← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 30

Sashe 23

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bello ya gyad'a kai "eh, a littafin fada'ilu ma'u zam zam sahafi na 29 malamai sunce annabin rahma ya d'iga zam zam a bakin yaro, ko zuma a d'ugawa yaron a bakinsa ko a d'uga a bakin musulmi ya gauraya da yawunsa sannan a d'iga wa yaro"

Gyad'a kai tayi game da cewa "akwai zumar addu'a cikin jakar ki hajar wacce na baki ki rinqa lasa ko"

Mom hajar dke shedding tears tayi nodding kanta a qasa, jakar gwaggo ta janyo ta miqa wa barrister ya saka cikin bakinsa yasa wa yaran a baki, mulai mulai kuwa ya mamule, yay masa kiran sallah a kunnenta na dama game da miqata gurin gwaggo daidai lokacin da wayar bello ta karad'e falon da qara,

Sunan Bro A yayi appearing saman screen d'in yay saurin answering,
"Gamunan qarasowa" yace game da hanging off,
"Ina ganin ya kamata mu wuce goverment house dan tuni su Ammi sun qaraso"

Barrister ya kalli sashen da mom hajar take a hankali ya taka zuwa inda take "zaki iya bin mu ko hankalinki yafi kwanciya a nan"

Girgiza kai tayi, game da d'aga kai tana kallon nurse "sister pls taimaka min da hijabi na a ciki"

Kai ta d'aga tashiga wata qofa dake falon.

Riqe da ita barrister ya zauna a baya ya kwanto da kanta saman qirjinsa zuciyarsa ciki da tunani dalilin matar tasa nayin hakan?

Yayin da gwaggo ke gaba rungume da qawarta kamar yacce tace, bello kuma na driving hankalinsa baki d'aya naga kwaltar yana juya steering wheel cike da qwarewa.



Hannun Ammi cikin na mummyn Sam dake bacci sanadiyyar allurar da akayi mata, Anwar ne yaja hannun hasheem suka fita daga d'akin

"Ya dai ragowar mutuwa" hasheem ya furta cike da tsokana

'Yar qaramar dariya yayi, "bansan wulaqanci mijin fat mango" ya qarashe game da kanne masa ido d'aya, naushin wasa ya kai masa ya kauce yana fad'in

"Wlh karka kuma zagar min mata ko mu hanaka zaman garin nan"

Hannu ya had'a gu d'aya "ayi min afuwa masu gari, zo muje mu taho da baqin mu na nijar"

Da motar hasheem suka tafi basu tsaya ko ina ba se gaban gidan senator asi'u, seda akayi musu iso suka qarasa ciki cikin tangamemen falon inda Alhaji tasi'u yake basu wani jima ba suka fito biye dasu wata baqar jeep ce inda bayan sun fara tafiya suka sa'ba hanya,

Daga can kuma ss office a wata tinted mota aka sako hajiya maryam da d'anta halim ala nufo gidan gomnati dasu.

***
Ta wutsiyar ido take kallonta dan ta kula tunda su Ammi suka tafi take wani sukuku ko suna hira bata jefo baki kaman yarda ta kanyi lokxi zuwa lokaci,

Bakin gadonta munu ta zauna game da d'an jijjiga qafarta, idonta dake a lumshe ta bud'e suka sauka saman na munu,

"Tashi muyi wata magana" munu tace,

Kai ta gyad'a mata, tare da jingina bayanta jikin bango bayan tasa pillowfor support,

"Sam inaso ki fad'a min gaskiya duk tambayar da zanyi miki pls"

Sai da ta sauke numfashi tace "ina jinki,"

"Zaki iya fad'a min whats going on between ke da Bro B?"

Baki ta bud'e ta katseta, "truth..i want the truth"

"Munu is kind of weird! I don't know how to put it into words"

Dariya tayi qasa qasa "ki fad'a min Sam zan fahimta, i saw the chemistry between the two you"

"Dagaske?" Tace in a worry voice,

"Hey chill, nice fa all i know is yana yawan kallonki a sace that is tun lokacin da muka koma gidan su ga yawan yi miki fad'a wanda ni a fahimtata yanason yake jin maganar ki ko da kuwa cikin kuka ne"

Fuska ta yamutse "ke munu, ba novel kike karantawa ba all this signals..."

"Oh! Ke a tunaninki abinda nake karantawa all na wash? To tsaya kiji duk abinda qwaqwalwa ta qirqira used to happen in real life"

"Ahh" tayi making sound,

"Baki yarda ba kenan?, shikenan, yanzu dai i need my answer"

Gyara zaman Sam tayi had'e da crossing legs, nan ta zayyane mata tun first kiss d'insu har abinda ya faru ranar da suka zo yi musu sallama,

"..munu wlh forcing d'ina yake abin nata damu na, kinsan yanda nake i usually bar magana a zuciyana...and i'm also scared to say it out especially to Ammi, dan Allah ki taimaka min munu.." ta qarashe cikin kuka,

"Shiishh...is ok" tasa hannu ta goge mata hawaye tare da rungume ta, tunani ya cika kanta,

Zuciyarta na bata lallai akwai de wata a qasa dan a yacce take ganin Ammi bayan kamasu cikin intimacy will never let go of it cikin sauqi dole akwai wata a qasa, da wannan tunanin bacci ya sace su kasancewar su duka ba sallah suke ba (they are on period).

***

Tun bayan da suka isa gidan a ka bawa Ammi band'aki ta wanke mom hajar tas har da babyn ma, duk da cewa har kawo wa wannan lokacin tana zubda hawaye haka anyi anyi ta furta abinda ke zuciyarta taqi qarshema she insisted on lallai idan an zauna maganar data tara su zata fad'a idan kuma an takurata zata fasa maganar kuma she's going to live, hakan yasa aka bar yi mata maganar tun bare da suka samu ta shayar da baby teema wato fateema zahra kamar yanda barrister ya rad'a mata suna.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(29)

Sallamar sa ce taja hankalin bello dake hira da Ammi tsam ya miqe ya fad'a kan qirjinsa a tare suka saki wani silent kuka,
"Bro B...dafatan kana cikin qoshin lafiya?"

'Dago kai yayi game da dafa kafad'arshi

yace "yanzu kam dana ganka na tabbatar da lafiya nake, tun bayan daka tafi na kasance cikin fargaba da d'imauta, yanzu kam bazan yarda ka kuma yin nesa dani ba qafata qafarka" ya kuma rungume shi, d'an dukan bayansa Anwar yayi "nima bazan kuma yarda na barka cikin garinnan dake dabaibaye da abubuwan al'ajabi ba d'an uwana "

Knocking akayi bisa door, inda me girma gomna ya bada umarnin a shigo,

P.A d'in gomna ne,
"Ya akayi Rabi'u?"

Sai da ya sara cike da girmamawa yace
"Sir, dss bashari yace a sanar maka da zuwansa"

"Let him in" cewar jamilu mainasara

Ya juya idonsa a lumshe ba tare daya furta uffan ga mutan falon dake ta'ba hira kad'an kad'an cike da alhini ba,

Qarar qarafunan dake riqe da hannu da qafar halim ne yaja hankulansu kan masu shigowar, seda suka shigo falon sosai Ammi ta miqe tsaye sede kafin ta samu damar furta wata kalma muryar kawu kabiru ta daki kunnan gwaggo itama de miqewar tayi lokaci d'aya hawaye ya yanke mata, nan kuma isowar umma salamatu ta kuma saka falon a wani yanayin yayin da take hajiya maryam ta hau zantuttuka masu kama da sambatu cewar lallai se an fitar da umma salamatu daga falon

firr ta rikice musu tamkar sabuwar ta'bi har seda kyautar lafiyayyan mari daga hannun me girma gomna ya sauka a kuncin ta kafin a samu weather d'in d'akin ta daidaita,

nuna kanta tayi da yatsa cikin zare idanu take fad'in "Ni? Ni ka mara jamilu.."

Dariya ya d'anyi me sauti, "kwarai maryam yau sunana jamilu...to Alhamdulillah tunda ke kanki kinsan ta faru ta kuma qare, a yau ina so ki sani duk wanda ya jira ganin bacci na to kuwa ze rasa nashi, maryam kin shani na warke inaso da bakin ki a gaban kafatanin mutanen falon nan or let me say family ki fad'i gaskiyar yanda al'amarin aure ya qullu tsakanina dake bayan 'yaruwar ki mariya da na nema?"

Kallon kallo aka koma yi, cikin sauti me cike da d'imbin mamaki gwaggo tace
"Me kake shirin cewa ranka ya dad'e?"

Kai ya gyad'a idonsa saman fuskar hajiya maryam da yakejin tsanarta fiye da tunani yace "kar ki bari na fusata, dan al'amarin baze ta'ba yin kyau ba"

'Dit dit..qarar na'urar dake nuna fitar numfashin hajiya mariya ta karad'e kunnuwansu
"ta farka" shine abinda wata nurse dake kula da lafiyar ta, ta furta cikin farinciki, cikin su rasa me bawa wani hanya akayi, Ammi dake gaba turus tayi data shiga dakyar ta iya jan qafa zuwa gaban gadon cikin zubar hawaye yayinda ta toshe bakinta da hannu..

Cikin murya me fitar da iska ta marasa lafiya tace "yaya...ha.j.j..o" ta miqa mata hannu, saurin kamawa Ammi tayi game da jinjina kai, "nice..nice mari.."

Smiling hajiya mariya tayi, d'ai d'ai take binsu da ido kan fuskar jamilu mainasara ta tsaya, ta lumshe ido ta bud'e cikin qoqarin tashi,

"Tsaya na taimaka miki jikin ki ba qarfi sosai" cewar nurse bayan da ta gyara mata pillow a bayanta ta yacce zata fi jin dad'in zama, murmushi ta mayar mata, kan ta waiwaya ta kalli yaruwar tata

tace "tun bayan da labarin rasuwar daddyn Sam ya riske ni, nake mafarkin yaro me irin fuskarki yana bawa mami na kulawa yaya hajjo, se de mafarkina na jiya daban ne da sauran..shin dagaske ne Mainasara yasa an qwato ni ceto ni daga azabar da yaya maryam ke gana min na tsayin lokacin da Allah kad'ai yasan yawansu..yaya hajjo kin ta'ba jin labarin da mutum ke yiwa kansa fatan mutuwa?...to nayi wa kaina har wani lokacin nakan nemi kauce hanya,

Tsayin wannan lokacin na kasance cikin wani cage da ko cikin dabbobi mafi qasqanci ake ajiyewa ciki, ba sallah, ba wanka se bayan wata take bani sitira na sauya, abinci sau d'aya a rana, bayan gida ina yinsa ne cikin ledar da kawo min abinci, ina shan ruwa sau biyu a rana,

Bani da abin rufa cikin ko wani yanayi da ake ciki haka nake kwana, ga sauro dake addaba ta, kinsan me nake ce mata tun ina kwana d'aya a wurinta?"

Ammi ta girgiza kai "..ina ce mata ne, yaya maryam ki taimakeni ki kashe ni idan bazaki iya ba ki bawa yaran ki su qarasa ni ko ki bani guba nasha..." ta qarashe cikin hawaye,

Ammi ma cikin zubar hawaye tace "ya isa haka mari, duk ba mafarki kike yi ba, tabbas mainasara ya ceto ki daga hannun makirar can and he stands to get justice for you, ki bar zubar da hawaye kada kanki yayi ciwo.."
Chapter 23 · 0% Book details