← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 30

Sashe 16

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Atoh a ajiye min da dare ta dumama zanci"

Hanyar kitchen ta nufa, "to bari na shaida mata kuwa" shi kuma ya haye sama.

***
Tsaye yake bayan wata takekiyar daf dake ajiye gefen titi, seda ya gama qarewa samarin kallon tsaf kan ya danna Bluetooth dake maqale cikin kunnen sa, "na gama survey d'in"

Daga can akace "Bello mutanen nan na da mutuqar hatsari, lallai ka kula"

"Doctor insha'Allah zan kula, go and pamper Rayya not me"

Daga ciki yana iya jiyo sautin murmushinsa, "to naji, ka gyara settings d'in glasses d'in?"

"Eh"

"Then you are good to go, take care"

Kai ya d'aga, kan ya tsallaka titin zuwa gurin samarin dake zaune saman dakali.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(22)

Barka yace dasu game da d'aga musu hannu, kallons sukayi duka a kaikice cike da mamakin qarfin gwiwa irin tashi kul da yanda kowa ke shayin zuwa kusa dasu

Cikin kakkausar murya d'ay cikinsu wato oga Nafi'u yace "kai yane?", shafa kansa yayi had'e da kunna Bluetooth dake maqale cikin kunnensa ta yacce ze iya jin maganar da dr ke mishi,

Ya kada baki yace, "ahh sannunku fa, sunana buhari me dabaibayi nazo bautar qasa ne nan makarantar gomnati"

"To se aka yi yaya.." cewar wani cikin zafin rai, hannu oga nafi'u ya d'aga masa, idonshi saman na bello "se aka yaya d'an bautar qasa"

"Ina so ne idan babu damuwa nake zama cikin ku idan ina gida"

Kallon juna sukayi, can d'ayan yace " me ze hana, sede idan ka yarda amma za mu rinqa qaruwa da kai ta wani fannin ko ya"

Kai ya gyad'a "well inhar wannan ne me sauqi ne ai ina d kayan abinci, kayan kallo impact wancan shagon jikin makarantar can nawa ne"

Nan d'ayannan daya d'au zafi ya washe baki da cewa "kai wancan kwftareren shagon, ah lallai mun samu mafaka, ni sunana rody"

Ni kuma "aqilu"

Cikin fara'a d'ayan yace "barka ni sunana salihu"

Jinjina kai yayi, "da fatan zaku riqe ni da hannu biyu ku bani dukkan amanar ku"

Dariya suka kwashe da ita tun qarfi kan wanda aka kira da salihu ya dafa kafad'arshi yace "zo muje abokina"

Ba tare da wani tunani ba ya mara masa baya,suka nufi wani layi, "ina zamuje haka"

"Gidan mu, inaso na nuna wa baba ta yau na samu kalar abokin da take fatan nake huld'a dasu"

_kar ka bishi_ daga cikin Bluetooth doctor ya nemi dakatar dashi, gyaran murya yayi a wayance kan yace "salihu bari naje masallaci wani lokaci maje na gaishesu"

'Dan jimm yayi alamun beji dad'i ba, yace "shikenan ni bari na watso ruwa se mu had'u a can shagon" jinjina kai yayi ya juya ya nufi masallaci,

Bayan an idar da sallah yace da salihu ya jira bari ya zaga band'aki, bayan wani incompleted building ya fake tare da danna wabi button jikin glasses dinsa wanda duk qura idonka baka isa ka gane akwai shi, fuskar hasheem t bayyana ta ciki,
"Buhari me dabaibayi" ya bushe da dariya, dariyar shima yayi, "kayi scanning fuskokin su?"

"Eh, gashinan computer na neman su"

"Aha, bari naje"

"Okay I'll keep you updated"

Direct d'akinsa suka wuce daidai qofar shiga suka had'u dasu, oga nafi'u yace "abokin zamu fita aiki da Allah kad'an sama mana me maiqo odan mun dawo akwai naka kason"

Rody yace "ahh oga kace yau akwai zuwa duniyar sama"

"Wajibul manzil aboki naa" cewar aqilu cikin muryarsa ta riqeqqen d'an daba, gira ya d'aga da cewa dafatan ba zaku wuce goman dare ba dan ina kwanciya da wuri sboda zuwa aiki"

Girgiza kai oga nafi'u yayi had'e da jinjina masa yace "se mun dawo" suka juya a tare, salihu dake baya ya d'ago masa hannu tare da sakar masa murmushi me kama da yaqe jiki a sanyaye, numfashi ya sauke bayan ya rufe qofar da key ya fad'a saman tamusashshiyar katifar dake qasan d'akin yana kuma qarewa shagon kallo game da jinjina kai yana mamakin ta yanda ake mutane ke iya rayuwa a irin wannan area,

Seda ya tabbatar sunyi nisa da anguwar ya fito, ta wata boyeyyiyar hanya yabi dan zuwa gida can ya jangi driver zaune cikin mota ya shiga suka tafi yana shiga ya ciccire kayan jikinsa had'e da qullewa cikin leda, ya kishingid'a jikin leather seat tunanin Sam ya maye gurbin tunaninsa.

***
Hawaye yaci gaba da zuba a idon Ammi yayin d take rungume da Sam a qirjinta, d'ayan hannunta kuma cikin na Anwar, saman kujera ta zauna tare da kuma kwanto da Sam kan cinyarta, shiru tayi kan ta fara magana da cewa

" Alhaji muhammadu ningi shine sunan mahaifin mu ni da qanwata mariya tun ina shekara sha hud'u mariya na sha biyu mahaifiyarmu umma indo Allah yayi mata rasuwa hakan yasa jama'a matsantawa mahaifinmu qarin aure har yakai aka had'ashi da yarinyar kawunsa a cewarsu baze yiwu ya zauna hakanan da yara mata ba,

Ina da kusanci sosai da mariya dan ta d'aukeni ne tamkar umma komai se ta tambaye ni ta keyi har wata ran hakan ke 'bata ran y
Umma ramatu wato matar mahaifin mu, kula da hakan yasa nake takatsantsan, umma ramatu irin mutanen nan ne masu nunawa duniya tamkar su had'iye ka dan so a baya kuma sunfi kowa qinka , sauqin abun d'aya umma ramatu bata fiye zaman gida ba dan se yamma liqis take dawowa daga office inda take aiki a office d'in matar mataimakin governor,

A shekarar dana gama secondary d'an abokin mahaifina ya ganni yace yana so, ba a d'au wani lokaci ba aka aurar dani gareshi ba tare da an duba wai ya kusan haihuwata ba duk da umma ramatu taso cusa wa babanmu ra'ayin hakan 'yan uwansa suka qi kuma Alhamdulillah naci ribar hakan duk da Allah da ya fini sonshi ya kar'bi abinshi se ya barni da gwarazan mazan da zasu sharen hawaye na, (ta shafo sumar Anwar)

Mariya tayi aure a lokacin bello yana da shekara sha biyu a duniya, lokacin Alhaji amin alfalla ya zama Ambassador of nigeria to turkey dan gaba d'aya can muka koma da zama yayin da yara n kawo su nan garin karatu.

Akwai wata rana da bazan manta ba mariya nada shekari goma da aure ta kira ni da daddare take shaida min gobe zataje ningi kamar yacce ta saba tana kai sadakar abinci da suturu ga mabuqata amma tanaji tamkar kada taje, meyasa na tambayeta, tace wullahi yaya inaji tamkar zanyi wani nisan zango ne, dariya nayi mata dan a tunani na shirmenta ne kurum, na kuma ce kada ta sake ta fasa zuwan, to dama gskya tun aurenta nada watanni ta fara fuskantar qalubale daga dangin mijinta har takai wani lokacin ta nemi tahowa turkey na bata baki,

Barrister usman kuwa qanin mijina ne ubansu d'aya, nice na had'asu da maiqasa ganin yana neman lawyer da ze danqawa amanar wills d'inshi,

Ranar da mariya ta 'bace a ranar na dira a nigeria dan duba mahaifina Allah barshi n qarasa kano na duba qanwata se mugun labari ya riske ni, gidan da ban samu zuw kenan ba na tafi kano, tun muna saka ran Allah ze bayyana ta har kwanaki suka shura aka tafi wata uku,

Labarin rashin lafiyar me gidana yasa ni koma wa turkey inda isata asibiti keda wuya na tarar da gawar mijina wanda akayi poisoning a abinci, ranar nayi kuka tamkar zan mutu har ta kaini ga kwanciya a asibitin tsawon wata guda

Duk abinnan dake faruwa ban yarda an sanar wa da yara ba, ni da kaina dana samu lafiya na tattara komai nawa na komo nan se da na tabbatar sunzo gurina hutu na fad'a musu zancen da har yau idan na tuna nake jin ba dad'i dan ni da kaina nasan ban kyauta musu ba ko ba komai zasu so ganin gawar mahaifin su. (Nan ma girgiza mata kai Anwar yayi tare da sa hannu ya share mata hawaye)

Wannan shine gskyar labarin mu ni da 'yar uwata mariya, rasuwar mahaifinki kuwa barrister ne firr ya hanani zuwa, wanda bana ce ga dalilin hakan ba se de abinda na sani baze ta'ba yin abin da yasan be kamace ni ba"

_kuyi manage da wannan insha'Allah zuwa anjima zaku sake jina_ son so🥰

©️Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(23)

_this whole page is for you my wattpadians_ 💖

_jiddatul khair😍 thanks for your immense support_ 😘


..hannu tasa ta share hawayen dake fita a idon sam ta d'ora da cewa "samira yanzu da Allah ya kawo ki garemu bazan kuma yarda ki bar ni ba, kece zaki maye min gurbin 'yaruwa ta a fuskarki zan rinqa ganin mariya ta, taja hanci tare da kamo hannun Anwar, insha'Allah bazaki kuma shedding tears ba while we are alive, Anwar is your brother and bello ma haka wic is younger to Anwar,

Sam i never thought kece wacce suke kulawa da ita, but daga yanda naji labarin ki a bakin barrister yasa ni tausaya miki na kuma sa yarana lallai su taya uncle d'insu fighting dan wannan case d'in is not just for his carrier is a big goal in his own life and theirs,

Ta kalli Anwar kan a kuma maida idonta kan Sam, "kiyi hakuri da maganganu na, na sani sunyi miki tsauri da nauyi a yanayin shekarun ki, but i know my baby has a deep understanding, kar ki ta'ba bari wani abu daga maganata ya ta'ba ki, kada ki damu kwatakwata i'm with you, your brothers are, uhm?" Ta qarashe da sigar tambaya,

Jijjiga kai Sam tayi tare da dad'a ruqunqume Ammi cikin sanyin muryar kuka tace "i'm so happy Ammi, yau is one of the best days in my whole life, yanzu saura abu biyu buri na ya cika"

"Abu biyu" suka kalli juna Ammi da Anwar
Chapter 16 · 0% Book details