← Book details Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 90

Sashe 32

Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka ci abinci sannan ku tafi,za ka rakata har can ciki ka yi ma shugan nasu bayani ba ta jin daɗin jikinta ne kwana biyu"Mamy ke magana ta na kallon BASHEER ,ya gyaɗa kai yace "to Mamy babu damuwa" da sauri duk suka kalle shi Sheera tace "wai Mamy hum..."ya ɗago ya harareta yace "halan ke ɗaya ke da Mamyn?" Ta muguɗa baki ta ɗaga gira guda tace "Yes!daga ni babu kowa ni ce ta farko ni ce Auta"wata harar ya kuma yi mata kafin yace "ke ce dai ta biyo Malama,ko ba kiji sunan ki ba Busheeraaaa hakan na nufin akwai Yayan ki Basheer yeeelum😝" yayi mata gwalo .

Sheera ta fara kukan wasa dan kuwa Mamy da Jumma ba su ji abinda yace ba hasali ma su na can su na hirar su daban.Mamy ta waigo tace "Sheera lafiyar ki kuwa?" BASHEER yayi dariya yace "ina ga Mamy abun ne ya motsa sai an yi mata turaren salamatu 😆" ruwa cike da kofi na sanyi ta ɗauka ta watsa ma BASHEER a fuska kafin ta tashi ta fita da gudu.
Ya ja ajiyar zuciya Mamy ta taso hankali tashe ta sa gefen mayafinta ta goge masa fuska ta na basa haƙuri,murmushin ƙarfin hali yayi ya cigaba da cin abincin sa bayan ya gama yayi masu sallama.

Bisa babur ya tarar da ita ta na selfie sai dariya ta ke,tsawa ya daka mata yace "keee!"ta zabura ta miƙe wayar hannunta ta faɗi ƙasa ya duƙa ya ɗauka ya sata aljihunsa.
Idon Sheera suka ciko da ƙwalla ta dubi Basheer ta ga duk ya turniƙe fuska,da sauri ta sunne kai ta na wasa da yatsunta.Ya hau 🏍️ ya kunna,ta mirror ya kalleta kyakkyawar fuskarta ya ƙura ma ido.Da sauri ya rumtse ido ganin ƙwallarta ta ɗiga a ƙasa,sosai yaji zafin haka.Murya a ɗan dake yace "hau mu tafi"ta goge hawayen da bayan hannunta kafin ta matsa,gefen cikinsa ta matse sannan ta hau babur ɗin.
A slow ya fara gudu ya na tunanin ita kuma Sheera wane maras imani ne ya sihirceta?dan kuwa ya gani a idonta.Babu wanda yayi ma É—an uwansa magana har suka isa makarantar.

Ya na tsayawa ta fara ƙoƙarin sauka sai dai sam ta kasa saboda yadda bujen ta ya matseta sosai sai ya tashi sannan ta iya birkito ƙafarta .Ta turo baki ta na ƙara gwada sauka amman halo ta kasa,ta ɗan tura bayansa da dukan hannuwan ta kafin ta fara kukan sangartar ta wanda ta saba "ka tashi na sauka mana"ta furta a shagwaɓe wani yarrr BASHEER ya ji kafin ya gyara mirror ɗin moto 🏍️ ya na kallon yadda ta ke faman zumɓurar baki.
Ya lashi baki ya na jin ina ma ace laɓanta mallakinsa ne da in ya fara tsutsar su Allah kawai zai taɓe ta "dan Allah ka tashi ka ga fah na makkara kuma mutane sun fara kallon mu"ta sake faɗa cikin sigar roƙo,yayi murmushin gefen baki kafin yace "ai ba Ni na hauda ki ba"ta harare sa ta cikin mirror tace "to ce ma nayi ka sauke ni balle ka gaya min magana?" "Ko kin ce hakan ba zai faru ba dan ba ke ce Badiya ba" "wace Badiya ?" "Bad baby matar BASHEER mana" ta ja tsuki tace"ohon maku in ma da Badaru ne miye ruwana" BASHEER yayi dariyar mugunta yace "shiyasa har kika ji haushi jiya kika yi ta kuka"ta waro ido tace "Ni ɗin? Allah kiyaye min da yin kuka saboda wata banza" BASHEER ya haɗe rai sosai ya juyo ya na kallonta cikin dakewa ya tambaye ta "wace ce banza?"wani tsoro ya kamata sai ta kasa magana sai faman juya ido.Ta yunƙura dakyar ta na mai ɗora hannunta kan kafaɗun sa ta sauko.

Shi ma sauka yayi bayan ya kile kan 🏍️,ciki suka shiga ya yiwa shugaban makarantar bayani kamar yadda Mamy ta buƙata.Shugaban yace "ok to babu matsala za'a yi mata exam ɗin da ba tayi ba,dan haka ki zama cikin shiri ok?" Sheera ta gyaɗa kai.
BASHEER ya fito har ya kunna babur ya tsinkayo muryar ta "Sheebar...."ya tsaya tare da waigowa ya kalleta da ɗan gudu ta ƙaraso kafin tace "waya ta" "ba zan bayar ba"ya faɗa ya na mai tada moton da gudu ya bar harabar makarantar.
Sheera ta riƙe ƙugu ta na jin wani takaici na luluɓe ta,"mi ya ɗauki kansa da har zai ja da ni"ta faɗa a fili sai kuma Zuciyarta tayi wani matsananci bugawa tuna sam wayarta ba ta da code ga kuma vidéos ɗinta na lesbian.Ji tayi kamar ta ƙurma ihu,jiki babu ƙwari ta nufi aji.

BASHEER kuwa yawo ya fara yi a gari ya na aikinsa na ƊAN ACAƁA,sosai ya samu kuɗi.Gida ya nufa da kansa ya zuba ruwan wanka saboda har yanzu Badiya fushi ta ke da shi.Bai tambayeta abinci ba dan bai ga alamun ta yi shi ba,furar da ya shigo da ita ya dama ya sha kafin ya haye gado Badiya cikin gunguni tace "kamar gadon shi"bai tankata ba sai wayar Sheera da ya fiddo ya fara dubawa,mutuwar kwance yayi ganin mace da mace suna lasar junansu.Videos ne na lesbian sun fi 100 a ciki kama da na turawa da baƙaƙen fata,zuciyarsa ce ta fara lugude ya na jin ɓacin rai.Iska ya fara kaɗawa nan take yayinda idon BASHEER suka fara lumshewa suna wani yi masa danƙo, ɗifff ganinsa ya ɗauke sakamakon wani nanauyan barci da ya ɗauke sa......
[03/08 à 15:18] Chamsiya Laouali Rabo: *PAID PAGE🪶*

*LITTAFIN KUƊI NE ƳAR UWA KI BIYA 200 KACAL DOMIN KI KARANTA CIKIN KWANCIYAR HANKALI,DUK MAI BUƘATA TA TUNTUƁE NI TA WHATSAPP* +22795045822 DUK WACCE TA KARANTA MIN BOOK BA TARE DA TA BIYA TA SA A RAN TA INA BIYAR TA 200 KO GOBE.

*P*

Cikin mafarki rayuwar SHEERA ta fara zo ma BASHEER daki-daki,tamkar yadda in ka kunna Film ya ke tafiya épisode par épisode.Ya na gama mafarkin ya falka daga nanauyan barcin.Tasbihi yayi ga Ubangijinsa kafin ya tashi zaune,kansa ne ke ɗan sara masa kamar zai tsage.Agogo ya duba ya ga lokacin sallar zuhur har ya ɗan gota,ya sauka daga bed tare da fita waje banɗaki ya shiga yayi wanka gami da alwala sannan ya wuce masjid.
Zaune yayi ya fara tilawar alƙur'ani sai kuma mafarkin da yayi ya dawo masa a kai,zuciyarsa ta tsananta bugawa yayinda kuma gefe guda ya fara tunanin ta ina zai taimaki Sheera?
Ya ja ajiyar zuciya ya na tunanin yadda ya ga kyakkyawar surar SHEERA a mafarki su na aikata masha'a ita da Farida.
Da sauri ya tashi ya fita daga masjid É—in,ya na zuwa gida ya ja babur É—insa sai MARYAM ABACHA makarantar su Sheera.
Da taimakon shugaban su aka kai shi har inda suke karatu,ɗan nesa da ita ya tsaya ya na kallon ta kafin ya ɗaga murya yace "Sheera???" Da sauri ta juyo suka haɗa ido huɗu.Tayi saurin miƙewa ta na tuntuɓe ta nufo sa,ko gaishesa ba tayi ba tace "wayata ce ka zo kawo min ?ta na ina?" Ɗan madaidaicin bakinta ya tsura ma ido sai ya ji ta bada tausayi.

"Ina Farida ?"ita ce tambayar da yayi mata,ta kallesa dakyau cike da mamaki tace "ina ka santa?"ya haɗe rai yace"ki dai bani amsata kawai" ta turo baki tace"tayi balaguro " "ya aka yi kika sani ke da ba ki zuwa makaranta kwana biyu da suka wuce?"tayi shiru ta na kallon shi kafin ta bashi amsa da "ƙawarmu Maryam ta shaida min tun ranar da wani mai mota ya tafi da ita ba ta dawo ba sai jiya da ita Faridar ta kirata ta shaida mata ta tafi Turai" BASHEER ya lumshe ido komi sak irin na mafarkinsa "shi kuwa Daddyn ki fah?"ya faɗa ya na mai zuba mata ido.Yanayin fuskarta ya canza kafin tace "ban sani ba lokacin banda lafiya,to wai kai wane ne ma da za ka tsare ni da tambayoyi?"ta faɗa ta na hararensa,yi yayi kamar zai tsone mata ido kafin yace " *ƊAN ACAƁA* ne amman kuma ya sha banban da wanda kika sani"ta ja tsuki tace "ban wayata" ya maƙe kafaɗa yace "na ƙi na bayar ta ƙarfin tsiya ce,in kuma ki na da shi ki zo ki ƙwata"ta turo baki ta na kallon manyan damtsansa ga wani ƙaton ƙirji,dariya ta kwashe da ita tace "wlh in da boxe ma ka shi na san za ka zubar da ƙatti yo irin wannan damatsa kamar Singam"
Shagala yayi da kallonta yadda ta ke dariya har da wani riƙe ciki ,ƙugu ya riƙe ya cigaba da kallonta.Ta tsagaita dariyar tace "dan Allah in lokacin Kokowa yayi ka shiga gasar na san za ka iya..."ya matso da da ita da sauri ta gimtse maganar ta na kallon shi.
"Nace ko za mu gwada yin kokowar da ke?" Ta ture sa yayi baya kaɗan kafin tace "Allah kiyaye min da na haɗa jikina da na ka mai warin ƙatti"

Basheer ya haɗe rai yace "waye ƙaton?"yadda yayi maganar cikin tsawa yasa ta shiga hankalin ta,murya na ɗan rawa tace "kayi haƙuri wasa na ke ma"ya kuma game fuska yace "Ni abokin wasar ki ne?"ta girgiza kai "kenan raina ni ne kika yi?"a dake ya sake yi mata tambayar hakan yasa zuciyarta yin rauni sai hawaye.
Ba ta san miye dalilin da yasa ta ke jin shakkar Basheer ba a duk in ya shiga wannan yanayin,ya ja dogon numfashi haka kawai bai san mi ya ja ra'ayinsa ba ya kamo dukkan hannuwanta."ÆŠago ki kalle ni"ya faÉ—a a tausashe cikin murya mai sanyi,ta É—ago dara-daran idonta ta zube su cikin nasa.
Ya kuma jan ajiyar zuciya yace "mine ne?kukan mi kike?"ta rausayar da idonta suka wani juya hakan ya baiwa hawayen idonta damar É—asowa.
Wani irin zafi yaji har cikin tsokar ransa,ya busa fuskarta ta lumshe ido ta na jin wani irin yanayi.
Chapter 32 · 0% Book details