← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 30

Sashe 6

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk inda quluwa takai ya gama quluwa alhaji me babura kenan wanda yayi tattaki takanas yazo wajen Anwar dan tattaunawa ta musamman, dad’a karkacewa yayi bisa kujerar yana hararar shi qasa qasa,

‘Dago kai yayi a nutse murmushi maqale a bakin shi, “barka da zuwa alhaji hope u didn’t find any difficulty coming in here?”

Tambayar tazo mishi kamar da rainin hankali, basarwa yayi “ah Alhamdulillah, ya aiki naga kamar kana aikine ma”

“Aa no karka damu nagama ai, if to say ban gama ba da zan sallame ka ne zuwa wani lokaci “

Jinjina kai Alhaji yay yaci gaba, “ko akwai wani abu da kake buqata?”

“Sir Anwar kan maganar nan ce da mukayi a waya kan fitulun babura”

Jimm yayi zuwa can ya sauke numfashi yace, “alhaji me babura ko?”

“Eh eh ni ne”

“Na tuna, amm bari muga..”
Wasu takaddu ya janyo ya bashi yace gashi ya cike yayu transfer yanzu”

Haka suka ci gaba da tattaunawa har Allah yasa aka dace suka rabu.

***
Sam ta tashi a firgice tana qwala kiran Abbanta da umma har ma da Ameer nurse munirat ta fad’o d’akin a guje

“Shhh calm down fine baby, menene ya sameki, gashi doctor hasheem ya fita wayyo”

Marairaice wa Sam tayi “please ki kaini gurin umma na da Amir kinji kar su tafi su barni” kuka take bil haqqi, har da su majina

“Okay ok kiyi shiru bari naje na d’auko waya na kira doctor”

Girgiza kai tayi a tsorace, tunanin ta d’aya wannan mafarkin da tayi wai sun tafi sun Bart’s gashi tana ta neman su bata gan su ba”

Wani sabon kukan ne ya su’buce mata, zuwa can bacci me nauyi yayi nasarar d’auketa.

Munirat dake bakin qofa ta le’ko da farantin silver a hannunta me d’auke da allura ta shigo tayi mata.

Tajima a tsaye tana kallon ta ba abinda take se qiyasta kyawu irin na Sam, zuwa can ta sauke ajiyar zuci ta fita tana gunaguni saboda wayar Doctor da taqi shiga

***
Qarar bell ce ta tashe shi jin se dannawa ake ba qaqqautawa salati yayi tare da miqewa ya zauna hannu yasa ya murza idanu, ya kai hannu ya kunna bedside lamp idansa ya kai kan agogo 5:10am wane haka?

Tashi yayi yana gyara zaman boxers d’insa ya nufi qofa, fridge ya tsaya yasha ruwa sannan ya nufi qofa ya bud’e, saurin juyawa yayi ya kalli time kan ya waiwayo ya kalle shi

“Hasheem?!”

Winking ya masa ya ra’be ta gefensa ya shige ciki, rufe qofar yayi ya biyo shi saman kujera ya zube yace “lafiya dai na ganka da asuba haka?”

Dariya yayi, “ina neman rakiyar ka ne”

“Rakiya yanzu?”

“Taimaka min zakayi, nayi maka alqawarin daga yau bazan kuma takura ka ba bare ma tafiya zakayi zamu jima bamu had’u ba”

Numfashi ya sauke yace “amma kasan yau by eleven jirgina ze tashi right?”

“I promise you ba zamu jima ba”

“What’s so important da gurin da zamu je kuma inane?”

“Kasan dai ni ba d’an yankan kai bane”

“Kana fad’a min magana ne? Zan fasa wullahi”

Hannu ya had’e gu d’aya “yi hakuri yalla’bai ka shirya mu tafi”

Hararan wasa ya yi masa ya shige d’aki .

Se gurin 6:30am suka kama hanya, banda hamma ba abinda suke bugawa daidai wani tamfatsetsen gate yayi horn gate d’in ya bud’e ya nausa hancin motar ciki a harabar yayi parking suka fito wani matashin saurayi yayi musu sallama tare da yi musu iso zuwa bakin wani pool cikin wata bukka.

Zaman su ke da wuya ya fito sanye da jallabiya hannunsa riqe da mug sallama yayi musu suka amsa, kiran sunansa da yayi ne yasa shi d’ago kai ko ba’a fad’a ba yasan wanene numfashi ya fusar tare da watsawa hasheem wani killer look.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(9)

*NOT EDITED*

Sipping shayin yayi kan ya kada baki yace “Anwar Amin Alfalla, the young talented billionaire nasan za kayi mamakin ganina ko, well to clear your doubt ba abin mamaki bane duba da nan jihata ce, nakan san duk wani shige da fice da akeyi cikin ta” ya numfasa “well kuyi haquri na cika ku da surutu ban baku abin sha ba, duba da weather d’in garin nasan zaku fi buqatar me d’an d’umi”

Basu kai ga yin magana ba ya bada order a kawo musu abun ta’bawa, maida idonsa yayi kan fuskar Anwar wearing a smile yace “Anwar ko kana da abin cewa?”

Forming line yayi da bakinsa still idanunsa maqale kan hasheem kan yayi faking smile yace “ranka ya dad’e sir bani da abin fad’i, se abinda kace”

Jinjina kai mainasara yayi “ok I think duba ga lokaci let’s just get straight to the point but kafin nan Anwar ko meye dalilinka na qin yin aiki dani? Ma’ana qin yimin abinda nayi requesting duk da cewar na had’a maka da deposit ne?”

Murmusawa yayi yana me kuma sadda kai qasa yace “I’m sorry ranka ya dad’e amma inaga zefi cancanta muje kan maganar data kawo mu nan daga baya se muyi wannan”

“Ko zan iya sanin dalilin da yasa kasan cewa ba maganar kenan data zaunar damu a nan ba”

“Ranka ya dad’e akwai different companies da suke qwararru ta wannan fannin wanda suka dame ni ta ko ina kan meyasa akan ni kad’ai zaka damu?”

Gyad’a kai mainasara yayi yana mamakin courage irin na Anwar ya d’age gira “maganar ka gaskiya ce, amma inaso ko dan gaba ka kiyaye, maganar mu ta gaba kuma..ko ka sanar dashi?” Ya karashe maganar idonsa kan hasheem

“Aa ranka ya dad’e abinda ka aika ni yi kad’ai na aiwatar wannan hurumin ka ne”

“Anwar! Ina neman alfarma a gurin ka”

Mamaki ya cika shi cikin sanyin sauti yace “alfarma? A wurina kuma”

Mainasara ya jinjina kai, daidai lokacin aka kawo musu abin ta’bawa aka zuba wa hasheem anwar kuma tea kawai ya kar‘ a shima d’in kad’an ya kur’ba
“Anwar inason ka nemi auren yarinya ta Rayya..” maganar da me girma governor ya sashi wata muguwar qwarewa

Tun qarfi hasheem ya shiga taping bayansa, bayan ya kar’bi gorar sassanyar ruwan sanyi ya tuttula masa a baki, sunkuyar da kai yayi na wasu sakanni kan yaja hanci ya mi’ke tsaye da sauri yana d’an sadda kai yace “with due respect ur excellency, I’m sorry for what I did a baya, amma idan kana son hukuntani ne dan Allah kayi ta wani hanya ba wannan ba”

Dariya mainasara yayi “Anwar kenan” ya dafo kafad’ar shi “a kan wani dalili zan nema hukunta ka, kan rights d’inka? Aa bana haka, kuma hukunci da ‘yata how ridiculous! “ ya maida idonsa kan hasheem “dr ko zaka iya yiwa abokin ka bayanin rayya! I mean inda ta Ganshi”

Gyaran murya yayi bayan ya kora ruwa ya kalli Anwar dake masa wani d’an banzan kallo “yarinyar da ta fad’i a bakin office d’azu”

Kya’be baki yayi, ta ya suke expecting ze iya tuna wata yarinya! Wacce take asibiti ma mara lafiya, shirun da yayi yasa me girma governor dad’a watso masa tambaya, “ka tuna ta?”

Girgiza kai yayi a qafule yace “I can’t remember her”

“Whatever de Anwar wannan be maqasudin zaman nan namu, Ina neman alfarmarka da ka taimaka min, Rayya bata ta’ba neman abu ta rasa ba ko da kuwa Nisan sa yakai birnin sin, ga qoqon bara ta nan Anwar dan darajar Allah ka taimaka min”

Kallon mamaki yabi governor dashi, soyayya? Shi ya so wata? Kuma wai da aure!”

“Silence didn’t speak Anwar so zan baka dama kayi tunani amma kafin nan zanso ka ganta kan ka tafi dan abokin ka yace za kaje ganin gida”

“Ye...yea..h, a zuciyarsa kuwa banda tafarfasa ba abinda take, shi yaso wata da zancen aure Ina yake da time ma, gskya ma he’s not ready kwata kwata, to speeds things up ya amsa da to,

Nan da nan kuwa fara’ar me girma governor ta fad’ad’a inda yasa ayi ma firstlady magana ta sa Rayya ta kintsa, shiru be ya biyo baya har na wani d’an lokaci kan wayar dake gefen me girma governor ta d’au qara yana d’agawa ya sauke ya qwalawa wani magana inda ya umarceshi yaje government house ya d’auko Rayya,

Tattaunawa suka cigaba dayi tsakanin me girma governor da hasheem inda nan take me girma governor yayi ma hasheem alqawarin alkhairi masu yawa saboda kawo mishi Anwar da yayi.

Can gefen Anwar kuwa daddanna waya kawai yake amma hankalinsa kwacakon yana kan lokaci dan Allah Allah yake su tafi yaje ya fara shiri ya kuma ci mutuncin hasheem for bringing him to this hell

To hell mana kai shifa ji yake kamar yana zaune a waya, horn d’in da suka ji ne yasa shi d’ago kai a nutse waze gani? Wannan fat mango d’ince, wacce ta nemi kissing virgin lips d’inshi,

Idan be manta ba itace wacce ya hankad’e jiya, itace dama governor yake magana?, lallai dole yayi pleading dan Allah ne kad’ai yasan maza nawa taso raping, saurin kauda tunanin yayi jin maganar hasheem a kunnenshi

“Look how breathtaking beautiful she is”

Girar sama data qasa ya had’e ya watsa masa hararar kana da hankali kuwa, iska yaji fuuu ta doko shi before he knows se ganinta yayi tsugunne gabanshi ta tallafo chubby kumatunta ta tsare shi da ido,

“Hey bro A meyasa kullum kake dad’a kyau ne”

Saurin d’aga kai yayi yaga me girma governor bayanan ya maida hankalin shi kan hasheem ido waje Yana pointing d’inta da hannu alamun “is she d one?”

Kai hasheem ya d’aga masa yayi baya yayi relaxing yana sakacen Haqori...

(Ayimin afuwa yau ban samu damar typing da yawa ba. Tnc u)

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

Assalamu alaikum Ina neman afuwar jina shiru da ku kayi hakan ya faru sanadiyyar kakata da Allah yayi wa rasuwa, Ina barar addu’ar duk wanda ya karanta post d’in 🙏 nagode.

(10)
A nutse ya sauke kwayar idanunsa saman nata wanda hakan ya haddasa wa Rayya fad’a wa cikin shauqin bege, cike da izza yace “tashi a gaba na!”
Chapter 6 · 0% Book details