Sashe 24
Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ɓangaren su Basheer kuwa tuni ya girma yanzu Masha Allah ya na cikin 6years,duk wata kalma babu wacce ba zai furta da kyau ba.Sosai ya ke samun kulawa wajen iyayensa,kullum cikin karatun Alkur'ani ya ke wanda hakan shine burin Adams wanda ya ke kira da Abba.
Fatima na zaune ta na wanke kwanoni sai Basheer ya shigo da gudu hannunsa riƙe da wata ƴar ƙaramar ball ta leda,abun ka da yaro hannunsa ya kubce ta faɗa cikin ruwan da Innar sa ke wanke kwanoni.Dundu tayi masa a baya tace "ban hana ka wasa da wannan ball ɗin ba ?" Basheer ya fashe da kuka ganin Inna ta jefa ball ɗin saman rumfa.Wani dundun ta sake yi masa a baya wanda tayi da na sanin yinsa,wani raɗaɗi taji ga hannunta kafin ayi yarɓi da ita can gefe bisa kwanoni.Ball ɗin ta faɗo da kanta daga bisa rumfa Basheer ya ɗauki kayarsa ya na goge hawaye, Inna kuwa banda sunan Allah babu abinda ta ke ambata.
Abba ya shigo bakinsa É—auke da sallama, Basheer ya nufe sa sai kuma yayi tsaye ya na kallon mahaifin nasa.
Abba ya jawo sa jikinsa yace "Basiru na lafiya kayi tsaya?" Inna da ta tashi ta na kwashe kwanonin tace "yauwa tunda Allah ya kawo ka ai shikenan,yanzu nan wani lamari ya faru da ni"nan ta kwashe komi ta shaida masa shiru yayi na ɗan wani lokaci kafin yace " bari mu kai sa gun Baba Malam to ni wannan lamari na Basiru na rasa kansa haka fa jiya ya ke bani labarin wani abu da ya taɓa faruwa kawai shiru ne nayi.."bai ƙarasa zancen ba wayar sa ta ɗau ringing ya na ɗagawa aka ce "an kawo wata mata ne haihu jini ya ƙi tsayawa kamar irin cas ɗin da ka taɓa réglé ne shiyasa mu ka kira ka"
Abba ya nufi waje hankali tashe ,Basheer zai bin sa Inna ta riƙe sa.Kuka ya fashe da shi ya na cewa "Abba kar kaje zai k..a s.he kaaaa "kasancewar cikin kuka ya ke maganar sam Inna ba ta fahimci abinda ya ke cewa ba.Ganin rigimar Basheer ta ƙi ƙarewa ya saka Inna rufe ɗaki ta ja sa zuwa gidan Baba Malam.
Abba ko kuma Adams na zuwa asibiti ya aje babur ɗinsa,tun daga nesa Jumma ta gane sa.Zuciyarta ta shiga bugawa da ƙarfi,sai ta samu kanta da ɓoyewa ta na kallonsa ya na yiwa wata nurse bayanin yadda ake yi a tsayar da jini tare da mata alama ta tafi ta fara aikin ya na zuwa.
Ya fito waje dan nemo wani abu pharmacie suka yi kiciɓus da AlGabid,ƴar kallon-kallon suka fara kafin AlGabid ya nuna sa da ɗan yatsan sa manuni kawai sai Adams ya dafe saitin zuciyar sa ya na jin wata azaba.
Jumma da ke can laɓe tace "Adamssss!"tare da nufo sa da sauri,kasancewar duk an tafi sallah asibitin tsit ta ke AlGabid da sauri ya bar gun ya shiga can cikin asibitin sai kuma ya kirawo Jumma ta na kallon Adams dafe da zuciya ta bar sa nan.
Dakyar Adams ya ɗauki babur ɗin sa ya nufi gidan Baba Malam,saboda sarai ya san da tsafi ne AlGabid ya riƙe masa zuciya.
A can ciki nurse tayi nasarar tsayar da jinin a ƙarshe kuma aka cire mahaifar Mamy gaba ɗaya,jaririya sai kuka ta ke carawa.
An kai Mamy ɗakin hutu, Jumma ido sun yi mata jawur saboda kukan da tayi, shi kuwa AlGabid duk bai cikin nutsuwar sa hakan yasa ya baiwa Mamy damar zaɓar suna.Murmushi kan fuskar ta tace "tunda Allah bai sa na samu namijin ba a saka mata Busheera" haka kuwa nurse ta rubuta a takardar jaririyar.
Kafin AlGabid ya tafi sai da ya É—aure bakin Jumma ta yadda ba za ta gaya ma Hawas abinda ya faru ba,cike da so ta ke kallon Baby wacce ke kama da ita sak sai idon da ke kama da na Adams irin na mage.Tayi murmushi ta shafi sumar kanta kafin ta fara tofe ta da addu'a,ta na mai jin kewar Yayanta sai dai babu yadda za ta yi.
Ba su É—auki lokaci ba aka sallame su suka tafi gida,nan ne kawai Daddy ya É—auki Babyn nan yaji duk duniya in akwai wacce ya ke so to sai dai ta biyo bayan ÆŠiyar sa.
"Yanzu sabida Allah duk sunayen ƴan gayu ga su nan dayawa amman ki rasa wanda za ki zaɓa sai Busheera?hum!to ni dai da SHEERA zan rinƙa kiranta"Daddy ke faɗa,ita kuwa Mamy dariya kawai ta ke yi sam ba ta gaya masa ba saboda Sarki Basheer wato mahaifinta ta saka sunan ba.
Ahmad kuwa na ta aikin shafar gashin Sheera wanda ya ke da yawa sosai ga sulɓi,Jumma dai na gefe ta na ƙara auna rashin imani na Daddy da farko mamaki ya ke bata amman yanzu tsoro ne ƙarara danƙare ga ranta.
Gidan Baba Malam Basheer bai jima da yin barci ba,aka kira wayar Inna aka shaida mata Abba yayi accident.Ko da suka isa asibiti tuni rai yayi halin sa,haka aka yi masa wanka tare da kai sa gidan gaskiya ita kuwa Inna tun daga ranar ta yi watsi da wayarta.Basheer kuwa tuni an tura sa Maiduguri wajen karatu,a nan gidan kakaninta ta cigaba da zama har ta gama ta kaba.Duk mijin da ya fito mata sai ta ƙiya, lokacin da ta zo ma Laminu da maganar ta na son zuwa AGADAS ko dan ta kai Basheer gun dangin sa kawai sai ya ɗauke ƙafar sa ma.
Sosai Basheer ya maida hankali gun karatun sa,sai da ya kai 10year sannan aka maido sa ya fara karatun boko sai dai bai yi nisa ba ya tsaya saboda rashin kuÉ—i,Bala malam ma da ke taimaka masu shi ma ya tarda wa'adi.
Kuɗin da Adams ya bari su ne aka tattara suka sayi gida,nan Inna ta fara yin ƙananan sana'o'i Basheer na yi mata talla.
A wani yammaci na juma'a, Basheer ya dawo daga talla kamar yadda ya saba.Shigowar sa kenan kawai ya yanke jiki ya faÉ—i,idonsa suka yi sama ya na juya su cikin kuka Inna ta fara jijiga sa sai dai shiru.Adaidaita ta tsayar dan su je asibiti,tun kafin su isa Basheer ya dawo daidai tamkar ba shi ne ya faÉ—i ba.
Ta goge hawaye tace "Basiru mi kake ji" ya kalleta da idonsa da har yanzu ba su ida dawowa daidai ba yace "ban jin komi Inna ,ina ne za mu je?"mai adaidaita ya mayar da akalar tuƙin ya maido su gida a bisa hanya ne ya ke cewa "ina ga fah yaron nan farfaɗiya ce gare sa ba ciwon asibiti ba" Inna tace "yau ne kawai ya taɓa yin haka fah" "to Allah kyauta ya basa lafiya" Inna ta amsa da "amen"kafin ta ja hannun Basheer su shiga gida.
Wunin ranar haka tayi shi babu daÉ—i,sai dai ganin kamar Basheer É—in na cikin walwalar shi ya saka ta É—an ji sanyi.
Kwanaki na tafiya a haka Basheer kullum sai ya faɗi in an ɗauki kamar minti goma sai ya dawo daidai, wannan dalilin ya sa Inna ta fara neman masa magani.Alhamdullah ya ɗan samu sassauci kafin a sannu ya bar faɗuwa,hakan yasa ya koma Maiduguri da karatu duk wata Inna na yi masa aiken kuɗi da wasu abubuwan buƙata.
Ya na ɗan 15years ya sauke alƙur'ani mai girma,zuwa wannan lokaci duk wata halitta ta cikar girman namiji ta bayyana gare shi.
Ranar da ya zo ganin gida a ranar ya ƙara faɗuwa,hankalin Inna in yayi dubu to ya tashi.
Da bincike har ta samu labarin wani mai bayar da magani a ƙauyen LUKA,tsaf ta shirya ita da Basheer suka tafi.
Gidan akwai mutane sosai sai ka kama layi,Basheer ya zauna bisa wani banci can nesa da inda Inna ta zauna cikin wasu mata.
Wata ƴar yarinya ce ba za ta wuce 9years ba,amman a ido sai kace ƴar shekara biyar komi na ta irin na yara.An yi mata kitso dunƙule uku an saka mata duwatsu,da gudu ta nufo inda Basheer ke zaune jikinsa ta faɗa ta na waiwayen bayanta ganin Jumma ta biyo ta.
Basheer ya riƙeta ya na cewa "tsaya mana kin ga kar ki wahalar da Mama" kuka ta fashe da shi ta na ƙanƙame Basheer,Jumma ta ce "ɗan samari dan Allah taimako min to ka kawota daga ɗakin da za'a duba ta ne ta tsera ke,ita ce mu ka kawo ba ta lafiya" Basheer ya miƙe saɓe da Sheera wacce ke ta kuka sam ba ta son a kaita ɗakin da malamin ke duba mutane.
Su na shiga ɗakin kan Basheer ya sara da sauri ya dire Sheera ya na dafe kansa,Mamy dai na duƙe ta na kuka tun bayan da malam ya fara bayanin abinda ke tattare da Sheera.
FaÉ—uwar sa kawai suka ji, Jumma ta riÆ™e Sheera da kyau yayinda ita kuma Mamy ta fita waje."Innalillahi shi ma bai da lafiya ashe"cewar Jumma ta na mai danne Sheera malamin ya saka wani abu cikin bakinta ya na tatso wasu ruwa tsanwa sharrr,malam ya dubi yaronsa yace "je kayi ma wanda ya kawo yaron nan magana,na ga alama abubuwan sa su na da yawa baya ga aljanar da ke jikinsa akwai wani babban al'amari na tambari Æ™ungiyar tsafi " ambaton Æ™ungiyar tsafi ya saka Jumma cewa "wannan É—an yaron shi zai shiga Æ™ungiya oh duniya ta zo Æ™arshe" malam yace "a'a shi ai wannan Æ™arya matsafi akwai ÆOYAYYEN SIRRI (MRS SADAUKI) game da shi ne,ki na ga ta dalilin É—aukar yarinyar nan da yayi duk wata gubar da ke cikin jikinta ta na fitowa za ta samu sauÆ™i nan É—an lokaci" Jumma ta waro ido "kace É—an baiwa ne"ta faÉ—a ta na kallon fuskar Basheer wacce ke É—auke da wani Æ™ato tabon ja wajen kumcin sa na hagu.
"Kar ki fitar da wannan sirrin saboda yin haka tamkar wasa da rayuwar ki ne,duk wani mutumen da yaji wani zancen ƙauyen LUKA to a nan ya ke barin sa balle na wannan yaro" Jumma tayi gum da bakinta,kafin ta shiga goge ma Sheera baki.Lokacin da za ta fita suka yi karo ita da Inna wacce yaron malam ya nemo,haƙuri suka baiwa juna kafin kowa ya fice.