← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 104

Sashe 61

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Horn yayi agaban gidansu Ilham mai gadinsu yafito yabude musu suka shiga ciki, yarane atsakar gidan sunata wasa saiga Mummy tafito tana murmushi tana musu sannu tazuwa tace "oyoyo oyoyo" parking Waleed yayi su Ammi suka sauko daga motar sukai wajen ta, sanan Waleed ma yafito yabi bayansu, cikeda girmamawa dakuma kunya yace "ina yini Mummy" "ina yini Waleed, sannunku da zuwa ku shigo dan Allah kunga yara duk sun cika gidan wlh yaran yan biyu ne, sunyi tafiya suna dubai fa bama suga baby ba har yanzu, amman yau mukesa ran zasu dawo in sha Allahu" Mom ce tace "Allah yadawo dasu lpy" hadadden falon su suka shiga Waleed yasami kujera ya zauna su Ammi zasu zauna Mummy tace "kawa bazamu bar yara su zanta ba, muje sama, Waleed bari aturo ta" tai maganan tana kwalama Ilham kira. "Ilham, Ilham kifito ga mijinki" wani daki Mummy tabude musu suka shiga, basu dade da zama ba saiga Ilham ta shigo tana sanye cikin wata atampa riga da zani, tai wani irin kiba nonon ta sun ciko sunyi suntum sabida shayarwa, tai duhu sosai kaman ba itaba sabida zafin ruwan zafin jego, har kasa ta tsugunna agaban Ammi da Mom tace "sannunku da zuwa Ammi ina yini" kanta Ammi ta shafa tace "daughter na sannu kinji ya jego? Nonon ki naciwo ne" gyadama Ammi kai tayi tace "eh yanamin barin ma inzaisha nono" cikeda tausayawa Ammi tace "kije yana falo ki fadamai inyaso yasamo miki abinda zakisha sannu kinji" gyadama Ammi kai tayi ta kalli Mom tace "ina yini Mom sannu da zuwa" "sannu Ilham ya jego kinji yanda mukeji ko yanzu damuka haifoku" dariya Mummy tayi tace "ai ingaya muku yaron nan inyafara kuka itama farawa takeyi kullum bamu baccin dare, kai jikan Kawata badai kuka ba" tai maganan cikeda zolaya, Ammi tace "inkin gajine bani kayana na tattara natafi dasu mufa ba'a mana wulakanci" dariya duk sukayi adakin, Ammi tasake kallonta ganin tana inda take tace "jeki gaida mijinki" tashi tayi Mummy tace "ko dauko yaron nan daga bacci kikaimai" gyadamata kai tayi tafita, dakinta ta shiga ta dauko Arham karami tarikeshi a hannu sanan ta sauka kasa tundaga sama Waleed kebinta da kallo harta karaso gabanshi tana murmushi ta zauna kusadashi ahankali tace "Baby oyoyo, sai yau zakazo kaganni nai fushi" dan murmushi yamata yasa hannunshi ya karbi danshi yarike ahannu yace "sorry I've been busy" sanan yazuba ma yaron ido yana kallonshi yaron dako sunanshi ba'a yiba amman yay kato yay kyau sosai sai kallon yanda yaron yag kamada Arham yake, yanda taga yana kallon yaron saida gabanta yafadi akullum gani take kaman dazaran ya kalli yaron zai gane dan Arham ne, ganin kallon dayake mishi yasa tace "Baby kakosan Arham ko zuwa duba takwaran shi baiyiba, ko kiranmu ma awaya baiyiba wlh baby abin yaban mamaki" murmushi yayi yakai Arham kafadarshi dayake son yafara ihu danhar yatashi yace "zaizo he's busy" ahankali yace "yimin list din abubuwan dakuke bukata na suna" murmushi tayi cikedajin dadi tace "Baby ni nafison kaban kudin zan aika ayomin siyayyan" gyadamata kai yayi yace "nawa kike so"? Wani irin dadi taji danso take tahada kudaden data samu da wanda zai bata tabama Arham tamai transfer halan zaisa yafara daukan wayanta dan gabaki daya bai daukan wayanta bai mata reply na message gashi batada halin fita tana jego saisa har Allah Allah take tai arba'in, ahankali kaman wata marainiya tace "5m ma zai isa" gyada mata kai yayi yace "ok zan miki transfer to your account anjima" rungume shi tayi tace "thank you Baby na Allah barmu tare" haka suka zauna afalon sukai shiru sai kallonshi take dan yamata kyau yan kwana biyun nan dabata ganshi ba gani take kaman tai shekara bata ganshi ba saitaga ya kara kyau, ga Arham ko kadan yaki kuka ajikinshi da normal ne yaron nan natashi zaisha nono ya koshi fa saiya fara uban kuka harsai yayi bacci amman yanzu yana jikin Waleed dakemai wasa yay shiru, cikin zuciyanta tace "danda bama nakaba jibi yanda yay bonding dakai I wonder yanda yaranka zasuyi bonding dakai" hannunshi takama ahankali tadaura kan boobs dinta tana kallon fuskarshi tace "ciwo yakemin Dr" sauke hannunshi yayi da sauri yana kallon boobs din yace "zan aiko miki da magani, sorry" yay maganan ahankali, gyadamai kai tayi yajuya yacigaba da wasa da Arham itakuma na kusadashi tana kallonshi, suna zaune ahaka har su Ammi suka fito, tashi duk sukayi aka shiga sallama sanan suka rakosu har mota, Waleed yabude booth yakira mai gadi suka shiga shigar da kayan dasuka kawo musu ciki sanan suka shiga mota suka musu sallama suka tafi, suna fita motar daya dauko su Anty Hassu suka shigo gidan, da sauri Ilham tafara murna tace "oyoyo yan dubai Anty hope kunyomin tsaraba" fitowa sukayi daga motar rungume su Ilham tayi sanan aka dunguma akai cikin gida, duk bajewa sukayi afalo da yaransu Mummy takawo musu Arham karami, Anty Hassu ce tafara karban yaron hadiye murmushin datake yi tayi ganin yaron gabaki daya sai tunanin ta yakoma kan fuskar Arham dasuka tabagani agidan har sau biyu, kaman Arham da yaron harya baci, dan murmushi ta kakalo tayi tamika ma Anty Hussai yaron, karbanshi tayi ta shiga murna dan ita mutum ce da batada lura haka, itakuma Hassu a kawai lura gata da kaf kaf da abu banbancin su kenan, sakewa Anty Hassu tayi gudun kar Ilham ta zargi wani abu suka cigaba da hira har magrib sanan aka tashi dan aje ai salla Mummy tabama Ilham yaron, tace "kije ki kwantar dashi ki zauna tareda shi mangariba tayi Ilham zama kake kusada yaran ka ka natsar dasu" karbanshi Ilham tayi tana murmushi dan dadi sosai takeji tana expecting kudi tai sama, bude dakinta tayi ta shiga tana shiga kafin ma ta kwantar da Arham aka bude kofa aka shigo dakin da sauri tajuyo Anty Hassu ce, maida kofar tayi ta rufe sanan tasaka sakata, tashi tsaye Ilham tayi rikeda Arham dake bacci akafadar ta tace "Anty Hassu" karasowa Anty Hassu tayi tamika hannu tace "bani shi na kwantar miki dashi" karbanshi Anty Hassu tayi sanan ta kwantar dashi ahankali cikin gadonshi ta gyaramai net sanan tajuyo ta zauna abakin gadon takamo hannun Ilham ta zauanr da ita tace "zauna nazo muyi magana ne saisa ma na kulle kofa dan banso aji maganan mu" zama ahankali Ilham tayi tana kallonta, hannayenta Anty Hassu takama tarike tace "Ilham, agidan nan bayan yayyin mu maza guda biyu, saini da Husai, sai wata data rasu kafin ke, saisu Farida, Ilham kinga kome zai faru we are family and we will always be, sanan babu wanda zai rufa maka asiri aduniyan nan kaman dan uwanka najini, kingani nan niba yarinya bace ke kanki kinada shekaru 26 sanan akwai wata data girmeki data basu kafin mu kinsan ko mun kwana biyu, kalleni da kyau Ilham niba yarinya bace, sanan duk gidan nan a duka yaran da Baba yahaifa shi kanshi Baba yafadi bai taba ganin d'a mai fikra da lura da abu cikin dukanmu kamani ni ba, ko rashin lafiya ake agidan nan kafin a fada ina ganin mara lafiyan nasan baida lafiya, so Ilham bansan kwana kwana, sabida inason na taimaka mikine tun kafin lokaci yakure miki" Anty Hassu tai maganan babu wasa tattare da ita sanan ta tsare Ilham din da idanun rass batako kyaftasu sanan ta nuna mata Arham dake cikin gadonshi da yatsa tace "dan chan yaron waye? Na mijinki ne kona abokin mijinki"? Wani irin faduwa gaban Ilham yayi da ita kanta Anty Hassu saida taga faduwar gabanta.

Kasa magana tayi saiji datayi bakinta ya bushe sosai ta shiga lashe lips dinta, Anty Hassu tace "bayan wanan bazan sake miki tambayan nan ba, yaron nan dan wayeshi na mijinki ne kona abokin mijinki"? Kasa magana still Ilham tayi tabude bakin ma komi takasa fitowa, gyadakai Anty Hassu tayi tace "yayi miki kyau Ilham, magana daya tal zan gayamiki, kwana chassain da tara na barawo ne kwana dayane tal na maishi, kibi duniya asannu sanan kidinga sara kina kallon bakin gatari dan karyazo daga baya yadauki wuyanki, bari naje nai salla" Anty Hassu tamike kaman ba ita tai maganan ba tai kofa tasa hannu tabude sakatar tabude kofan tafita daga dakin, dawani irin sauri Ilham ta tashi tai gadon Arham karami, yaye net din tayida sauri sanan ta kalli fuskarshi muryanta na rawa cikeda tashin hankali tace "wai daman ana gane kaiba dan Waleed bane? Tokodai Waleed yagane shiru kawai yamin yana kallona? Innalillahi wa innailaihi raji'un, ya Allah karufamin asiri"
[11/1, 11:48 PM] Re@l🖤 K@usy 🔐: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_💫

✍️ M SHAKUR

3️⃣9️⃣

_duk wacce bata karanta DUNIYA BIYU MABANBANTA ba ansha dake, littafi ne da dan Nigeria 🇳🇬 Bahaushe yahadu da balarabiyan kasan Morocco🇲🇦, a Two Different world ne zakuji asalin bayanin miye tsantsan cin amana da hassada, wat are you waiting for? Biya kiji abinda wayanda suka biya keji, kika karanta kuma na Allah ya isa kin kaskantar da kanki_

_I don't like much surutu please, M Shakur bansan littafin Allah ya isa bane, yanzu dai kinji nakudi ne_
How to subscribe
_Pay 500 into my account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461_

Hawayen daya zubomatane ta share tana sharce majina sanan tadau wayarta dagakan gadon daidai alert na shigowa tabude da sauri instead of 5m data tambayay saitaga alert na 7m wani irin dadi taji ya lullubeta da sauri tai dailing number Arham amman harya gama ringing bai da gaba, takirashi yafi sau goma still bai dagaba cillar da wayan tayi cikin fushi tafashe da kuka, ace ta haihu yau yaro kwanan shi biyar amman har yanzu baizo ya duba dandan shiba, tamai text, tamai text, takirashi, takirashi harta gaji amman bai daukaba, baimayi acknowledging anyone of them ba, to wai yanzu baya sonta ne kome? Ina sonta dayace yake mata yake eh? Yanzu when she need Arham the most suhadu su kula da dansu yanzu ne zai juyamata baya baima damu da itaba, wlh tai nadaman budema Arham kafa harya shigeta yamata ciki ta haifan mishi d'a.
Chapter 61 · 0% Book details