← Book details Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 90

Sashe 44

Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yadda ya ke son hakice abun a ransa amman ya kasa doli yayi alwala ya fara karatun Alkur'ani a haka ya fara jin sassauci har ma ya ci abincin da Badiya ta kawo masa.
Ta zauna kusa da shi ta na kallonsa yayinda mai tsaronta ita ma ta kasa ta tsare ta na hankalce da su,jariri ta ke gasa ma cibiya amman rabin hankalinta na kansu.
"Miye wai ke damun ka?" BADIYA ta tambaya,kai ya girgiza mata yace "babu komi,je ki karɓo min Daddy ina son ganinsa duk yau ban ɗauke sa sosai ba"
"Yanzu aka yi masa wanka sai an shirya sa,tun É—azu ya ke rigima wai zafi ya ke ji"
"In shaa Allah ya kusa shiga AC sati mai zuwa za mu tafi Agadas" BADIYA tace "na zata sai mun yi arba'in ai" ya waro ido yace "rufa min asiri ai na matsu na tafi na ga Kakanni na" Badiya ta haÉ—e rai tace "sai maganar auren ku ko?" Yi yayi kamar bai ji ta ba ya É—auki ruwa ya fara sha.

BADIYA ta tashi daga inda ya ke ta na jin wani azababen kishi na taso mata,Bébé Adams ta karɓa ta fara basa nono yayinda idonta ke ɗigar da hawayen baƙin ciki.
Basheer ya girgiza kai a zuci ya na jinjina girman kishin mata wanda ya ke cike da zallar hauka.

A yau aka yi suna an yi biki sosai wanda Mamy ta É—auki charge É—in komi.Tunda Æ´an bikin suka watse BADIYA ke kwance babu lafiya,jini sai zuba ya ke yi mata kamar yau ne ta haihu.
Doli suka tafi asibiti, Sheera ke riƙe da Bébé Adams ta na ririga shi,kamar an ce ta waiga ta tsinkayi Maryam.Mamy ta baiwa BB ɗin kafin ta nufi inda Maryam ke tsaye jikin wani iccen gwaba, "Maryam?" Da sauri ta waigo ta na ganin Sheera ta fashe da kuka tare da faɗawa jikinta.
"Minene ba ki lafiya ne na ga duk kin rame kin yi baƙi?"Sheera ta tambayeta,cikin kuka tace "Sheera ina cikin tashin hankali banda lafiya sosai duk exam ɗin da ake yi min result ɗin nunawa ya ke lafiya ta lau alhalin ina jin raɗaɗi musamman a ƙasana tamkar zai zazzago haka na ke ji.Tun da Farida ta ɓata kullum sai nayi mafarkinta wai ta na cikin wata duniyar mutanen ɓoye"
"Kamar ya ta ɓata?"Sheera ta tambaya , ta goge hawaye tace "kiyi haƙuri na ɓoye maki Farida da Daddyn ki suke holewa shi ya shigar da ita ƙungiyar asiri,nima Alhaji Tambari ke faɗa min ashe shi ma ya na ciki shine ya ke son nima na shiga in kuma ba zan yarda ba to ba zan taɓa warkewa ba"

Tunda Maryam ta furta da Daddy Farida ke holewa kwanyar Sheera ta tafi hutun wucen gadi,wata irin tsanar su ce taji hakan yasa ta bar Maryam nan tsaye ta koma ciki.
Da Basheer ta ci karo kawai sai ta shige ƙirjinsa ta fasa kuka, Mamy wacce ke can zaune ta taso ta fara tambayar lafiya Cikin kuka Sheera tayi masu bayani,da sauri Basheer ya fito ya samu Maryam ɗin.

"Kin ga illar zina da kwaɗayin abun duniya ko?yanzu da kike da gida da mota miye amfanin su tunda ba ki da lafiyar da za ki morar su?" Basheer ya faɗa tare da tsayawa ya nisa kafin ya cigaba da cewa "zan taimaka maki na kai ki gun malamina zai yi maki ruƙiya bi'izinin Allah za ki samu sauƙi" godiya Maryam ta yi masa,sai da ya koma ciki ya shaida ma Mamy kafin ya kai Maryam can gidan malam Abba.

Dakyar BADIYA ta samu tayi kokowa da zuciyarta har aka samu hawan jinin ya sauka,sosai Mamy taji daɗin ganin ta warware Sheera dai na tsaye daga bakin ƙofa ta na kallonsu har Basheer ya dawo.
Takardar sallama likita ya basu suka je gida bayan ya baiwa BADIYA shawarar ta cire damuwa,sannan ta rinƙa controling fushin ta.

40days later

Cikin motar gida suka so shiryar tafiyar sai dai motar ba za ta É—auke su ba hakan yasa suka shiga Bus.
Tun ƙarfe biyar na asubah mota ke gudu da su amman ba su kai ba sai wuraren tara na dare .
Su na sauka Inna ta kira Kawu Laminu,ashe tun tuni su na cikin gidan motar shi da dogarai kasancewar shi tun jiya ya zo garin Agadas É—in.
Motoci ne na alfarma suka zo tarben su,bayan an gama loda kayansu suka shiga zuwa Masarauta.Zuciyar Mamy banda buga babu abinda ta ke yi,su na shiga cikin masarautar aka fara yin busa irin ta Æ´aÆ´an sarauta tuni duk jinin jikinsu ya fara gudu musamman Basheer da har wani cicira ya ke tamkar wanda ya hau mazari.

Duk ahalin gidan a falo suka tarar da su,Sarki Basheer wanda tuni tsufa ya kama shi sosai na zaune kan kujera ya miƙe ƙafafunsa gefensa na dama uwar gida sarautar mata ce uwa ga Adams da kuma Hawas yayinda gefen hagunsa kuma amaryarsa ce uwar ƴaƴansa Ƴan mata guda shidda.
Bisa gwiwoyinta ta zube ta na wani irin kuka tamkar ranta zai fita,yayinda su kuma iyayenta ke murmurshin farin ciki dan su tun da Kawu Laminu ya kawo masu labarin ta suka yi nasu kukan.

Sarki ya buÉ—e hannuwansa ya na cewa "ku zo nan jikokina" Sheera tamkar jira ta ke ta ruga ta faÉ—a jikinsa ta na kuka yayinda Basheer yaje gun Mamie wacce ta tsufa ita ma sosai.
Inna da Badiya suka samu gu suka zauna suma su na sharar ƙwalla.
Kawu Laminu ne mai juriyar gabatar da kowa, Sarki ya karɓi BB Adams ya rungume ya na jin tamkar Ɗansa ne marigayi duk da dai kammaninsa ba su gushe ba tunda ga Basheer nan.

Masauki aka basu suka yi wanka kafin a gabatar masu da abinci,sun kuwa ci kafin a buÉ—e babin hira wacce ta soma da neman gafara da kuma godiya ga Ubangiji.
Sai da dare yayi sosai kafin sarki ya umarci kowa ya je masaukinsa, Sheera kamar za ta mutu jin sarki ya ware ma Basheer da BADIYA part guda.Ta zuntar baki ta nufi É—akin Mamie wacce ta kasance Kakarta, Mamy kuma da Inna a É—aki guda suka kwana.

Wasu hawayen takaici suka zubo daga idonta,Mamie ta girgiza kai tace "ba'a san ƴaƴan Sarauta da zazzafan kishi ba,saboda duk tsiyar ki dama sai an yi maki kishiya.In ba abun ki ba ina kika taɓa ganin Sarki ya zauna da mata ɗaya?gwara ma ki aro juriya dan kuwa bayan ke akwai wata"
Sheera ta kalleta da alamun mamaki,Mamie tace "eh na san komi Kawun ku duk ya fayyace mana tun zuwansa,yanzu haka tuni an tanadi abubuwan da za'a yi shagalin bikin ku sati mai zuwa "ta faɗa ta na miƙo ma Sheera wani kindirmun nono cikin kofi fari ƙal da shi,ba tace komi ba ta karɓa ta fara sha sai taji ashe hadda niƙaƙen cikwi a ciki ga wani goût na daban wanda ba ta san ko miye ba.
Sai da ta sha rabi sannan ta janye kofin, Mamie tace"a'a duka za ki shanye akwai wasu ma da za ki sha nan gaba" Sheera ta waro ido kafin ta shanye,wani ɗan murfi Mamie ta cika da zuma ta bata ta sha daga nan ta fara a'auna mata kaloli wasu bauri,wasu ɗaci,wasu kuma zaƙi.

Sheera ta turo baki tace"Ni dai na gaji a bar ni a haka kar cikina ya fashe "Mamie tayi dariya tace "ai kuwa sai dai ya fashe ungo daga wannan shikenan"ta karɓa ta sha, Mamie ta rufe ƴar ƙaramar frigo kafin ta buɗe wani akwati.

Tiririn ƙamshi kala-kala ya fara fitowa,wata jigida ta fitar daga cikin gidanta ta baiwa Sheera.Abun ka da ba sabon ba sai Sheera taji tamkar jigidar na iya hanata barci "Mamie gaskiya wannan duwatsun za su takura min"
"Ai kuwa gwara ki saba dan kuwa jigida na da wani sirri na daban,duk cikakken nami in yaji ƙararta doli ya ji ra'ayin ki" Sheera ta washe baki tace "a haba! Gaskiya to ina so a bar min" Mamie ta girgiza kai ta sake miƙo mata wata ƴar ƙaramar sarƙa mai rabacar ƴaƴan azurfa tace "ki saka a ƙafar dama"ba ta musa ba ta kuwa saka sai ta ga ta ƙawata ƙafar.

Wani zane ta fiddo mai shegen ƙamshi tace ɗaura wannan sai na baki turarurukan da za ki linde jikin ki, Sheera ta karɓa tayi ɗaurin ƙirji.
Mamie ta buɗe mata kwalaban humra Sheera ta fara linde duk jikinta da shi,ta na gamawa Mamie ta nuna mata gado tace "to jeki ki kwanta ai kin yi ƙoƙari ma"haka Sheera ta lafe kan gado ta na tunanin wai auren su za'a yi da Basheer.

"Ban gane gajiya gare ki ba?Ni kenan ba mutum ba ne da zan ce na gaji?" Basheer ya faÉ—a ya na kallon BADIYA wacce ta dire daga kan shimfiÉ—ar su ta na guje masa.
Ya sassauta murya yace "dan Allah ki zo ba zan wani daɗe ba kin ji"ta maƙe kafaɗa ta na kallon BB Adams.
Basheer ya tanke fuska tare da yin kwanciya ya juya mata baya,so ya ke yayi zuciya amman ita wutsiyarsa ba ta san wannan ba.An ɗauki kamar minti goma sannan BADIYA ta zo ta kwanta,da sauri Basheer ya murƙusheta ta na kuka ta na ƙari dan tunda tayi arba'in yau ne haɗuwar su ta farko.

Washegari
Duk Æ´aÆ´an sarki masu aure a cikin Agadas tuni sun zo yayinda sauran kuma sai nan gaba.
Wata ƙaramar Walima Sarki ya haɗa ta taya murna,zuwa marice kuma aka gabatar da akwatunan auren Sheera inda sarki ya wakilta Kawu Laminu matsayin waliyin ta.
Chapter 44 · 0% Book details