← Book details Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 90

Sashe 23

Dan Achaba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tarhanine yau ina cikin farin ciki" Momy ta faɗa ta na mai shigewa cikin jikinsa,ya rungume ta gam ya na jin son su ita da Ɗan cikin na ɓarka bango da tsokar tsakiyar ƙirjin sa.Damshin hawayenta suka jiƙa rigar sa har yaji ɗumin su,ya ɗan cire ta daga jikinsa ya na kallo kafin ya tambaye ta "minene Tarhani?"ta goge hawaye tace "na tuno da gida ne,mi zai hana mu je tunda yanzu mun samu ƙaruwa ina ga albarkacin sa za su yafe ma" fuskar Daddy tayi baƙi ransa ya ɓace cikin masifa yace "duk ranar da naji kin sake ambaton ko da garin Agadas ne sai na yi maki abinda ba ki taɓa zato ba "ƙuuu ya nufi ɗakinsa ya barta nan tsaye.
Jumma ta ƙaraso ta dafa ta tace "kiyi haƙuri amman jadawalin komawar mu Agadas ba ya nan kusa sai an ɗauki shekaru masu tsayi dan haka ki cire hakan daga zuciyar ki" ta goge ido tace "amman Jumma ai su ɗin iyayena ne,miyasa ba zan je na nemi albarkar su ba?" Jumma tayi wani murmushi wanda ita ɗaya ta san ma'anar sa kafin tace "Uwar ɗakina ke yarinya ce har yanzu ba ki san wa kike aure ba,zuwa AGADAS daidai ya ke da fitar ruhin ki dan haka in ki na son rayuwarki ki cire wannan a ran ki" "haba Jumma ya za ki ce haka?wannan sam bai dace ba"cewar Momy ta na mai yin tafiyarta ɗakin Daddy.
A zaune ta tarar da shi bakin bed ƙugunsa ɗaure da towel alamun ya fito daga wanka ne,ta zauna kusa da shi ta mai ɗora hannunta kan kafaɗar sa tace "Masoyi fushin ya isa haka,ka zo ka ci abinci yau ni na girka ma da kaina"ya sauke ajiyar zuciya ya dubeta wani irin sonta ya ke wanda baki ba zai iya furtawa ba.
Ya laƙace hancinta yace"Allah sa dai yayi daɗi dan an ce mata masu ciki sun fiya sangarta"tayi dariya ta ɗan kishingiɗa kan jikinsa tace "Allah Hubby yayi daɗi sosai ina ga yau sai kayi santi dayawa saboda girkin na daban ne" ya zagaye ƙugunta yace "kenan har kin fi Jumma iya girki?amman kam naji daɗi kice gobe in gayyato abokaina su ci girkin ki?" Ta ɗago da sauri tace "kenan kayi abokai?naji daɗi sosai mijina shi ma yanzu ya na da aboki ba ma ɗaya ba dayawa"

"Kin fiya surutu Tarhani zo ki shirya ni mu je mu ci abincin yau akwai wani meeting da za mu yi"cewar Daddy ya na mai tashi ya nufi drower,Mamy ta isa gun sa ta fara zaɓar masa kayan da zai sa maras nauyi.Tsaf ta shirya sa kafin su fita falo,Jumma na zaune ta baiwa Ahmad abinci a baki.Daddy yayi tsaye ya na kallon yadda Ahmad ke lashe hannun Jumma sai yaji wani kishi ya taso masa,duk ƙoƙarin hana kansa da yayi amman sai da ya tanka "Jumma yanzu abinci kike basa da hannu babu cokali ne?"ta ɗago ta kallesa sam yanzu ba ta iya karantar tunanin AlGabid balle ta ga abinda ke cikin zuciyarsa.
"Shi yace na basa wai nayi masa irin na Bébé "ta bashi amsa cike da ladabi da kuma tsoronsa,ya zo ya ɗauki Ahmad ya kaisa can table à manger kafin yace "daga yau nan za ka rinƙa zaunawa ka ci abinci kaji ko?" Ahmad ya gyaɗa kai yace "to Daddy"shi kuma ya saki murmushi kafin ya cewa Momy"zo kiyi servir ɗin mu " kamar jira take ta zuba masu abincin suka fara ci su biyu a plate ɗaya sai tambayoyi ya ke yiwa Ahmad game da makaranta.

Jumma É—aki ta koma ta na jin haushin yadda ake nuna mata iko ita da ÆŠanta,zuwa can kuma ta sauke ajiyar zuciya tuna yadda suke son Ahmad kamar su suka haife sa.
Kwanciya tayi kan gado,babu jimawa ta fara jin sanyi na ratsa ta kamar wacce aka sa cikin ƙanƙara.Macen nan wacce ta zama abokiyar hirar ta a cikin mafarki ita ta bayyana gare ta, Jumma ta ke dadaɓawa ta na yi mata raɗe a kunne.Tsawon lokaci kafin ta tafiyarta Jumma ta fara barcin ta mai kamar mutuwa,mafarkai barkatai ta ke yi uwanda tamkar alerte ne ake yi mata dangane da abinda zai faru cikin ƴan kwanakin nan.

Su na gama cin abincin Daddy ya ja Ahmad suka wuce É—akinsa,ita kuwa Mamy kallon tv ta fara yi.
Wanka ya yi masa kafin shimfiɗe sa kan bed, Ahmad ya yiwa Daddy ƙuri can idonsa suka fara lumshewa Daddy ya sauke ajiyar zuciya yayinda kwanyar sa ta fara tambayar sa ya fara neman Ahmad tun yanzu koko sai ya ƙara wasu shekaru?
Ya shafi fuskar yaron kafin ya manna masa kiss a goshi,kaya ya canza ya fesa turare ya É—auki makullin motar shi.

"Zan tafi sai na dawo in dare yayi sosai ku rufe ƙofar ɗakin" Daddy ya faɗa kafin ya fice,Mamy tayi masa fatan a dawo lafiya.Daddy ya yiwa mota key ya wuce can inda za su yi meeting ɗin,ƙaton hall ne duk wanda ka gani a nan to Ɗa ne ga ƙungiyar ASOMA.Dukkansu sun saka baƙaƙen kaya kamar yadda tsarin ya ke, Daddy na isa shi ma ya kama layi cikin ƴan uwansa ya suna jiran shugaban ya iso.

Bayan sun gama meeting Daddy ya koma gida,Mamy na barci taji ana shafar cikinta da sauri ta buɗe ido ta zube su kan Daddy.Haka kawai ta samu bakinta da yin addu'o'i,shi kuwa ya ɓata fuska ya na cewa "kamar kin ga wani mugu shine kike wani karanto min addu'o'i?"
Jikinsa ta faÉ—a ta na cewa "mafarki nayi za'a cire min Babyn,wlh in hakan ta faru kashe kaina zan na huta haba ina dalili tun É—azu na ke jin wani abu kamar ana suivre É—ina" jikin Daddy yayi sanyi,shi kuwa bai shirya rasa matar shi ba amman ya san ya zai yi ya shawo lamarin.

Rarrashinta ya fara yi ya na kwantar mata da hankali a haka har barci ya É—auke ta, Daddy ya fita ya shiga É—akin sa.
Gaban madubi ya koma ya na yin suratai can sai wani haske ya bayyana tare da wani hayaƙi,fuskar Daddy a yamutse yace "ya mai girma Shugaba ayi haƙuri na canza Magaji na bayar da Ahmad a matsayin wanda zai gaje ni amman a ƙyale Ɗan cikin matata" ya na gama faɗa ya sunne kai,daga cikin mirror ɗin wata murya tace "amman kaji sarai abinda Demon suka ce, wannan cikin na matar ka barazana zai zama ga ƙungiyar ASOMA,sam babu alkhairi a tattare da shi.Amman babu damuwa za mu karɓi shi namijin matsayin magajin ka in ya kai shekaru goma sha biyu,sannan ka sani daga an haifi yaron cikin matar ka zai zamana cikin kulawar ƙungiya za mu tanadi aljannu wanda za su rinƙa gadin jinjirin har izuwa shekaru 25"
Daddy ya sauke ajiyar zuciya kafin yayi na'am da lamarin, wannan hayaƙin ya fito daga cikin madubi ya shiga jikin Ahmad wanda ke kwance ya na barci.

Bayan kwana biyu Daddy ya gayyato wani babban abokinsa na kasuwanci,sannan kuma ɓangare guda abokin tarayyar aikin jarida.
Sosai Mamy tayi masu girki mai daÉ—i,su na ci su na hirar jaridun da za su buga cikin satinan.Sai Daddy ya lura da irin kallon da abokin nasa ke bin Mamy da shi,ya gimtse fuska saboda akwai shi da kishi sosai.
"Abokina ka dace da mace mai kyau sai dai sam ba ta dace da kai ba,yadda kake mugu in ta sani na san barin ka za ta yi.Amm... nace wai mi ya jawo ra'ayin ka har ka shiga wannan tsarin na ga har Babyn cikin ta ma an ɗora masa matakan tsaro?" Ɗan Jarida Kader ya faɗa ya na kallon Daddy cikin ido wanda ya nuna sam bai gane abinda ya ke nufi ba,Kader ya murmusa yace "za ka iya ɓoye ma kowa ka na cikin ƙungiyar matsafa amman banda ni saboda tun ranar da mu ka fara ganin juna na ga hakan a goshin ka" Daddy ya miƙe yace "dan Allah ko za ka taso mu tafi wani gun"babu muso Kader ya miƙe bayan ya yiwa Mamy sallama Daddy ya ja sa zuwa wani daji.

Suka fito daga mota Daddy yace "na tsani mai surutu a duniya wanda ya mayar da bakinsa tamkar rariya,da ace ka riƙe wannan zancen a zuciyar ka da ba ka jawo ma kan ka mutuwa ba"ya na gama faɗa ya yanki wuyan Kader tuni maƙogoran sa ya fara fitar da jini.
Kader ya riƙe maƙogoron sa ya fara magana dakyar "ka kashe ni amman ka sani mutuwata ita ce farkon rugujewar ƙungiyar ASOMA ta dalilin ka za'a shafeta a jerin ƙungiyoyin duniyar matsafa.Ka sa a ran ka Baba tsoho ba zai taɓa barin ka ba, ƙungiyar BOULE MAGIQUE ita ce ƙungiyar da duk ta gagari kowa amman yau kai ka ci nasarar kashe mumber ta hhhh ina tausayin ka" Daddy ya luma masa wuƙa a ciki yace " in kun haɗe lahira sai ka baiwa shi shugaban naku labarin wa ya kashe ka" Kader ya bushe da dariya yace "ba za ka taɓa ganewa ba sai ranar da na rusa plan ɗin ka,Baba tsoho Aljani ne ba bil'adama ba babu buƙatar sai na gaya masa waye ya kashe ni ( masu son jin taƙaitacen Baba tsoho gami da ƙungiyar BOULE MAGIQUE ta nemi littafin ABINCIN WANI GUBAR WANI🤧)

Daddy ya dawo gida ya na jin har yanzu takaicinsa bai kau ba,hakan yasa ya kira shugan su ya shaida masa komi dangane da abinda yayi.
Wasu dokokin aka ƙara shimfiɗa masa wanda suka kusan saka sa hauka,shi ba wai luwaɗin ne ya ke ma jimame ba a'a yadda Demon ya zaɓi Jumma a matsayin wacce zai rinƙa tarawa da ita.
Ganin bai da mafita ya sa shi yin amfani da maganin barci ya na zuba ma Jumma,in tayi barci sai ya lalaɓa ya biya buƙatar sa wannan shine ya basa kariya game da farmakin da Baba tsoho ke sawa a kai masa.
Ɓangaren Jumma kuwa sam ta ka sa gane kanta,macen da ke zo mata a mafarki ma ta bar zuwa sosai hakan ke damun ta. Ana haka har cikin Mamy ya tsufa,dukkan kulawarta ya dawo kanta.

_____
Chapter 23 · 0% Book details