← Book details Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 90

Sashe 38

Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sheera ce ta ja hannunsa zuwa tsakiyar salon ta fara yi masa surutu kamar kanya,shi kuwa saurarenta kawai ya ke amman hankalin sa bai tare da shi.
Jus kawai ya sha ya miƙe ya nufi ɗakinsa,wanka ya fara yi kafin ya buɗe drower sa ƙaton karensa mai suna RAM yayi ɓul ya fito ya na kaɗa bindi.Daddy ya saki wani murmushi "Barka da fitowa duniya a karo na biyu a rayuwar ka,yanzu kam za ka wataya cikin gari duk ina kake so.Za ka yi min maganin duk wani mugu da munafuki kar ka raga ma kowa duk wanda ya cuce ni ko da a ɓoye ne kai za ka ɗauki mataki ta hanyar cizonsa daga nan zan yi abinda ya kamata na janye masa sauran jinin jikinsa.Fatan za kayi haka domin ina son yin kuɗi fiye da kowa na duniya hhhh" Daddy ke faɗa ya na shafa kan baƙin 🐕 wanda tamkar ya na magana da mutum har gyaɗa kai ya ke ya na fiddo halshe alamun zai yi biyayya.
System ɗin sa ya kunna sai dai wayam babu komi,wani ƙululub baƙin ciki ya rufe sa so ya ke ya ga ta yaya aka yi Sheera ta samu lafiya tunda shugaba Marlin yace bai da hannu a ciki.
Wayarsa ya ɗauka ya kira Jumma,ba ta wani jima ba ta shigo ɗakin fuskarta a murtuƙe.Kallonta yayi na wani ɗan lokaci kafin ya juya allon system ɗin gabanta yace "ya aka yi babu komi a ciki?" Cikin dakiya Jumma tace "ka tambayi system ɗin mana" Daddy ya waro ido sam bai yi tunanin abun Jumma ya kai haka ba na za ta iya gaya masa baƙar magana.

Dakewa yayi ya nuna kamar bai ji zafi ba ya ƙara tambayarta"kin taɓa ganin inda system tayi magana?" Ta fara wasa da yatsunta tace "mi zai hana in kuwa ta kasance ta matsafi ce?"tayi maganar ta na wurga masa idonta da suka rikiɗa suka yi wani irin ja tamkar garwashi.Sai da gaban Daddy ya faɗi amman da ya ke shi ma mugun gaske ne sai ya miƙe tsaye yace "zan ko tabbatar maki da Ni matsafi ne amman ki jira lokaci" "tabbarwa ta nawa kuma bayan ga baƙin kare nan ka aje a matsayin dodon tsafin ka?"
Gefen wuyansa ya shafa ya na wani juya kai kafin yace "fitar min daga ɗaki" ta taɓe baki tace "ko ba kace ba fita zan yi mtsw " zuciyar Daddy ta shiga bugawa da ƙarfi kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito, RAM ya kalla wanda ke bin Jumma da ido, Daddy ya girgiza kai yace "a'a kar ka ɗauki matakin komi ta na da sauran amfani a gu na"ya na gama faɗa ya saka kaya ya nufi ɗakin Mamy.

A zaune ya tarar da ita kan sallaya ta na jan casbi,da mugun mamaki yace "sallar mi ce kike yi yanzu?"ba ta ko kalle sa ba balle yasa ran za ta amsa.Ya zauna kusa da ita ya ja ajiyar zuciya kafin ya kamo hannunta yace "kiyi haƙuri dan Allah ki bar wannan fushin"ta dubesa tace "fushi?fushi akan mi?saboda kai zan yi fushi?mutumen da ya tsallake Ƴar cikinsa ya tafi yawon shsƙatawa ba tare da ya tunanin wane halin iyalansa ke ciki?"kawai sai ta fashe da kuka ,Daddy ya rungumeta da sauri kuma ya janye jikinsa sakamakon wani abu girrr da ya ja sa tamkar lantarki.

Tashi yayi tsaye ya na kallonta,sai kuma ya fice ya na tafiya kamar wanda bai cikin nutsuwar sa.Ɗakinsa ya shiga ya ƙargame da key kafin yayi shigar jajayen kaya ya haɗe fuskarsa da farar hoda,sunayen manyan aljanu gami da wasu kalaman tsafi ya ke faman ambato.
Tamkar a Film haka shugaba Marlin ya bayyana a ɗakinsa tsaye a jikin madubi,fuska babu annuri Marlin yace "sanadin rungumar waccan banzar matar ta ka wacce ta mayar da ambaton Allah ruwan shan ta ga shi nan har hantar cikin ka na kaɗawa" Daddy ya dube sa yace "miye abun yi kenan?" Marlin yace "doli su nisanta da kai,haka na sake haramta masu dukiyar ka.Ka canza masu gida saboda zamanta a nan babban hatsari ne ,dan da zarar ka koma taɓa jikinta ƙila abun ya fi haka"

Daddy ya girgiza kai yace "a'a ba zan iya yin nisa da su ba saboda su ɗin rayuwata ne,amman zan kiyaye haɗa jiki da ita.Ya maganar Sheera ita wane lokaci ne kuka ƙa'ide min na karɓa budurcinta?"

Marlin yace "nan ba da jimawa ba dan na ga yarinya tamkar kanta ya fara rawa,in lokaci yayi zan faɗa ma" Daddy ya jinjina kai yace "akwai wani yaro da na gan su a tare Ƙarfin Ikona ya kasa tantance shi waye,kar yaje ya canza ma Sheera akala" Marlin yace "wai ka na nufin ta fara kula samari?ka na aikin mi?"yayi tambayar cikin ɗaga murya , Daddy yace "a'a ba saurayin ta ba ne juste abonné ɗin ta ne"
"Zan tafi na ga alamu ba ka da hankali ,ayi ma abu ka kasa ɗaukar mataki ita wannan Jumma sai yaushe za ka kawo min ita?" Daddy yace " sai nayi tunani" Marlin bai sake cewa komi ba ya ɓace ɓat.

A ɓangaren Sheera kuwa ɗakinta ta koma ta na ta jaraba kiran Basheer amman ya ƙi shiga ,da zarar ta fara ƙara sai a maido mata kiran.
Ta rasa mi ke yi mata daɗi,tashi tayi ta ɗauki ƴar ƙaramar bag ta fito.Babu kowa a falo hakan ya sa ta fita zuwa bakin titi, adaidaita ta tsayar tace a kaita bayan école Soura.Bayan ya kawota ta biya sa kuɗi,nan ta fara tambayar ina ne gidan Basheer *ƊAN ACAƁA* sai da ta sha wuya sosai kafin ta samu wani yaro ya kaita.

A tsakar gida ta ga babur É—in BASHEER,tayi zaune a kansa kafin ta tura masa text.Kiransa ya shigo wayarta ta É—aga ta na dariya "ka fito mana Allah gani a cikin gidanka bisa mashin ban san ina ne lungun ka ba" ya kashe kiran kafin ya fito.

Daga bakin ƙofa yayi tsaye ya na kallonta cike da mamakin yadda aka yi ta zo nan,ta miƙe tare da nufarsa ta na murmushi.Jikinsa ta faɗa ta na mai cewa "kayi haƙuri Sheebar"bugun zuciyarsa ne ya ƙaru yasa hannu zai cireta amman ta riƙe sa gam.A shagwaɓe ta kuma cewa "doli ce ta sa ni furta baƙaƙen lafuza a gare ka, amman dan Allah kayi haƙuri" ya kalli cikin idonta yace "to naji sake Ni"ta turo baki tace "dan kar matar ka ta gan mu?" "Ke da ba ki sona to miye na tambaya?"ta saki murmushi tace"ina sonka fa irin sosai ɗin nan" Badiya wacce barcin da ta fara bai gama game mata jiki ba,ta leƙo kenan taji wannan furuci da sauri tace "Innalillahi wa'inna iley raji'un"ta na mai kallon lalausan hannuwan Sheera wanda suka zagaye BASHEER ta baya.

Da sauri Basheer ya waigo ya na kallonta, Sheera ma sake sa tayi ta na ƙare ma Badiya kallo."Har kin tashi ne ?mi kike ji yanzu?"Basheer ya tambaya ya na nufar Badiya,ta ƙwace hannunta idonta na wani irin rufewa tsabar bala'i tace "Basheer har cikin gidan aurena?wannan karuwar fa?" "Uwar ki ce karuwa" Sheera ta faɗa daga can bakin ƙofa BASHEER ya harareta kafin ya rungume matar shi wacce ke ƙoƙarin tafiya ta shaƙo wuyan Sheera.

"Sake ni wlh sai na ci uwar ta ko ma ɗiyar uban wace ce,shegiya mai kama da kafirai" Badiya ta faɗa ta na son kubcewa daga riƙon da Basheer yayi mata.Sheera kuwa ido ta waro ta na kallon ƙaton cikin Badiya wani maƙoƙon baƙin ciki ne ya rufeta tuna wannan cikin fah na Basheer ne, wata zuciya ta ɗibi Sheera kawai sai ta kutso Basheer ya daka mata tsawa kawai sai ta fashe da kuka.
Ya sungumi Badiya ya kaita ɗaki "dan Allah ki zauna kar ki jajiɓo min aiki wannan yarinyar da kike gani ba daidai ta ke ba,dan Allah ki tsaya nan kar ki fita" Basheer yayi ta lalaɓa Badiya kafin ya dawo gun Sheera wacce sai gwanjin kuka ta ke.

"To sai ki wuce mu tafi tunda kin gama ni da matata"ya faɗa ya na hararenta kafin ya ja hannunta su fita,babur ɗin ya kunna Sheera ta hau za ta zagaye ƙugunsa yayi saurin dakatar da ita.
"Dallah Malama kar ki ƙanƙame ni nan ba ADS ba ce mu na fita yara za su iya bin mu da ihu" Sheera ta turo baki ta na mai gyara zama haɗi da goge hawayenta.

Basheer na tuƙi ya na satar kallonta har suka hau babban titin da zai sada ka da quartier ɗin su,ta kwanta bisa gadon bayan shi murya can ƙasa-ƙasa tace "Sheebar mu tafi Plaza akwai maganar da na ke son mu yi" yayi banza da ita ,ta zura hannunta na dama daidai cikinsa ta matsa tace "please kajiiii" Basheer ya ja wani uban burki ya tsaya kafin ya buge mata hannu yace "shine kuma sai kin min mugunta ko?"ta turo baki tace"to ba kai ne ka ƙi saurarena ba"ya banka mata harara yace "gayamin ina jin ki" ta saki baki "a nan kan titin za mu yi magana?" Basheer ya kunna babur ɗin shi ya na mai cewa "tunda ba za ki faɗa ba ke kika sani" da sauri kamar zubar ruwa tace "Daddyna na cikin ƙungiyar asiri"cak bugun zuciyarsa ya tsaya yayinda kwanyarsa ta shiga juyawa ta na son tuno masa tsohon mafarkinsa.
Chapter 38 · 0% Book details