← Book details Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 90

Sashe 39

Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarƙashin wata bishiya ya nufa da su,ya na tsayawa Sheera ta sauka shi ma haka kafin ya tangale mashin.
"Zauna!"ya umarce ta ya na mai nuna mata moto,tayi zaune ta na kallonsa shi kuwa Basheer hannuwa ya harÉ—e ya na kallonta.
Sheera ta sunne kai tace "tun watannin baya da suka wuce na taɓa ganin Daddy a falo shi ɗaya zaune su na meeting da mutanen da idona suka kasa gani sai dai zantukansu kawai,Ni ba wannan ne ya ke bani tsoro ba yadda naji su na ambatar sunana"
"Miyasa ba ki gaya ma Mamyn ki ba?"
"Tunanina ne aka garwa da na wata lusarar dabba,sam na manta ko kaÉ—an wannan tunanin bai zuwar min sai yanzu.In na gaya ma Mamy za ta shiga damuwa kuma ban son matsala ta shiga tsakaninsu,ina son Daddyna sosai" Sheera ta faÉ—a ta na kuka, Basheer ya ja dogon numfashi kafin yace "babu abinda zai yi maki,yanzu ina son ki saka masa ido da farko ina son sanin plan É—in sa game da ke kafin na san abun yi"
Sheera ta girgiza kai tace "ina jin tsoro sosai Sheebar,duk yadda kake tunanin Daddy to ya wuce nan har wani Mr É—in mu ya kashe fa kawai dan yace ya na sona"

"Ke ya aka yi kika sani?"Basheer ya tambayeta,shiru tayi ta kasa yin magana dan kuwa ba ta sani ba kawai dai zancen taji a kwanyarta.Gashin kanta da ya rufe gefen fuskarta ya gyara ya na mai cewa "kalle ni cikin ido" Sheera ta zuba manyan idonta irin nasa cikin idonsa kafin ta fara motsi da baki "Sheebar Jumma...."sai kuma tayi shiru ,ya lumshe ido saboda abinda kwanyar sa tayi masa capté daga cikin memory Sheera.
"Tabbas Jumma ce take amfani da tunanin Sheera,wace ce ita?miye alaƙar su da ahalin?"duk a zuci yayi tambayoyin kafin ya buɗe idonsa.

Sheera kuwa zoben hannun Sheebar ta ƙura ma ido wanda ke fitar da wani haske,da sauri ta hannunta ta taɓa ta na cewa "Sheebar ina son wannan zoben" maganarta ce ta dawo da shi daga tunanin da ya ke.
Wani abun almara zoben hannun nasa ya rikiɗe ya koma na diamond sai ƙyalli ya ke, ƙoƙarin ciresa Sheera ta ke daga yatsansa shi kuwa sam hankalinsa ya fara fita daga gare sa har ta zare zoben ta saka sa a nata yatsan.
Tamkar yadda ruwa ke kashe wuta haka Sheera ta fara jin sauyi a jikinta wani tururi na fita daga ƙofofin hancinta,da sauri ta rungume BASHEER sakamakon wani irin sanyi da take ji.
Kasancewar unguwar Æ´an bariki sam hakan bai wani damu mutane ba,hadari ne ya fara gangamuwa yayinda giza-gizai suka shiga gudu ruwan sama suka fara sauka.
Sheera ta fara sauke ajiyar zuciya ta na jin saukar ruwan tamkar ruwan zafi ne,sanyi da jikinta yayi a sannu ya fara fita.
Ruwa duk ya jiƙa su a haka Basheer ya goya ta ya kai ta gidan su, cike da nishaɗi ta shiga gida .
Wani uban ihu tayi ganin baƙin kare ya dirfafo ya nufo ta ya na habshi, Sheera ta ƙwala ƙara tare da faɗuwa ƙasa RAM ya rugo kenan zai cijeta wani haske ya fito daga zoben Sheera ya masa wani ƙulli cak ya tsaya daidai nan Daddy ya fito wanda dama bai jima da fiddo 🐕 ba a waje tsakar gida sai kuma ya ji kukansa.

Mamy da Jumma duk suma sun fito, Daddy ya ɗaga Sheera ya na tambayarta in ba taji ciwo ba.Da sauri ta shiga jikinsa ta na mai cigaba da kukanta,Mamy kuwa mafarkin da ta taɓa yi ya faɗo mata a rai.Da sauri ta ƙaraso ta na cewa "Daddyn Sheera ina kuma aka samu wannan baƙin Karen?gaskiya a fitar da shi" Daddy ya kalli RAM wanda ke fiddo halshe ya na son cizon Sheera wanda hakan ya tabbatarwa ma Daddy cewa lalle akwai laifin da Sheerar ta aikata.
Da sauri ya saki Sheera ya je ya Ram ya mayar da shi cikin kejin sa,kamar almara haka Ram ke yiwa Daddy magana a zahiri habshi ya ke amman abaÉ—ini jawabi ya ke "Sheera ta sanar ma wani da sirrin ka amman ban san miye tace ba haka na kasa tantance ko waye" hankali tashe Daddy ya nufi cikin É—aki ko kallon Sheera bai yi ba wacce Jumma da Mamy ke aikin rarrashinta.

"Ba ka da hankali AlGabid,har sai yaushe ne za ka gane cewa zaman iyalan ka cikin gidanka za su kawo ma matsala?ita wannan matar ta ka ina so ka koreta ta bar gidan ka duk wata matsa da kake ganin ta na tasowa daga ƙugunta ne.Budurcin Sheera kuma ina son ka karɓe min shi nan da sati mai zuwa,in mun je meeting zan gaya ma wajen da za ka kaita domin kwantawa da ita" shugaba Marlin ke magana ya juya ma Daddy baya.
Hankalin Daddy in yayi dubu to ya tashi "waye ta faɗa ma sirrina?" Daddy ya tambaya "ka nemo da kan ka wannan ba matsala ta ba ce!Sannan ka sani tuni kujerar muƙamin ka ta fara rawa hakan na nuni daf kake da rasata.Budurcin Sheera shine sacrifice na ƙarshe da za ka kawo,rashin kawo sa kuma ya na daidai da fitar numfashin ka" Marlin ke faɗa fuskarsa a murtuƙe.

Daddy yace "na sani shugaba,kawo budurcin Sheera shine abu ma fi sauƙi a rayuwata tunda da wannan burin na ke kwana na ke tashi.Zan nemawa ita mahaifiyarta ta wani gidan,amman ba zan iya nisanta Sheera daga gare ni ba za ta zauna nan ita da Jumma"
Marlin yace "in kayi hakan da ka taimaki kan ka"ya ɓacewa ganin Daddy tamkar wani hayaƙi.

FARIDA POV.

Sosai ta zo da maƙudan kuɗi wanda ita kanta ba ta san iyakar su ba,déjà ta buɗe compte bancaire can ta zuba dukkan kuɗin da Daddy ya bata.
Ranar da ta dawo dakyar Maryam ta gane ta,ihun murna suka fara kafin su zauna su fara hirar yaushe gamo.
"Yanzu nan dagaske ke ce Farida?kin ga yadda kika koma fatar jikin ki sai wani sheƙi? Gaya min wace irin rayuwa kuka yi ke da alhajin ki?" Maryam ta faɗa ta na gyara zama,Farida tayi dariya tace "dan Allah ƙawata ki bari har gobe duk zan gaya maki komi yanzu dai wanka zan shiga in na ci abinci ki raka ni na sayo mota" Maryam ta waro ido tace"har da mota za ki saya waiiii! Kice dai za mu zaga gari sannan mu ci mai kyau ?"

"Eh duk abinda mu ke so za mu yi a yanzu tunda ina da isassun kuÉ—i,ke dai bari nayi wanka"Farida ta faÉ—a ta na shiga toilet.Bayan ta gama wanka ne ta fito "wai Ni kama ya Ameee ÆŠan gouverneur har yanzu ya na nan da É—aukar kai?"
Maryam tace"hum!ai ki bari wulaƙanci sai ma abun da yayi gaba"
"Wlh ƙawata ina mugun son gayen nan,ban san ya zan yi ba" Maryam ta marairaice fuska tace "nima bayan tafiyar ki na faɗa son Yayan Sheera Allah kamar nayi hauka"
"Dama Sheera ta na da wani magaji ne?shine kuma AlGabid bai taɓa yi min hirar shi ba?"
"Waye kuma AlGabid?"Maryam ta tambaya
"Baban Sheera mana"Farida ta ba ta amsa , Maryam tace "kar dai ki ce min shine ya ja ki zuwa Dubai" Farida ta É—aga gira tace"eh ko da matsala ne?" Maryam ta girgiza tace "sam hakan bai dace ba!Kuma in Sheera sani ba za taji daÉ—i ba"
"Sai in ke za ki faÉ—a mata kuwa"daga nan ba su ce komi ba har Farida ta gama shiryawa suka fita cikin motar Maryam.

Macijin cikinta ne ya fara yi mata yawo ya na yi mata tuni akan lalle yunwa ya ke ji,Farida ta ja tsuki tace "dan Allah ki canza akala mu fara zuwa gidan cin abinci kafin mu tafi sayen motar" Maryam tayi dariya ta canza alakalar kamar yadda ta buƙata ta na mai cewa "ke wannan duk ranar da kika samu ciki an shiga uku,lokacin da kika shigo fa da ledar abinci a hannunki ki na ci kuma yanzu har kin ji yunwa" Farida kasa cewa tayi komi saboda cikinta ke faman ƙugi.
Ko da suka isa gidan cin abinci da sauri ta masu oder abincin mutum biyar,Maryam da É—aya ita kuma huÉ—u.
Maryam sai kallonta ta ke cike da mamaki yadda har ta canye plat biyu ta fasa ta uku,su na nan zaune Alhaji Tambari ya zo a bazata ya ja kujera ya zauna ya na shirin magana idonsa ya sauka kan macijin Farida....
[10/08 à 14:39] Chamsiya Laouali Rabo: *PAID PAGE🪶*

*LITTAFIN KUƊI NE ƳAR UWA KI BIYA 200 KACAL DOMIN KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI,DUK MAI BUƘATA TA TUNTUƁE NI TA WHATSAPP* +22795045822 DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK BA TARE DA TA BIYA TA SA A RAN TA INA BIYAR TA 200 KO GOBE.

*X*

Bai ce komi ba sai ɗan satar kallonta da ya ke yi ya na mamakin yaushe kuma ta shiga ƙungiyar asiri?
"Ka tuna ta kuwa?ƙawata wannan wacce ka tarar da ita a hotel?"Maryam ta tambayi Alhaji Tambari ganin kamar ya na yiwa Farida kallon ƙasa-ƙasa ita a tunanin ko bai gane Faridar ba ne.
Ya murmusa yace "na shaida ta!" "Yauwa! Ta na son sayen mota ne shine za mu je in mun gama cin abinci" cewar Maryam, Alhaji Tambari yace "ta gayi irin wacce ta ke so sai ta bani congilar kawo mata ita"

Farida wacce ke ta fafutukar cin abinci ta dube sa ,karon farko da ta sa baki cikin hirar "irin ƙatuwar nan na ke so mai taya baya,fara mai baƙaƙen madubai"
"An gama ba ki da matsala in kin shirya saya sai ki min magana sati mai zuwa ana kawo maki ita"
Farida ta siÉ—e yatsunta tace "ko a yau in zai yiyu a shirye na ke" Alhaji Tambari ya ciro wayar sa daga aljihu ya nuna mata hotunan motoci kala-kala,nan Farida ta ruÉ—e ta rasa wacce za ta É—auka duk da can farko ta na da chooce .
"Ina ma ace duk a bani su wlh duk sun yi min"ta faɗa cikin dariya, Maryam ta karɓi wayar tace "RAV4 ɗin nan dai duk ta fi su kyau kawai ki ɗauketa,in kuma ki na da ra'ayin ƙari sai ki sayi ƴar ƙarama kamar tawa"
Chapter 39 · 0% Book details