← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 30

Sashe 29

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bro A kazo inji Ammi" daga nesa ta jiyo muryar bro B yana qwalo kiran, daqyar ta iya seta kanta tare da qoqarin d'ago kanshi, "ana kiran ka" tace cikin dashashshiyar murya, idanunsa da suka canza launi ya bud'e cikin nata har tana iya hango kwantacciyar qwalla daga ciki, dad'a lumshe ido yayi game da fad'in "i need you, pls ki tallafeni" gani tayi hawaye na biyo fuskar sa ba qaramin tashin hankali ta shiga ba har bata san lokacin data tallafo fuskarsa ba
Tace "dan Allah ka dena kuka, zanyi maka duk abinda kake so kar Allah yayi fushi dani kaji"
One sided murmushi yayi "wane yace miki haka?"
"Gwaggo, tace idan har kace nayi maka abu naqi se Allah yayi fushi dani"
Jimm ya d'anyi kan yace "sa kayan ki kizo muje wurin Ammi "
"Ammi?" Ta tambaya
"Yeah, kinji dai abinda gwaggo tace miki ko?" Ta d'aga kai "to maza shirya kizo kiji wata magana"

Nodding tayi, ta shiga closet d'in Ammi tasa kayanta, sannan ta qarashe drying kanta, kula da cewa bata shafa mai ba se da yasa ta tu'be ya mulketa wanda ya d'auke su kusa rabin awa har seda ta fara yi masa kukan shagwa'ba, se da su kayi sallar isha suka fito falon.

8:00pm

Jero wa suka yi har gaban dining table inda kowa ke zaune ana kwasar dinner ya ja mata kujerar kusa da bello ta zauna ya zauna opposite tata, tashi tayi ta zuzzuba musu suka fara ci ba tare da sunce uffan ba, d'ago kai yayi yaga kowa ya maida hankali kan abinci, gyara zama yayi game da miqe qafa ya zira ta ciki qarqashin teburin seda ya tabbatar ya ta'bo qafarta har ta d'an kallo shi, yayi murmushi

Ya shiga yi mata tafiyar tsutsa a sangalelen ta, sede bisa mamakin sa ko kallo be isheta ba, sema dariya da take ita da munu yatsu ya had'e guri d'aya da niyyar mintsininta yaji qafa baibaye da gashi saurin maida idonsa yayi qasan table me ze gani, bello ya kalla yaga ya d'aga masa gira game da murmushi, haushi yasa shi kicking qafar har se da bello yayi ihu, ya miqe rai 'bace ze bar wurin Ammi

tace "Ann samu wuri inason magana da ku"

Zama yayi a salu'be tace "munyi magana da 'yanuwana nan da sati biyu zamu miqa maka matarka dan baze yiwu ku rinqa yi mana rashin kunya a gida ba, and again za'a daura auren bello da mubina (munu) a ranar asabar d'innan me zuwa..." bata kai ga qarasa maganar ba wayarta tayi qara, da hannu tayi musu alamar tana zuwa, qaga wayar a kunnenta ke da wuya ta sake ta game da yin salati...

"Allah ya yiwa maryam rasuwa"

©️Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(34)
Rud'ewa falon yayi da koke×2, an rasa me lallashin wani 'yan mazan ne sukayi qoqarin basu baki, wayar sa dake haske ya d'aga ganin sunan hasheem yasa shi saurin picking daga can yace
"Dagaske ne abinda nake ji?"
"Yea...ina matar ka?"
"Gamu a asibiti bata san wanda ke kanta ba"
"Ka kula da ita bari naje na samar mana ticket"
Sallama sukayi, gaban Ammi ya qarasa ya shaida mata fitar sa, nan ya bar bello wurin su.

***
Bayan kwana hud'u

~Uncle ne ya tarbesu a airport d'in malam amin kano inda ya wuce dasu direct zuwa gidan gomnati dan can ake zaman makokin.

Da isar su wuri ya kuma hautsinewa ganin Rayya kowa se gaisuwa ake musu, duk wani mahaluqin dake gidan se ya zubda hawaye idan ya kalli jamilu mainasara, duk ya rame ya qojale ya fita hayyacinsa to abune ya had'e masa ga abinda ya had'asu da Maryam, ga rashin d'iyarsa tilo data za'bi tabi mijinta ga musibar mutan gari da kullum ke yada mishi magana kan cewar ya zalunci matarsa cikin qaryayyakin da ake yad'awa ma har cewa akayi kamashi tayi da 'yar uwarta, yanzu haka yafi sati biyu kwance ba lafiya .

Hasheem ne zaune gefen kanta hannunsa cikin nata ta hanashi matsawa ko can da nan, kusa da su Sam da munu ne sunyi jugum×2 su Ammi na can main parlor tare da manyan baqi dake zuwar musu gaisuwa daka gari×2,

Da taimakon Allah da ma'aiki aka tashi zaman makoki lafiya, kwanan su biyu da zuwa aka je can family house d'in gidan baban su munu aka d'aura aurenta da bello bisa sadaki naira dubu d'ari biyar bisa waliccin qanin mahaifinta commissioner of agriculture Alh sabe doguwa,

Duk wani abinda ya dace na al'ada anyi shi na daga zaman makokin hajiya maryam, duk wannan zama da ake Rayya taqi yarda ta had'u da mahaifinta duk ko da qoqarin da yake na ganin hakan ya faru, ko jin muryarsa tayi yanzu zata bar wurin, kasancewar rashin lafiyarta yasa su mummyn Sam suke lalla'bata sai de a ranar da suka cika sati uku aka sa hasheem ya kawo ta a zauna,

A babban falon sirri na jamilu mainasara suka taru Ammi, mummyn Sam, gwaggo, mom hajar, barr, da me girma gomna ke zaune saman kujera yayin da duka yaran ke zaune qasa, Sam kusa da qafar mummyn ta, munu kusa da gwaggo yayin da hasheem, Anwar, bello ke jere a gefe d'aya, Rayya kuma na kwance gefen Ammi se ka rantse bacci take amma idonta biyu hasali ma hawaye ke zuba a idonta
"Da sunan Allah me rahma me jinqai, me bayarwa me amshewa, na tara ku anan ne ba dan komai ba se dan ku tayani bawa d'iyata ha'kuri ku kuma tambayar min ita shin meye laifina a gareta? Mahaifana a late yanzu matata ma haka and wacce kawai zan kalla naji sanyi ta juya min baya, a yanzu ita kad'ai ce dangi na amma duk yadda naso ta saurareni abin yaci tura, to shine nake so ku taimaka min kuyi mata magana wataqil ku ta amsa ku"

"La'haila ha ilallahu yau naga yaran zamani, ke rayya maza tashi zaune" cewar gwaggo tana tafa hannuwa,

Ammi rai 'bace tace "haba jamilu 'yar cikinka ta gagare ka tanqwasuwa,..ke yanzu ba se anjima ba ki nemi gafarar mahaifinki! Yanzun nan!" Taqarashe a tsawace,

Ajiyar zuci ta yi kan ta tashi zaune ta waiwaya sashen da suke cikin zubar hawaye tace "ku min afuwa iyayena na wlh ba ina yin haka bane dan na quntata ma mahaifina se dai na gaza sake wa ne saboda illar da mahaifiyata ta yi masa, a kullum na ganshi se mahaifiyata ta fad'o min, ku yafe min daddy" ta tashi ta je ta tsugunna kusa da qafarsa, "daddy i'm very sorry ka yafe min...and pls ka yafe ma mummy na.." tayi adding cikin zubar hawaye,

Hannu ya d'ora saman kanta ya shafo, "ba kiyi min laifin komai ba Rayya, tsorona be wuce laifin da nayi miki ba abinda kika fad'a yanzu kuma ko waye a matsayinki abinda ze yi kenan, na yafe miki and pls be open to me banason shiru shirun nan da kike yi min uhm?"

Kai ta d'aga, ya jata jikinsa ta kwanta, "to Alhamdulillahi" cewar Ammi,

"Rayya mahaifinki a yanzu shi ze taka rawar mahaifiyarki idan kina da damuwa let him know duk abinda ya ke ze saurare ki, we all can come in your second option uhm?" Mummyn Sam tace looking at her,

Kai ta d'aga with a smile plastered on her face kan ta kalli sashen da 'yan mazan suke tace "daddy nagode da afuwar ka a gareni but pls ina son kayi min wani abu in return"

"Anything for you my daughter "

"Idan duk ranar da mummy tayi 5 month zan fad'a maka, karka manta kayi min alqawari"

"I promised"

"Amm...i think ya kamata kafin mu tafi a tsaida ranar tarewar yaran nan dan bana son wata bidi'a ko ya kuka gani" Ammi ta qarashe idonta akan barrister da gomna

Barrister ya jinjina kai "hakane nake ganin idan babu damuwa akwai gidajen su dake nan daura da nawa a gyara idan yaso su fara tare wa anan kafin mu koma"

"Which means dole ayi d'an biki kenan idan ba haka ba mutanen mu su samu a bakin duniya" cewar gwaggo, dariya sukayi a take aka tsaida nan da sati biyu masu zuwa za a sha shagali.

Ranar Biki

Qoqarin kai hannu take ta ja zip d'in amma sam ta kasa cikin cuno baki take fad'in "ni ni ni Allah na gaji bazan ma fita ba, zir zir hawaye ya hau zubo mata, saman gado ta fad'a ta game da janyo wayarta tayi dialling number, bisa mamakin ta se jin ringing tayi a d'akin "mummy why do you left the fone here? Ta qarashe cikin chidish tune,

Wayar ta cilla gefe jin da tayi an rufe qofa alamar an shigo ita a dile tayi fushi duk a tunanin ta mummy ce. Qamshin turaren TOBACCO daya bigi hancinta yasa ta sauke ajiyar zuci game da lumshe ido, she doesn't see dis coming, ta ina ya shigo cikin tarin jama'ar nan? Ta tambayi kanta

Tafiyar tsutsan da yake mata yasa tayi saurin juyawa rigingine game da sakin dariya, "perfect" yace, qafafuns ya raba game da hawa samanta ba tare da ya ta'bata ba har seda fuskarsa ta daidaita da tata ya sakar ma kyawawan lips d'inta sumba kafin ya zira hannuwansa ta bayanta ya tallafo ta jikinsa, shiru ne ya biyo baya kan a hankali yace "nazo shirya amarya ta"

Wal tayi da ido, ya kanne mata idonsa, dariya tayi tace "ina su mummy?"

"Nace dasu su huta ni zan shirya abata"

"Mene?" Yanda ta waro ido ya sa shi dariya, daidai lokacin suka ji knocking, " maza tashi ta qaraso"

"Wa kenan"

Miss dee from abuja na taso ta takanas saboda ta shirya min ke, qofa ya bud'e matar ta shigo kallo d'aya zaka mata kasan ta jiqu da naira ga uban gayu da take dashi cikin daddad'an muryarta data tsumu da turanci suka gaisa da Anwar kan ta maida idonta kan Sam game da furta kalmar "tubarkallah, amaryarka tamkar ita tayi kanta, she is the real definition of beautiful,"
Chapter 29 · 0% Book details