← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 104

Sashe 22

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Wuraren 11 aka gama shiryata tsaf cikin lebsa r'batia blue(sunan kayan), yanada mugun kyau kayan dogon rigan ne daya amsheta, kalan blue da fari, kunnenta yaji hadaddun yan kunnaye hannayenta da warwarori na zinare, farin gyalen amare Amah ta dauramata kan saman gashinta da aka gyara tsaf sanan tajuyo tamata kiss cikeda so tace "zauna anan dan Amarya bata fitowa akafa, bari naje chan tsakar gida wajen su babanki, yanzun nan neggafa asisitance zasuzo afitar dake, I love you" murmushi tasakin ma Amah tace "jazakillah Amah" gyadamata kai Amah tayi tana dogara sandarta tafita, babu kowa aciki kowa na waje dan nanne ake bikin, duk yan ciki sun fita sabida Aby na raba kyauta.

Tana zaune shiru adaki tana kallon kanta a madubi ganin kyawun datayi yay yawa sai kewan Aby take sabida tun safe bataga Aby ba gashi aka'ida Amarya bata gani iyayen ta sai an fitar da ita acikin (amaria) a kaita wajen daurin auren dan Amarya bata tafiya da kafanta, tana cikin yan tunane tunane ta akai knocking kofar dakinsu faduwa taji gabanta yayi da sauri tajuyo tareda bada izinin shigowa wani ma'aikacin gidansu ne ya shigo yana sanye cikin wani uniform blue da purple, cikeda girmamawa yace "ga amaria ne abakin kofa anbamu izini mufito dake baya, Aby nason magana dake kafin mukaiki wajen daurin auren, motarshi na wajen" murmushi tayi tace "Aby" gyadamata kai yayi yace "bismillahi" mikewa tayi ahankali cikin blue embroidered dress din lebsa r'batia tasake kallon kanta amadubi sanan ahankali tafara tafiya, bude mata kofa ma'aikacin yayi tafita anan taga maza guda shida, dama a adaltance maza bakwai da ake kirada negaffa assistance ke daukan Amarya bayan ta shiga cikin amaria su daura hannayen abin akan kafadarsu sukaita chan wajen daurin auren, bude mata kofan sukayi ta tsugunna ahankali tashiga ciki ta zauna tare da tattare kasan gown dinta, cike da girmamawa yace "kin zauna da kyau? Are you comfortable?" gyadamai kai tayi tace "Alhamdulillah thank you" maida kofar yayi yarufe sanan yasauke labulen daya rufe kofan tabaya da akama ado ta yanda babu wanda zai iya hango amarya, daukan kafafuwan sukayi suka dagata sama suka daura akan kafadunsu instead of suyi tsakar gida sai sukai kitchen da ita, bude kofan bayan kitchen din sukayi suka fice babu kowa ata wurin, sanan suka cigaba da tafiya sukai gate din dake ta wurin bude gatedin sukayi suka fita, babu kowa ta wajen sabida daman Babanta yasai filin wajen babuma mutane sai wata katuwar bakar mota dake wajen, karasawa sukayi har gaban motan sanan suka sauketa, suka bude tafito ahankali, kallon wajen tayi sanan ta kalli daya daga cikin motar mahaifinta data gani awurin a pake murmushi tayi tace "Aby na ciki?" gyadamata kai sukayi, ahankali tasa hannunta tabude bayan motan daba kowa zata shiga taji saukan wani abu kaman tsumma a bakinta da hancinta within 3 good secs dip kanta yadauke, da sauri suka rirrike ta suka shigada ita cikin motan sanan wanda yazo yakirata yama direban da fuskarshi ke sanye da mask magana "yi sauri kutafi, yanzu mu zamuje daukota adaki as scheduled kumuje yara" da gudu suka dauki amaria suka tafi shikuma direban yaja motan dawani fitinannen gudu yabar anguwan.
Wanan kenan!!!
Chapter 22 · 0% Book details