← Book details Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 104

Sashe 103

Duniya Biyu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anatse yafara magana yace "Widad me and you have come a very very long way, tunba yauba kinsha fadi cewa no one understands you better than I do, kinsha fadi da bakinki cewan kafinma ki furta abu nakan fahimci abinda kikeso kafinma kifadi kintuna"? yaymaganan yana murmushi, gyadamai kai tayi ahankali, dan ajiyan zuciya yasauke yace "na zauna nai tunani mai tsawo, sanan na azumimci ranaku uku duk akanki ina rokon Allah should guide me to the right path which I believe shine abinda yayi dahar yasa nasami courage nazoma da iyayenki da maganan nan kafin ma nazo miki nan da ita" yasakeyin shiru sanan yace "after all this long journey Widad I come to understand wanan mugun son danake miki ba kowace irin so bace face so so kaman irin na wa da kanwarshi, I care about you Widad, I go for anything that will make you happy, bayan kin bace haukacewa ne kawai banyiba babu inda bamusa hoton ki ba, but for once in my life Widad nai tunani ba akaina dakanki kadai ba, for the first time in my life nai tunani akaina, akanki dakuma akan abinda kike dauke dashi acikin cikin ki" yasake yin shiru sanan yace "Widad da ace ni dinan dakike gani ba'a gidan mahaifina nataso ba bazan tabayin farin cikin dazanji irinshi agidan asalin mahaifina ba, kowani d'a dakika gani aduniyan nan burinshi shine yataso cikin so dakuma gatan iyayenshi, daga lokacin da mace ta dauki juna biyu a lokacin ne zata dena tunanin kanta kanta ita kadai, alokacin ne zatafara tunanin what's best for her and her child, our parents sacrifice alot for us, mata nawane ke zama da mazajan da basuso badan komiba saidan kawai yayansu ballema wanan da deep down kinasan ubanshi Widad, u just needs to find where wanan son uban nashi yake azuciyanki, kwanakin baya danazo naganku tare I saw how u looked at his father and I see nothing but pure love in your eyes" yay maganan ahankali kaman abin namai ciwo, yakai kusan 5min yay shiru sanan ya nisa yacigaba. "just to be sure nasamu natsuwa cewan kina hannun wayanda zasu kula dake yasa I made a research akan family mijinki nagano wayesu, your husband is a goodman a humanitarian, an activist, a Dr and many many more , yesterday I had a one on one chat da mijinki Widad I must admit cewa yaron nan na sonki and trust me idan nace TWO DIFFERENT WORLD means shit inhar Love din is real, komi dakika gani mukaddari ne da ace guy dinan ba mijinki bane da babu abinda zai kaiki Nigeria da bamu da yan uwa ko guda achan, kowani musulmi dolene yay imani da Allah dakuma rana ta karshe, sanan ya yarda da kaddara, koma meyafaru tsakanina dake kaddara ne, take me as your brother wanda kuma ya isa dake Widad ayau ina gayamiki cewa nida kaina without anyone forced me that na janye duk wata kalman soyayya dana taba fada miki ada, na janyeta nahakura, nadauke ki amatsayin sister na, and inhar kin daukeni amatsayin yayanki wanda yakuma isa dake abu daya zangaya miki shine kibi mijinki sauda kafa domin ko yana sonki sosai, go and build your marital home, go and build your family Widad I wish you all the best in this life kinji" yay murmushi yana hana kanshi kuka ganin yanda take kuka sosai, ahankali yace "tashi muje tun dazu Aby yakira family mijinki duk suna falo kibisu kutafi, sunce Qatar zaku koma bayan kungama vacation saiku koma Nigeria ko, don't cry let's go" bude kofa yayi yafita da ita, a falo tagansu duka sai kallonta suke banda Waleed da kanshi ke kasa yanada mugun kishi saisa baimason yadaura idanunshi akanta da Ahmad dasuke fitowa tare, tana zuwa tafada jikin Aby tana kuka sosai, hadasu Aby yayi yamusu wa'axi sosai mai ratsa jiki, sanan agaban kowa ya kwaso paper's na kamfamonin shi yasa tai signing dudda za'a dinga yimata managing, hana kowa tafiya Aby yayi yace sai yahada musu gagaruman liyafa wanda za'ayi gobe sanan zasubar garin, dakanshi yakaisu wani hadadden bangare agidan itakuma Amah ta tafi da Widad shashinta tun dare takira masu gyara, ranan yan aiki basuyi barci ba aka shiga decorating.

Da safe wuraren 9, designers Aby yatura side din su Ammi, aka dauki measurement din kowa sanan aka kawoma kowannensu Morrocan dress, wuraren 11 aka fara ceremony din, aka fitoda Widad da Waleed yakasa daina kallonta, dauke kai tayi daga kallonshi ita adole fushi take dashi ta ballamai harara sanan tashiga cikin masu rawan larabawa, Waleed was blown away dayaga tana rawa, subhanallah bura'uba baitaba ganin yarinyar data iya rawa irinta ba, she looks so happy adorable and charming suna hada ido zata ballamai harara, haka har wuraren 4 Aby yasa aka shirya musu tsaraba dan Uncle yasanar dasu cewa jirginsu 6 ne, Aby da Amah har Airport suka rakasu, aiko Widad tasha kuka kafin tarabu dasu.

Nigeria

Asibiti
Case din Arham saida akai documenting nashi ababbban littafin da'ake recording incidence na bura, kwanan shi bakwai chur aka sallame shi daga asibitin bayan yayi clearing duka bill din dayacimai kudi sosai, bai wani damuba tunda yasamu andike fess yana iya fitsari, gabaki daya, adaidaita yatare for the first time tun bayan yaje gaisuwan Mama bayan tarasu saiyau kawai yaji yanaso yaje gidan mahaifiyar shi, keke yatare ya shiga yana tafiya yana dingishi har zuwa gidan, gani yayi an kulle gate din da makulli baida key hakan yasa yadau dutse ya balle key din ya shiga cikin gidan yana kallon ko'ina ga motar Mama da Waleed yasaimata apake a kasan tent, ahankali yake tafiya har zuwa gaban flat dinsu balla key shima yayi sanan yabude kofar, chak ya tsaya abakin kofa yana kallon falon yaga kanan zaiga Mama akan kujeran dayake yawan dawowa daga aiki yaganta, ahankali ya shiga cikin dakin zama yayi akan kujeran dayay kura sosai baima damuba yana kallon kujeran da Mama kezama kai yana ganin kaman ita ya kegani zaune tana kallonshi, yakai kusan 5min ahaka saiga hawaye ahankali ya zilalo mai murya chan kasa yace "Mama dan Allah kiyafemin, nasan sabida kin rasu da fushina a zuciyan ki saisa komi yafara juyamin up side down" shiru yayi yasa hannu ya share hawayen da suka zubomai murya chan kasa yace "Mama wani yakusan yankemin gaba, Mama Alhakin kine kona Waleed suke bina"? Ya tambayi kanshi kafin ahankali yace "Mama I feel so empty, na kwacema Waleed gidan marayun shi, yanzu haka baida gidan marayu, na kwacemai mata ta haifamin yaro ba mijinta ba yanzu tana dauke dana biyu, Mama inada katon gidan marayu, inada mota lambo kaman ta Waleed Tawa baka, Mama inada yara kananu masu danyen jini harsu takwas danake amfani dasu dukdan nafi Waleed jin dadin duniya suma sunada yet Mama am still not full am not satisfy, nothing seems to satisfy me, Mama pl......" bai karasa magana yaji anyi knocking kofar falon tareda shigowa duka at a spot, polisawa yagani guda biyar hade da government officials, babban cikinsu ne dake sanye da suit yay murmushi yace "good Day Mr Arham, yau kwana uku kenan muna nemanka aduk inda mukasan zamu sameka but bamu sameka ba sai yanzun nan informant din damuka ijiye awanan anguwan suka sanar damu sunga shigowanka anguwan ka shiga gida" wani irin gyada musu kai yayi gabanshi nafaduwa, mutumin yace "office dinka yakama da wuta an nemeka an rasa har saida aka turamu, anan muka tarar da gidan marayun ka yaran damuka aminta dakai muka kaisu gidanka sun wulakanta, basuda abincin ci yara duk ciwo suke, bayan series of tests muka gano mata takwas nada ciki, nan muka turkesu for investigation anan suka sanar damu komi tundaga abu nafarko daka fara sakasu suka maka na yima Mr Waleed Warbai shairi har muka kulle gidan marayunshi, kabiyasu kudi kasai musu kaya akan suma Waleed shairi cewan yamusu fyade, sabida kaga yarane basuda gata saikai kai amfani da kansu da maraicin su kace ka auresu a masallacin gidan marayu da babu wanda yabamu shaidan abu makamancin daurin aure yataba faruwa akan hakan on that note Mr Arham, you are hereby being arrested for rape and assault, dakuma shairi har kasa aka kulle gidan marayun Waleed, banda haka duk wani property dayake naka zamuyi auction nashi ayi amfani da kudin abiya yaran dakaci amanan su sanan acigaba da lurada su dakuma cikin dasuke dauke dashi, you have the right kai shiru inba hakaba kome kafadi za'ayi amfani dashi akanka at the court of law" yana gama maganan daya daga cikin polisawan yay kanshi ya shiga samai ankwa juyawa Arham yayi ya kalli kujeran dayake ganin Mama zaune akai kaman wanda yazare yace "nasan duk aikin kine daman abinda yasa kika jawoni nazo gidan dan akamani ko, na tsaneki, Allah ya isa tsakanina dake dakuma Waleed, wlh sainaga bayanku dukanku, zaku gani, sukuma su Hassana dasuka tona sainaga bayansu" ya shiga ihu kaman wanda ya haukace yana tutturjewa suna fisganshi basu damuba haka suka fizgeshi sukai waje dashi suka sashi amotarsu yana surutai kaman zararre sukabar anguwan dashi.

Ina masu neman turare exotic ones, masu mugayen dadi, masu kama daki, masu dadi, da armashi, long lasting turaren gargajiya gashi sanyi yazo, Awwaba Scent got you covered, kayanta akwai sauki, tana delivery ko'ina, me kuka jira ne wai? 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 Just chat her up kuga abun mamaki ga number tanan https://wa.me/+2348034236800
[11/27, 9:56 PM] saleemah: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫

✍️ M SHAKUR

END!!!
Chapter 103 · 0% Book details