← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 30

Sashe 9

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Forming line yayi da baki, ya d’ora hannunsa saman nata dake kai komo saman ‘kirjinsa , zare glasses yayi ya d’ora saman littafin “Mata yaron ku d’innan yana caza min kai , na rasa ya zanyi, kina gani ke kika sa baki lallai na barshi ya taho amma daga zuwanshi kiga abinda yayi, ni nasan dama dalilin shed’aniyar yarinyar nan yasa shi cewa lallai ze zo har da yimin qarya! Wai ze zo ne inspecting company!”

Gyara zaman ta tayi saman cinyar sa tare da kwantar da kanta saman kafad’ar sa hucin numfashinta na dukan dokin wuyansa ta furta “afuwa...afuwa yalla’bai na sani Ann be kyauta ba amma be kamata a halin da yake ciki ka tafi ba tare da nuna damuwar ka ba, a halin da ake ciki yanzu addu’ar mu yafi buqata”

Ta d’ago kai, “um kaje ka duba shi idan jikin nasa da sauki ka nusar shi har fad’a ban hana kayi mishi ba, amma banda fushi kaji yalla’bai d’ina”

Ido ya lumshe tare da bata peck saman goshi, har bakin qofa ta raka shi sannan ta zauna saman kujerar daya tashi ta shiga dialling number Bro B.

‘Dakin samarin ya nufa inda ya tarar dashi ya fito daga band’aki d’aure da towel a ‘kugu, tsayawa yayi fuskar nan a had’e, da sauri ya iso gabanshi ya tsugunna a qasa

“Uncle...” hannu ya d’aga masa cikin Kausasa lafazi yace “Anwar komai kake yi kasani ubangiji yana kallon ka, kuma kowa yayi daidai lahirar sa ya gyara.” har ya juya ze fita ya tsaya “kar ka manta wata d’aya kawai na baka mu juya Nigeria tare”

Ido ya wangale “uncle nige..ria?”

“Yes...zan je da kaina wannan lokacin dan da alama abin ya fara fin qarfin ku” da haka ya fita daga d’akin inda ya bar Anwar da tunani.

***

Washegari misalin qarfe sha biyu da rabi aka basu sallama direct gidan gwaggo suka nufa abinka da yaro tuni ta manta da abin da ya faru dan had’uwarsu da munu yasa ta shiga sabgar ta, da dare misalin takwas mu’allim bello ya kawo mata ziyara har da rakiyar sholey da yaje takanas har gida ya d’auko ta duk dan yasa Sam farinciki aikuwa ji tayi tamkar tafi kowa sa’a a duniya yau gata ga munu da gwaggo ga kuma sholey se wuraren tara mu’allim da sholey suka tafi bayan yayo musu shopping da dama.

Bayan wata d’aya

Hasheem ke zaune gaban firstlady Yana prescribing magunguna for Rayya bayan ya gama ya nemi izinin tafiya, har ya tashi tsaye ta fad’o falon kamar wacce aka jefo se haki take

“W..ai..t doctor”

Waiwayo wa yayi ya sauke idonshi saman nata, baki ta turo gaba“kai meyesa ne kullum kullum kake tafiya da wuri” bambarakwai yaji maganar, kallon firstlady yayi ya kuma maida idonsa kanta

Taci gaba “ni ni Allah ka tsaya muyi hira tukunna ” ta shiga sharar qwalla, a fusace firstlady ta daka mata tsawa “ke! Ray...”

Hannu ya d’aga mata ta gefe still idanunsa kan Rayya yace “I’m sorry ma, kina son yauma muyi hirar aboki na ba”ya nuna mata kujera bismillah, diddira qafa ta hau yi, “ni Allah ka dena min hirar wani da ban sani ba, I only knows you and you alone I want to spend the rest of my life with” saurin kallon ta yayi cikin fad’uwar gaba

Sum sum sum ya nemi guri ya zauna without saying a word, hakan yasa firstlady hajiya maryam da muqarrabanta barin falon,
Murmushi me kama da yaqe ya saki had’e dayin qasa qasa da idonsa yace “I’m at your service ma”

Kunya taji ta kare idanunta daga mugun kallon da yake harba mata, yayin da reaction d’inta ke saka hasheem cikin wata duniyar ta daban.

*Bayan wata d’aya*

Malam aminu kano airport ya samu baquncin uncle usman da Anwar, inda Bro B ya taryo su a motar sa zuwa gidansu dake kwairanga road, shigar su befi da awa d’aya ba uncle ya yi shirin fita inda ya nemi rakiyar Bro B.

2:00pm

Ringing d’in da wayar shi ce ta farkar dashi, hannu ya miqa yayi ya d’auki wayar ya qaga a kunne, cikin sleepy voice yace “inaji”

“Tashi kaje sweet heaven high ka d’auko Samira, zan tura maka address d’in da zaka kaita”

Kafin yace wani abu d’if wayar ta mutu, bud’e ido yayi ya kuma duba wayar ganin tabbas uncle d’inne yasa shi tashi ya shiga wanka.

Farar top yasa mara hannu had’e da black three quarter ya feshe jikinsa da turaruka masu tsada sumar kansa da take kwance ya gyara ya d’auka car keys ya fice.

Wayar bello ya kira yana d’agawa yace “Bro B kasa a fad’a ma yarinyar nan kalar mota Ina school premises kar ta wuce 2mins u know I hate waiting” ya katse wayar tare da gyara tsayuwar motar

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(14)

*NOT EDITED *

Tunda security man ya sanar da ita saqon mu’allim bello gabanta ke fad’uwa, tare suka taho da sholey har ta isa jikin motar sannan su kayi sallama, knocking window tayi jin qofar a rufe, shiru ba’a bud’e ba kuma qwanqwasawa tayi jin ba’a bud’e d’in ba yasa ta kara fuskar ta jikin window wai ko zata gano ciki, wur wur take da ido, jiki na rawa jin wani mugun fitsari daya cika mata mara gashi bata son shiga toilet d’in makaranta idonta ya cika da kwalla jin yana neman zubowa , kallon motar ta kuma yi gata dai se huci take amma ba alamun mutum cikin ta, juya wa tayi da niyyar nufar waje dan neman abun hawa, taku biyu zuwa uku taji ance “ke!” Banza tayi dan a tunaninta mazan makarantar ne jin ana ta cewa ke! har sau ba adadi had’e dayin horn yasa ta waiwayo a fusace tana faman matse ‘kafafu

Wani irin bugu qirjinta yayi bazata ta’ba mance wannan fuskar ba ko da cikin mafarki wani nannauyan yawu ta had’iye a qafule ta watsa masa daradaran idanunta dake ta tsiyayar hawaye, komawa yayi cikin motar ya zauna yana qare mata kallo ta side mirrow badan tanaso ba se dan taimakon kanta kar tayi fitsarin wando yasa tayi saurin zuwa ta shiga tun kan ta qarasa rufe qofar ya figi motar su gateman da tsalle aka sha.

Ido ta runtse tun qarfi hannunta bisa handle d’in qofa ta ruqunqume duk tabi ta firgita jin yacce yake manna gudu bisa shimfid’ed’iyar kwaltar sokoto road, qafar nan tata gam take dan qiris take jira fitsarin ya zubo, wani irin giya yaja aiko sam ta qwala qara tun qarfi tare da fad’owa jikinsa ta ruqunqume shi, ita duk a tunanin ta accident su kayi, a hankali ta shiga bud’e ido jin shiru ba ko motsi

Idanunta suka fad’a cikin nashi hancinta dake bisa nashi ta janye da sauri kanta a qasa, “d’agani”

Sassanyar muryarsa ta doki kunnenta, saurin kallon kanta tayi cikin zare idanu ta koma bisa seat d’inta,

“Ke!!!! Fitsari kikayi min!!!!!”

Wani irin bugu qirjinta yayi tamkar ze ‘ballo waje ta shiga kuka wiwi tana sheshsheqa tabbas fitsari tayi kuma a jikin sa innalillahi wa innalillahir raji’un, yau kam tasan wannan mutumin se ya kusan kasheta,

Ji tayi ya ja motar ya kuma tsaya lokaci qanqani ta rikice ganin da tayi sun shigo wani gida murya na rawa tace “dan girman Allah kayi haquri kar kayi min komai wullahi zanyi duk abinda kace” kula da rud’ewar da tayi yasa shi sassauta abinda yayi niyyar yi mata, bud’e qofa yayi ya fita tare da fad’in “biyo ni”

Ciki ba qwari ta bi shi a baya har zuwa wani tafkeken falo me d’auke da kujeru seti biyu, wata qofa ya nuna May da yatsa “shiga ki gyara jikin ki, akwai aerial cikin toilet yanzu zan kawo miki kayannan ki wanke min tass!”

“Uhum”

Yaja tsaki “dirty human being”

~~~~
2 hours later

Parking Bello yayi suka fito se fara’a suke shida uncle, “kaga abinda nake fad’a maka ko?”

“Sosai uncle, nifa abin nan ya d’auren kai kana ganin zata yarda da maganar mu kuwa duba da ta manta abinda ya faru shekara ashirin baya?”

Dariya uncle yayi “yaro yaro ne kai dai zuba ido ka gani,”

“Su kuma su alhaji kabiru fa?...”

Murmushi yayi “they are trapped”

“Ban fahimce ka ba...”

Shigowarsu falon ke da wuya wayar bello tayi qara “gwaggon samira ce” ya furta idonsa bisa uncle,

“‘Daga muji”

Answer wa yayi, suka gaisa tace “dama nace yau ko su sam nayin wani abu ne a school shiru bata dawo ba”

Saurin kallon juna sukayi da uncle, cikin dabur dabur yace “ahh..ahh” uncle ya d’aga masa kai yace “eh nace ta jira na gama aiki ne se nayi dropping d’inta”

“Ayya to shikenan, na yarda da kai bazaka ta’ba barin wani abu ya kusance ta ba”

Girgiza kai yayi hannu a ka yace “insha’Allah nama gama yanzu zan kawo ta”

“Allah ya kawo ku lafiya” ta ajiye, a fusace ya juya zuwa window yaga ali driver na wankin mota, d’akin Anwar suka nufa se de daidai shiga d’akin suka ji an yi atishawa cak suka tsaya, kuma yi akayi har sau uku, da sauri suka fad’a d’akin da suke kyautata zaton anan ne.

Me zasu gani?
Sam!!! Suka furta a tare, “mu...muallimmm sanyiiii” ta fashe da wani irin kuka me cin rai, juyawa yayi ya d’auko bargo cikin wardrobe ya lullu’beta fad’i yake

“Shii shiii, babu abinda ze same ki kinji, trust me Sam, open your eyes please, ya kalli uncle, uncle kar ka bari ta rufe ido pls pls pls Sam say something,” tallafo ta yayi jikinsa yaji taja wani dogon numfashi har sau uku jikinta ya saki

‘Dora ta saman gado, wayar hasheem ya kira yana d’agawa ya fad’a masa tare da ce masa maza yazo yanzu.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(15)

*NOT EDITED*

_afuwa na rashin jina on time_ 🙏
Chapter 9 · 0% Book details