tunda yaga wanan karan takawo mai karan abun yay mata ciwone, ahankali yadago kanshi ya kalleta yace "Mama kiyakuri, ba lallai yanda kikadau zancen haka yake nufiba, kinsan aiki yake sosai achan ko hayaniyan yara zai iyasa yaji baya hayyacinshi, kimai uzuri aiba haka yakeba...." da sauri tace "wlh haka yake, kai bazaka gane Arham bane, nasan abokin kane ka tsani kaji laifinshi wanan halinka ne tun kana yaro amman saina fada saidai ku hadakai kuita fushi dani, kaga wanan Arham din dakake gani" tai maganan tana karkada kafafu tace "Waleed bawai banda godiyan Allah ba, kokuma inafa takura ba wlh Waleed bancin kudin Arham, nasan inada komi kamin komi Waleed amman wani zubin kowace uwa zataso ko biyar ne danta yadauka yabata yace ungo Mama asamana albarka, Waleed kaine chefanena duk wata, kaine motata kudin man da ake xubamin ciki, kaine magunguna na sanan kaine mai bani kudin kashewa tun kana dan kankanin ka kakemin wanan hidiman har gobe, bawai korafi nakema ba kokuma naga gazawar ka a'a yakamata ayanzu Arham kemin irin abubuwan nan sabida yagama makaranta yanada aikin yi, amman bayi komi, haryakai ga nace Arham ban kaza saida yace ai Waleed yayi miki kaza kokuma kinada kudi Waleed yabaki, kaga ai badadi" hakanan Waleed yaji baiji dadin abinda Arham yayi ba anatse yace "kiyakuri Mama zai gyara in sha Allah" tabe baki tayi tace "Allah yasa ci abincin ka na tsareka da surutu dan Albarka" spoon yadauka ahankali yashiga cin dambun yaci sosai dan yakusan cinye plate din sanan yature, sosai sukasha hira da Mama dudda kusan rabinta karan Arham take kawomai, sai wuraren la'asar yabar gidan, wani eye clinic yaje kai tsaye yafadi irin glasses din dayake so a keramai akamai yabiya kudi ya shiga mota yakoma orphanage.
[11/1, 11:47 PM] Re@l🖤 K@usy 🔐: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫

✍️ M SHAKUR

1️⃣9️⃣ & 2️⃣0️⃣
Chapter 36 · 0% Book details