← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 30

Sashe 26

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Key yay ma motar sa ya nausa bisa kwalta, yana tafe yana zubda qwalla besan haka soyayyar Sam tayi mishi mugun kamu ba se yau da waninsa ya furta kalmar so a gareta, wanin ma d'an uwansa, steering wheel ya doka tun qarfi tare da fashewa da kuka hannunsa saman qirji yana duka fad'i yake "why why meyasa ki kai mana haka she's my heart and bello is my own blood" ya sauke ajiyar zuciya, da taimakon Allah ya isa gidan kawu kabiru.

Cikin jerin motocin kawu ya ajiye tasa, da d'an saurinsa ya qarasa cikin gidan, ba me cewa ga halin da yake ciki saboda toshe idonsa da yayi da baqin gilashi,

A falo ya had'u da umma salamatu da mummyn Sam cike da wani tsananin kunyar su ya sunkuyar da kai, har qasa ya tsugunna ya gaida su, cike da fara'a suka amsa masa umma salamatu na tsokanar shi

"Haba Anwar a 21st century muke fa, surukuntaka is now old model, kai da za kazo mu zauna mu sha hirar mu "

Key d'in hannunshi ya cusa cikin sumar kanshi yana susa game da kuma sadda kai yana murmushi,

"Ammi fa?" Yace murya qasa

"Au ja'iri bazaka kulani ba kenan, to kaje tana d'akin ciki daka hagu"

Kai ya d'aga sum sum sum ya shige ciki, saman sallaya ya sameta zaune ta d'aga hannu sama tana addu'a, da azama ya isa gareta saman cinyarta ya kwantar da kanshi tare da sakin wani silent kuka wanda danshin ruwan da taji ne yasa data idar da addu'ar ta leqa fuskar sa,

"Subhanallahi, Ann lafiya?"

Kai ya girgiza "Ammi bro b.."

A rud'e tace
"Bello? Meya faru dashi?..d'agani muje na gani a ina yake?"

Girgiza mata kai yayi a hankali ya tashi zaune fuskar nan tayi jaga jaga da ruwan hawaye

"he..saidd..." gaza furta qarshen zancen yayi ,

A firgice tace "sunyi masa wani abu ne shima?" Ta tambaya

"Ko d'aya Ammi,...Ammi kinsan cewar inason bro B sosai ko? Inason shi sama da yanda nake qaunar kai na..i can even sacrifice my own life in har tasa zata inganta,"

Cikin rawar murya tace "naji...naji fad'a min abinda ke faruwa mana"

"...he is my only blood Ammi, i see Abbi when ever i look at him...Ammi soyayya batayi mana halacci ba"

"Ka fahimtar dani Ann, ni-nifa bangane inda maganarka ta dosa ba"

"Ammi zan iya bar mishi kowa, komai amma banda nan" ya nuna heart d'inshi da yatsa, ya cigaba da fad'in "...ita d'in zuciyata ce, rabuwa da ita tamkar rasa rayuwata ne,...meyasa ze ce yana son matata ta sunna!"

Ji tayi d'if duniyar ta tsaya mata idanunta kan qofa inda bello ke tsaye tamkar ruwa ya cinyeshi.

"Bel..lo!!!" Ta qwala kiransa on top of her voice,

'Dago kai yayi kan ya furta komai suka jiyo qugin mota tun qarfi, ai rasa me bawa wani hanya akayi tsakanin Ammi, umma salamatu da mummyn Sam,

"Shin meke faruwa ne?" Suka furta kusan a tare idonsu bisa fuskarta,

"Innalilllahi wa inn'ilaihir rajiun" ta furta a fili kan ta juya ta koma cikin gida suka mara mata baya,

A daddafe ya fito falon, ya zube a gabansu, cikin sambatu yake fad'in bazan iya rabuwa da matata ba kuyi min rai, haka ya rinqa maimaita kalmar har bacci nannauya yayi awon gaba dashi,

Cirko cirko sukayi a kanshi cike da tausaya masa, mummyn Sam ce tayi qarfin halin d'aukar waya ta kira bello,

Wani irin rough driving yake cikin fitar hankali, yayin da a gefe guda kuma 'yan sanda ke biye dashi sedai duk qoqarin su basu cimma shi ba, yayi gaba ya barsu da cizon yatsa🤣.

Shagon unguwar su salihu ya nufa dan yasan can ne ba wanda ya sani idan ka d'auke hasheem, wayarsa dake haske ya kashe ya kuma rufe kansa a d'akin, ruf da ciki yayi rungume da pillow yana kuka me cin rai,

A fusace ya tashi zaune yana maganganu, "wallahi a a bayan na gama shukata qiris ya rage na girbe, Sam batayi deserving heartless miji irin ka ba, baka sonta lallai se ka datse igiyar auren nan ka bani ita domin ita d'in tawa ce,

Nasha ganin soyayyata kwance cikin idonta, Sam bazata ta'ba amincewa da kai ba after dukkanin cin mutumcin da kayi mata, se yanzu da kaga ta isa ban ruwa...bazan ta'ba yarda ka mallaki abinda yake nawa ba, Sam Amanata ce, she's mine and i'm going to make her mine officially, dole ka sake ta na aura...!"

Da haka ya silale bacci yayi awon gaba dashi.

***
"Hasheem ya kake ganin lafiyar tashi"

"Mummy damuwar da yake ciki na neman ta'ba mishi zuciya dan yanzu haka yana cikin maxim.."

"Um um um um sam yarona lafiyarshi qalau..."

"Only if you give him abinda ya ke so Am..."

"Zo muje daga waje" tace dashi living mummyn Sam and umma salamatu behind.

"""
Tagumi ya kafa bayan gama sauraron abinda Ammi tace, "Ammi her love change d demon in him"

"Pardon?"

Jinjina kai yayi da cewa "tun sa'ada kuka zo na kula bai cika son magana ba kullum cikin kallon wayarsa which i definately know hotonta ne, he even day dream about her,..Anwar often smile amma yanzu his lips are always parted and spread kamar zasu ta'bo walls d'in kunnensa har hakwaransa ana gani yanzu"

"...you observe all this ba tare da kasan da maganar nan ba? Dr kasan yarana sosai, cikinsu who deserve to be with Sam?"

"Ammi Sam matar Anwar sunanta, kuma ba'a ta'ba canja wa tuwo suna Allah kad'ai yasan alkhairin da ya shirya cikin auren nan"

"Bello fa?.."

Gira ya d'aga game da cewa "well! Bello In my own observation tausayin Sam yafi rinjaye a zuciyarsa sama da soyayyar da yake ikirarin yana mata..."

"Kamar yaya?"

"Ina nufin tausayinta yake ji, be sani bane, but i'll make him understand" ya miqe tsaye,

"Ina zaka je?"

"Zanje na taho dashi"

"..bazaka iya samun shi ba, wayarsa a kashe take.."

One sided murmushi yayi "zan zo miki dashi yanzu Ammi"

Cike da damuwa ta d'aga kai, da ido ta bishi har ya 'bace wa ganin ta.

***
Abinci suke ci hakan yasa banda qarar spoon ba abinda ake ji,

"kim"

Saurin waiwayawa sukayi jin an qwala kiran hatsabibiyar yarinyar mss chloe kamar yanda suke kiranta dashi saboda rashin jin maganar ta.

Daga wata qofa ta fito, tana girgiza tamkar bishiya idan ana iska, dama gata kamar ta karye tsabar rama, ido biyu suka yi da munu ai kuwa ta galla mata harara,

Da turanci tace "ke wakike ma kallon banza"

Munu tace "ke da wani idon kika ga na kalle ki?"
Qwafa tayi cike da takaici can cikin zuciyarta kuwa haushi take ji da ba Sam bace, dan haka kurum taji batason yarinyar, yarinya tamkar ita ta halicci kanta, duk wani features da Anwar d'inta ke so na 'ya mace yarinyar nan me qwala qwalan ido tana dasu, abin takaicin kuma shine mom d'inta tace cousin sister d'in Anwar ce,

Numfarfashi take tamkar wacce tayi tsere idanunta na faman harararsu, sede hausawa sunce harara a duhu...dan ita samira ko d'ago kai bata yi ba kanta a qasa tana cigaba da cin abincinta.

Tsaki taja ta nufi wurin sakatariyar mahaifiyarta ta bata wata paper kan ta juya ta bar wurin cike da takaicin Anwar d'an uwan Samira ne.

Nannauyan ajiyar zuciya Sam ta sauke bayan ta waiga taga fitarta, ta dawo da idonta kan munu,

"Wai meyasa bakya shayin tsokanar matar nan ne? Bakya gudun ta fad'awa mamanta.."

"Ta fad'a mana se me ai itama mss chloe tasan halin nata, kuma inada tabbacin mu zata mara wa baya"

"Kinga kallon da tayi mana kuwa, Allah dakyar nake tura abincin nan dan qiris nake jira naga tayo kan mu nasa gudu"

Dariya Munu ta kwashe da ita, "kice dama sadda kan da kikayi idonki na kanta?"

"Ba dole ba kinga yanda take numfarfashi kamar tsohuwar guzuma"

Dariya suka kwashe da ita, daidai lokacin suka jiyo ihun mss chloe tana masifar wa yace sakatariyar ta ta bari Kim ta tafi California ba tare da saninta ba,

Kallon juna sukayi sum sum sum suka bar wurin zuwa sport complex.

***

Daqyar ya iya cire jiki daga katifa ya nufi qofa jin yadda ake bugu,

"Waye?" Ya tambaya in a sleepy yet cracky voice

"Bello bud'e nine"

Kamar ya share sede ya bud'e ya juya ciki, girgiza kai hasheem yayi bayan ya tura qofar,

Komawa yay ya kwanta idonsa a lumshe, yayin da hasheem ke tsaye a kanshi hannunsa cikin aljihu yana karantar yanayin shi,

Numfasawa yayi a hankali yace "Bello tashi muyi magana"

"Ina saurarenka" yace ba tare da ya motsa ba,

"Ka tashi ka zauna nace!" Yace in a commanding voice,

Bello ya tashi zaune game da fursar da iska me zafi daga bakinshi, yace "ina jinka"

"Menene dalilin da yasa baka ta'ba fad'amin labarin soyayyar da kake yiwa Sam ba, afterall ni da kai muke aikin nan tun farko, uhm?"

"A lokacin she's such a baby and at that time i have no feelings for her,..."

"Yaushe ka fara jin soyayyar a zuciyarka?"

"The day Anwar punished her"

"Uhumm?"

"Tana kuka...helplessly... kallo d'aya nayi mata naga yarinyar need a shoulder to lean on, amma kaga yanda yayi treating d'inta idan ta zama under his custody me kake tunanin ze faru, shin waye ya bashi ita da har yake ikirarin matar shi ce?!"

"Kawu kabiru, and it's official,..."

"Official my foot! Doctor nasan Anwar abokin k..."

"Anwar? Bello a kan mace kake kiran sunan d'anuwanka da raini? ka nutsu ka dawo hayyacinka fa, how sure are you ita yarinyar bata son auren? Or do you think 'yar qanqanuwar soyayyyar da kake ikirarin kanayi mata zata aminta da kai! Look idan rai ya 'baci be kamata hankali ya gushe ba, aure ba abun wasa bane kada na kuma jin kana cursing d'in shi in ba haka ba wullahi zaka gamu da fushin ubangiji, gara ka san abinda kake idan kuma kaqi tam! A yanzu haka mahaifiyarka na can hankali tashe kar ka bari ta dalilinka wani abu ya faru da lafiyar ta kamar yanda kayi sanadin ta d'an uwanka!" Da fad'in haka Hasheem ya fita a fusace cike da 'bacin rai.

©️ Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊
Chapter 26 · 0% Book details