← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 30

Sashe 22

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nafi'u ya daka musu tsawa, "dalla malamai bama san burr*uba, taya muna cikin wannan halin kuke neman yi mana hauka, wlh dan na katse muku rayuwa yanzu ba matsala bace a wurina, shashashai"

"Oga na rantse da kabarin tsohona wannan shegiya ce, ba kiga yanda ya zama qawar corper ranan ba, he is the one that told him our secret, na tabbata" cewar rody

"Kai dalla ware qasurgumin kafiri," salihu yace cikin zare idanu, kan su kuma cewa komai bello da bashari suka bayyana a gaban cell d'in

Bro b yayi smirking game da tafa hannu, duk suka maido hankalinsu gareshi, cikin had'e rai yace "ku dena zargin d'anuwanku domin ni da kaina na gano kud'in su waye tun kafin nazo gare ku.."

Dss bashari ya d'ora da cewa "and again idan kuka bari na qarajin muryarku sena sa an datse muku mafitsara"

One sided murmushi bro B yayi suka bar wurin dan dama suna tattaunawa ne suka jiyo hayaniyar su,

***
Washegari

Gwaggo tace "hajar zaki iya fitar nan kuwa? Ko cikin ne mu tafi asibiti?"

Girgiza kai tayi fuskarta kadaran kadahan, tace "a a gwaggo karki damu muje zan iya"

Hannunta gwaggo ta kama suka shiga motar bello dake tsaye yana jiran su, ba wanda yace da wani uffan tun bayan gaishesu da yayi,

"Ni kuwa bello lafiyar ka lau kuwa naga duk ka fad'a"

'Dan kallonta yayi cikin murmushi kan ya maida kansa titi yace "bakomai gwaggo kawai aiki ne da ya sakani gaba"

"Ashsha shiyasa baka zama gida sosai, Allah ya dafa maka"

"Ameen gwaggo, nayi kewar addu'oin ki"

"Haba ai babu ranar da zan d'ora goshina a aqasa batare da na sakoku a addu'ata ba, Allah de yayi muki albarka"

"Ameeen" yaja word d'in dai dai lokacin ya juya akalar motar zuwa state road,

"Wash wash wash bayana"

A firgice gwaggo ta waiwaya ganin yacce mom hajar ke botsare botsare ga gumi na karyo mata tako ina yasa ta cewa "bello inaga mu fara zuwa asibiti da alama haihuwa ce"

"Wayyo gwaggo bayana, wayyo...dan Allah ku kira min bar..ris..ter"

***

'Dakin haihuwa aka shiga da ita, yayin da bello ya fita zuwa gida ya d'auko kayan da ta had'a dan zuwan wannan rana, be jima da kawo kayan ba ya fita ya taho da uncle, dan be fita da mota ba, gwaggo kuwa ta kasa zaune ta kasa tsaye dan tana iya jiyo ihu da salatin da take.

Wucewar awa biyu kukan jinjiri ya karad'e harabar, ba a jima ba aka fito da baby nad'e cikin shawul,

Cikin zubar qwalla gwaggo ta rungume shi a jikinta daidai lokacin da su uncle suka shigo, babyn bello ya kar'ba dan uncle d'akin da take kwance ya shiga dan duba lafiyar matarsa,

"Gwaggo ki kalla kamarta d'aya da uncle sak"

Kai ta jinjina, bari na gano lafiyar ta" kan ta rufe baki uncle ya fito a rud'e yace "hajar is no where to be found"

"Kamar yaya?" Cewar gwaggo, kan ta fad'a d'akin a rud'e, har labule ta d'aga babu alamunta, daidai lokacin uncle ya umarci bello ya kira 'yan sanda dake kusa yanzu.

***

Yatsa tasa ta d'auke hawayen idonta, game da kauda kai gefe,

Hannu yasa ya riqo hannunta yace "Ammi.."

Murmushi tayi "Ann rabona da garin nan tun lokacin da mariya ta 'bata" taja numfashi

Tapping hannunta yay, ta kwanto da kanta saman kafad'arshi a hankali ta furta "nayi kewarta sosai"

Smiling yayi tunawa da wayar su da bello kwana biyu da suka wuce.

"Government house" tayi pronouncing a fili, kai ya d'aga yace "Ammi pls do me a favor"

Kallon meyasa ta mishi, murmushi yayi "duk tambayar da zaki yi zaki samu amsar ta idan muka qarasa ciki" waya ya zaro a aljihu ya kira layin Bro B har sau uku be d'aga ba kasancewar ya barta cikin mota ya shiga police station.

Hasheem ya kira, ya sanar dashi suna waje yace gashinan zuwa,

Kan ya qarasa rufe baki yaji d'iff wayar ta mutu, ba sufi minti uku a wurin ba ya iso, Ammi ya gaida cike da farinciki"

fad'awa yayi jikin Anwar game da fashewa da kuka,

"I missed you, how have you been?"

'Dago shi yay "I'm fine, kamanta ina tare da Ammi" kai hasheem ya jinjina cikin share qwalla yace "lets go in"

Cikin motar suka koma driver yaja su cikin gidan gomnatin, cikin babban falon baqi suka shiga

"Ammi bismillah, yanzu ze fito"

Gaza riqe mamakinta tayi tace "hasheem wai meke faruwa ne, me muke yi anan kuma wanene ze fito? Ina bello?"

Kallon juna Anwar da hasheem su kayi kan su kai ga yin magana sallamar da akayi ta ja hankulansu suka amsa daidai lokacin data juyo da niyyar ansawa sukayi ido hud'u,

Ido ta zuba masa tamkar me son karanto wani abu a jikinsa a hankali tace

"Jamilu mainasara?"

"Hajjo dafatan kina lafiya"

"Kunsan juna ne?" Anwar ya tambaya cikin rawar murya

Numfashi ya sauke , "ita d'in 'yar uwace ga matata"

"Matar ka?" Ta kuma tambaya cikin mamakin da yaqi sakinta

Murmushi yayi me kamar yaqe "matata wacce kuke mahaifi d'aya"

Ido waje tace "kana nufin sadiyar inna ramatu?"

Kai ya jinjina game da miqawa Anwar hannu "the great CEO AB machinery"

Shaking hannu sukayi, "ya akayi hakan ta faru? Kuma a ina ka gano su dan iya sanina har mahaifinmu ya rasu ba a samu gurin da suke ba" Ammin tayi adding

"Duk zan warware miki zare da abawa amma zanso mu fara dubo halin da patients d'inmu suke ciki, bismillah"

Jiki a salu'be suka mara masa baya zuwa wani d'aki, da isar su jikin Ammi ya hau rawa da ta qarasa bakin gadon kuwa yanke jiki tayi ta fad'i..

©️Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(28)

"Ammi!" Suka yo kanta a rud'e, ruwan dispenser hasheem ya tsiyayo cimin cup Anwar ya rinqa shafa mata samn fuska zuwa wuya, cikin hikimar ubangiji ta farka bakinta d'auke da sunan "mariya.." tashi tayi ta tsugunna setin fuskar ta, tasa hannu tana shafawa had'e da fashewa da kuka,

"Yanzu wani mara imanin ne ya maida ki haka? Shine yanzu ina ribar take ? Innalilllahi wa inna'ilaihir rajiun"

Kafad'unta ya riqo cikin kwantar da murya yace "Ammi ki bar kuka dan Allah mummy zata samu lafiya insha'Allah, ai duk wanda yaci zalin wani Allah ba ya barinshi, a yanzu haka mutanen da suka yi mata haka suna hannun hukuma, yanzu haka dalilin zuwan mu garinnan me girma gwamna ya nemi presence d'inmu dan warware abinda ya jima a rufe kamar yacce yace"

With cold eyes ta kalli governor "jamilu who is behind all this?"

*
"Doctor i'm sorry to say dole zamu rufe asibitin nan har zuwa mu gama binciken mu, Alhaji kai kuma inaso kayi hakuri kje gida da jaririna nema masa abinci , ku saka mishi ankwa muje"

"Wannn shine laifin banjiba ban gani ba, nashiga uku" cewar d'aya a ciki nurses d'in asibitin,
"Ku dakata yalla'bai"

Juyowa yayi "yes"

"Amm i think i know where she is"

Kallon kallo akayi, kan ya nuna mata hanya alamun muje to, nurse da doctor suna motar yan sanda yayin da bello a motar sa shi, uncle da kuma gwaggo ne se jinjirin dake hannun gwaggo.

Tafiyar minti qalilan ya kaisu doctors quarters qwanqwasa qofa tayi daka ciki aka ansa da cewa ana zuwa,

Wata dattijuwar mace ce da bazata wuce 50-60 b ta bud'e baki ta hangame, nurse d'in ta girgiza mata kai, kaucewa tayi gefe suka shiga,

'Daki nurse d'in ta shiga zuwa can ta fito hannunta riqe da mom hajar dake ciccije baki saboda ciwon jiki,

Sairin miqewa uncle yayi ya nufo ta, "bawan Allah kada ka ta'ba ta dan kuwa kai d'in azzalumi ne!"

Maganar nurse d'in ta razana zuqatan kafatanin mutanen dake falon, "sister nasira kinsan me kike cewa kuwa?" Doctor yace a tsawace,

Idonta ta sauke bisa fuskar mom hajar tace "d'azu bayan an tafi goge baby _turo d'an teburin allura nayi zuwa bakin gadon da take, sannu nayi mata, na shiga zuqo ruwan allura d zummar nayi mata naji an riqo hannuna "kina buqatar wani taimako ne ko wani na damunki?" Girgiza kai tayi "inaso ne ki cece ni" "na cece ki" nayi mumushi kawai dan a tunani na ba'akan cikin hankalinta take ba, tsikara mata allura nayi bayan nagama dubata na juya zan fita ta riqo hannuna, "idan ban gudu daga nan ba kasheni zasu yi", "suwa?" , "mutanen da suka kawo ni, mijina d'an yankan kai ne, jira yake na haihu ya kashe ni saboda wai amfani na ya qare a wurinsa", "let me call the police", hanani tayi a cewarta megidan nata nada mutuqar hatsari na bari ta bar asibitin idan ta samu lafiya se nayi reporting, shine dalilin daya sa nayi snicking out da ita na kawo ta gidana_ wannan mahaifiyata ce dana ce tayi mata wanka kan na dawo musan abinyi,

Qasa uncle ya durqushe, baki bud'e, gwaggo kuwa salati take da sallallami nan bello yayi musu bayanin yacce suke da ita har da irin sana'ar uncle d'in haquri aka bawa juna doctor da yansanda suka tafi, gwaggo ta matsa kusa da ita

"Hajar a d'an zaman da mukayi zan iya rantsewa kina da hujjar yin wannan qaryar, sede ki sani qarya ba abar wasa bace tun bare irin wannan qazafin, bakya gudun abinda zeje yazo bare yanzu yanda duniyar take, 'barayi, kidnappers, masu garkuwa da mutane duk neman sunake ido rufe! Meyasa meye dalilin ki na yin hakan?"

Kukane ya kufce mata me cin rai kan tace "na rantse da Allah gwaggo ba nayi haka bane dan cin zarafin barrister se dan kunyar abinda na aikata masa"

Jimm gwaggo tayi kan ta kalli barrister dake tsugunne idonsa a kan hajar tace "shikenan inaga ya dace muje gida a qarasa maganar nan, ungo babyn nan kayi mata addu'a"

A salu'be yasa hannu ya kar'beta "sedai ba dabino" yace

"Kash kaga kuwa mantawa mu kayi ba mu saka ba"

"Karki damu hajiya inada zamzam bari na kawo"

"Ah zam zam? Dama ana iy amfani dashi madadin dabino?" Cewar gwaggo
Chapter 22 · 0% Book details