← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 30

Sashe 15

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suka isa garin minna, inda ya umarci driver da ya kaisu inda zasu samu makwanci yace masa wullahi iykar sa da minna tasha, gudun haduwa da yan sanda kada su kamashi a cewarsa,
"Ba matsala idan kaga taxi ka tsayar mana se muje da ita"
Hakan kuw akayi, dattijo ne me taxi din banda shegen surutu babu abinda yake ga wani d'an banzan kllo da yake wa Sam ta mirror, duk jinta take a takure, ta rinqa jan hijabinta ita a lallai se ta dad'a sakaya jikinta dan tamkar yana kallonta tsirara take ji "wannan wani irin bala'ine" munu da ta kula tace, surin girgiza mata kai Sam tayi alamar tayi shiru, ta gefen ido ta kalli Anwar daya toshe idonsa da baqin gilashi tayi da alama bema san abinda ke wakana ba, har gaban wani tangamemen hotel ya kaisu inda Anwar yayi masa kyakkyawar sallama har sun sauka sun fara tafiya ya tsaida me taxi d'in da cewar akwai ragowan kaya, se da ya tabbatar ya shigar dasu reception ya dawo se de da zuwansa ya bud'e qofar tare da janyo mutumin da hannu ya kai mishi kyakkyawan naushi har se da bakinsa yayi jini

"Malam lafiya zaka doke ni"

"Uban wa ya baka damar kallon mini mata, daka samu ma ban faffasa maka jiki ba! Get out of my side gara kawai"

Ai kan kace meye wannan wuf ya fad'a mota ya tafi, anwar ya juya cikin hotel d'in rai 'bace, ba tare daya kalli gefen su ba yace "muje" a d'arare suka bi bayanshi dan sauri kamar zasu kifa.

VIP room ya kama musu guda biyu ko wanne ciki da falo, se da ya rakasu har d'akin ya shiga y dudduba sannan ya ansa key ya basu bayan ya nuna musu nashi dake gefen nasu sannan ya tafi nemar musu abinda zasu ci.

*Birmingham U.K*

"Ah ah hajar wannan kayan da kike had'awa fa" cewar Ammi data leqo dan kiran ta suci dinner, hannu tasa ta kare idonta "Ammi dama d'azu ne barrister ya kirani yace na shirya kayana ze turo min da kud'in tafiya nigeria"

"Zaman ya kama shi kenan?"

"Eh haka yace ze kwana biyu, ni wlh har na fara kewar ki" tace game da shagwa'be fuska,

Hararar wasa ammi tayi mata "kyaji dashi ja'ira, ni taso muci abinci bansan gulma"

Ta bud'e fuska tana dariya tare da miqewa tace "Ammi me muka samu"

"Abinda kika ce d'ana na kwad'ayi"

"Cowleg" ta furta ido waje har da d'an tsallenta ta mara mata baya.

***
Tun da yayi sallar asubahi ya nufi cafe din cikin hotel d'in cikin qoqarin tura saqo ta yanar gizo wato mail amma firr yaqi tafiya, wayar hashim ya kira bugun farko kuwa ya d'aga
"Duk wani d'an iska ya biyo bayanka"
"Tun da ka same ni a tsakiyar 'yan kan titi ba" ya bashi amsa, dariya hashim yayi suka gaisa cike da annashuwa yana tambayar jikinsa,

Yace "Ya akayi kasan nine"
"A halin da ake ciki yanzu duk baquwar number",

Girgiza kai yayi yace "doctor wani taimako nake so kayi min"
"Me kake so dani?"

"Zan turo maka saqo ta mail da inda zaka tura min yanzu pls"
"That is only if you tell me your whereabouts?"

Gashin kansa ya shafo had'e da murza goshinsa yace "sai ka jini" ya katse wayar cike da tunaninka, ya san hashim for a lifetime, baze ta'ba barin ko quda ya cutar dashi ba se de a yanayin da ake ciki yanzu idan aka cire Ammi da bello bayajin akwai wanda ze yarda dashi.

Qarar da wayarsa tayi yasa shi dawowa daga duniyar tunanin daya fad'a

_Reply "done" from doctor_

Murmusawa yayi, ya tashi ya shiga restaurants d'in kusa dashi ya kar'bo breakfast d'in da yayi musu order, knocking yayi bisa door,
"Waye" munu ta tambaya

Cike da jin dad'in yacce ta tambayar yace"nine" bud'ewa tayi fuskarta d'auke da fara'a "ina kwana Bro A"

"Lafiya" yace tare da handing mata leather bag d'in ya juya, har yayi taku biyu ya juyo zata rufe yace "wait, ina d'ayar take?"

"Sallah take" tace a duburburce, gyad'a kai yayi badan ya yarda ba ta kuma cewa "sallar walaha"

"Uhumm" kawai yace tare da d'aga girar sama ya tafi.

Rufe qofar tayi tana me hamdala da be gano taba, ta ajiye ledar bisa table cikin d'aga murya tace "se ki fito dodon naki ya tafi"

Sam dake bayan curtains ta fito hannu a saman qirji tana maida numfashi tamkar wacce tayi tsere
"Ke lafiyarki" munu ta tambayeta
"Baki ga abinda ya faru bane??"
Munu ta kyabe baki tana fad'in "eh naga de kin 'buya bayan curtains sbda kar bro A ya ganki... sbda yana cinye mutane..ko?"

Guntun tsuka tayi "ke dalla nifa tsoron wannan manyan idanun nasa nake bawai...."

Dariya munu tayi "ke da shi maga wanda yafi wani ido"

Turo baki tayi "tabb wlh gara nawa kina ganin nashi kamar na mujiya gashi yayi ta wani lumshe su kamar me jin bacci"

"Ehhh lallai har kin manta warning d'in daya kafa miki jiya ko, maza ya jiki, ni dai taho muci abinci dan yinwa nake ji"

Dad'a cuno bakin tayi ba tare da tace komai ba ta hau bud'e pack din abincin.

Anwar da ke tsaye jikin qofar ya ji duk dramer da suke ya girgiza kai wato 'buyar mishi tayi, sbda idanunsa irin na mujiya ko? Zaki sani ne ya furta a fili.

3 weeks later

Dawowar Ammi kenan daga raka mom hajar airport ko parking mota batayi ba wayar ta ta shiga qara alamun kira, d'agawa tayi had'e da yin sallama, aka ansa

"Ann! Kaine? Inaka shiga hakane na dena samunka " tace a rikice

"Ammi na lafiya ta qalau, inason fad'a miki ne ma in 3 days time zaki ganni, idan nazo zan fad'a miki duk abinda kike son ji, we wil talk later i love you"

Tun kan ta samu sukunin amsa shi ya katse wayar se qarar message taji

_reply "ammi kar ki sanar da kowa ina hanya, ki d'auki kayanki kije quarters d'in AB machinery zan same ki a can. Take care_

Tunani kala kala ta tsinci kanta dayi se de ta barwa kanta cewa anything has a reason baze ta'ba yin abu haka kurum ba.

Ranar wata laraba misalin 3:30pm tayi musu cikin tafkeken kamfanin AB machinery ginin da idan ka shige shi zaka zata sace ka akayi, katangar sa kad'ai abar kallo ce me tsayin gaske ce ainun, ko ina cikin wurin zagaye yake da qayatattun flowers masu fidda qamshin dad'i ko ina ka kalla mutane ne birjik sanye da kaya kala d'aya wato blue colur daga bayan su tamfkeken A da B ne a had'e, duk inda motar da suke ciki ta wuce se kaga ana tafi fuskokin mutanen da kallo d'aya zakayi musu kasan turawa ne manne da murmushi wasu kuma dariya kai kan gani kasan farinciki suke,

Maida idonta tayi inda yake tare da waro ido waje, dama yana fara'a haka? Hannu tasa ta dad'a murza ido wai kode mafarki take ganin tabbas d'in hakane yasa ta kuma leqawa ta kusurwar kujera inda har ta iya hango lotsawar man pride d'insa,

Iska ce me d'umi ta doki spot d'in wuyansa har besan lokacin daya lumshe ido ya bud'e a hankali ba, jin abin na neman kashe masa ga'bo'bin jiki yasa shi waigowa a hankali sede tsayawar da motar tayi yayi daidai da komawar ta jikin window dan qarasa kashe kwarkwatar idonta

"Sir mun qaraso" maganar driver ya d'au hankalinsa, daidai lokacin da yake shaqar wani ni'imtaccen qamshi, umartar sa yayi daya shigo da kayan shi kuma ya sauka ya tafi, ganin haka ta bud'e qofa tare da kamo hannun munu suka fito duk da son kalle kallen su basu samu daman yin hakan ba gudun kada ya 'bacewa ganinsu

Gaban wata tafkekiyar wooden door suka tarar dashi tsaye yana danna door bell, wata baqar fata ce ta bud'e qofar tare da rissinawa

"Welcome back sir"

Be amsa ta ba ya wuce bayan tayi gaggawar kaucewa, suma suka bi bayan nashi tamkar jela,

"Ammi na" ya furta cikin d'aga murya a lokacin daya dudduba d'akunan gidan

Cikin gigin bacci ta daddafa ta fito, sama ta nufa kasancewar tana underground apartment, kiran sunanta da ya kuma yi ne yasa ta yin saurin haura benan

"Ann my son" ta furta in a shaky voice wanda tuni hawaye suka hau ziraro mata, waigowar da zeyi ya hango ta tsaye da sauri ya isa gareta ya rungumeta dan yayi kewar Ammin nasa sosai

"Ammi na" ya furta a hankali, sun jima a haka kan munu tayi gyaran murya game da fad'in "ina wuni", share hawayen tayi da hannu ta d'ago kai a hankali, ta amsa musu tare da qare musu kallo

A nutse ta tako zuwa inda suke tana me dad'a fad'ad'a fara'arta tasa hannayenta ta shafo kawunan su dake sakaye cikin hijabi tace "sannun ku da zuwa yara na" hannu tasa ta d'ago ha'bar Sam tana kallon cikin qwayar idanunta, a hankali tace

"Samira"

Game da fashewa da kuka me tsanani wanda ya rud'asu duka, "Ammi ammi na lafiya me ya faru"

Ita kuwa samira baya tayi had'e da sakin kuka wurjanjan, munu ta shiga bata baki yayin da Anwar ke lalla'ba mahaifiyarsa

Hajjo wato Ammi ta d'ago tare da janyo samira ta rungume, idonta cikin na Anwar take cewa
"She's her mothers child, she looks exactly like her, she's mariya's photocopy" ta qarashe maganar cikin hawaye had'e da fara'a

"K..in..sa..n mummy na?"

Lumshe ido Ammi tayi

"'yar uwa tace ta jini.."

***
A can gida nigeria kuwa uncle ya rasa gane kan bro B, gashi baya barin d'akinsa a bud'e , motar sa kuwa ta jima da barin gidan, kamar ko yaushe dawowarsa daga office kenan ya tararda gwaggo zaune a falo tana kallon labarai

"A a barrister kaine haka da rana tsaka"

"Wullahi fa yau Alhamdulillh aikin namu da sauqi" ya zauna saman kujera suka gaisa tace, " to madalla sannu bari na samo maka ruwa kan a qarasa abincin yau munyi ranar abinci"

"Ai barshi gwaggo nagode, yanzu wani abokina da matarsa suka matsa seda naci a gidan su"

"Ai kuwa yau abincin ka tayi tuwo da miyar agushi me tantaqwashi"
Chapter 15 · 0% Book details